WASHEGARI
Gidan su sireenah tunda safe mama ta tashi ta kunna gas ta dafa ruwan zafi ta saka kayan yaji da lipton akai ruwan shayi ba madara aka aika Al-ƙasim ya kaima sireenah kalacinta prision da yake basu da nisa da gidan yarin, breadyn da Baba ya sawo aka raba kowa aka ɓallamasa sukai karin kumallo, kafin daga bisani mama ta hau gyaran sauran shinkafar da suke da ita wacce ba zata huce kwata ba cikin wadda Najeeb ya kawo musu da yake bahausace.
Baba ya miƙe yana kallon mama kafin yace “ To mu zamu fita kasuwa muga ya. . .
