Washegari Lahadi Zayyan yazo Dandume zance wajen Safiyyah, a yau ne suka taba tattaunawa extensively akan rayuwar kowannensu, Zayyan ya baima Safiyyah tarihinshi dana iyayenshi kaf, itama ta bashi nasu in detail, basu taba yin hira mai zurfi da tsayi akan junansu irin yau ba, yanayin neman auren Zayyan da Safiyyah cikin dattaku kamar na mutanen da, sabida koyarwar gidansu Safiyyah da suka dora soyayyar tasu akai, har sunan su Hatoon yau ya gaya mata, da su Yaya Zubaida, sai yau Safiyyah ta san adadin ‘yan gidansu, da hotunansu cikin wayarsa, ita kuma ta kira kyawawan kannenta uku mata duk. . .