Bangaren Faisal ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kaiwa da komowa yake a falon, irin abin nan da mutum marar sukuni yake aikatawa wato safa da marwa, inda kuma a take ya hau magana da kansa a fili kuma a bayyane kamar wani zararre “ taya ma za'a ace na auri wannan kucakar yarinyar gaskiya Dady bai mani adalciba nifa ko da na ayyana a raina zan aureta ba kalar wannan auren ba aure zanyi da ita na burgewa da gusar da sha'awa daga na samu biyan buƙata na bata red cart tai gaba, ni da nai. . .