Wannan ɗauke ƙafa da Khamis ya yi ma iyalansa ba baƙo ba ne a wurin Aisha. Tunda suka yi aure ta fahimci ƙaurace ma gida ce hanyar farko da yake huce haushinsa, don haka yanzu ko a jikinta.
Maryam kuwa sosai hakan ya sa ta damuwa, don rabonta da ganinsa tun da suka rabu a falo da yammacin jiya, duk da kuwa a ranar take karɓar girki.
Gashi tun jiyan ta yi tanadin mantar da shi damuwar da suka sa shi, sai dai bata samu damar haka ba. A daren kuwa ta kira shi ya fi a ƙirga. . .
I look forward to reading your interesting books.