“Amin summa Amin na gode kwarai yayana Allah ya saka da alkhairi Allah ya bar zumunici Allah ya ƙaro donƙon kauna a tsakaninmu ”.
Amin Sireenah.
Sai da ta saka gefen ɗan kwalinta ta share hawayen da suka fara bin fuskar ta kafin ta ce “To yaya wane hali su mama suke ciki kasan mama batasan hayaƙi ko kadan sukuma su yaya saratu kowa da lalurarsa ko yasuke yi su ci abinci? ”.
“ mama da yaya saratu dama kowa duka suna lafiya domin (gas) ɗin da Ummah ta saya da sunan tara kayan bikin ƙanwata na ɗauko batare da sanintaba na kai. . .
