Shigowar baba da yaya salima wurjanjan shine ya dawo da sireenah daga duniyar tunanin da tashiga, ta kalli yaya salima fuskarta tai face face da hawaye da majina ga babu hannun da zata share wuyan abayarta ajirge tai wani iri babu kyan gani sai tausayinta ya kamani.
"Garin ya ya hakan ta far? " cewar baba cikin tashin hankali
" sireenah ce yau bata dawo da wuriba har magariba hakan yasa mama wura wuta zatai sanwa saboda baƙar yunwar da mukeji shine kararen suka tirniƙe gidan da hayaƙi sai mukaga mama ta yankejiki ta faɗi lumfashinta yana sama. . .