Skip to content
Part 15 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Wannan ɗauke ƙafa da Khamis ya yi ma iyalansa ba baƙo ba ne a wurin Aisha. Tunda suka yi aure ta fahimci ƙaurace ma gida ce hanyar farko da yake huce haushinsa, don haka yanzu ko a jikinta.

Maryam kuwa sosai hakan ya sa ta damuwa, don rabonta da ganinsa tun da suka rabu a falo da yammacin jiya, duk da kuwa a ranar take karɓar girki.

Gashi tun jiyan ta yi tanadin mantar da shi damuwar da suka sa shi, sai dai bata samu damar haka ba. A daren kuwa ta kira shi ya fi a ƙirga gami da tura mishi texes, amma bai ɗaga kiran ba kuma bai yi mata reply ba.

Yadda ta ga rana kuwa haka ta ga wannan dare da tuni ya shuɗe. Abu biyu ne suka hana ta bacci, tsoro da kuma kewar mijinta. Washegari da burin iske shi a ɗakin shi ta gama sallar Asuba, sai dai kafin ta fita ta jiyo ƙarar fitar motarshi.

Maryam ba ta taɓa sanin fushin miji na da taɓa zuciya ba sai yanzu, don tunda suka yi aure makamancin haka bai taɓa faruwa ba, duk da suna samun saɓani sosai, saboda an ce ‘Zo mu zauna zo mu saɓa’ ne. Kuma Khamis ya sha yin fushi da ita, amma bai taɓa ta’azzara kamar na wannan lokacin ba.

“Oh ni ‘ya su, yanzu ya zan yi?”

Ta faɗa lokacin da take tsaye a jikin tagar ɗakinta, bayan ta sake kira bai ɗaga ba.Text mai ɗauke da damuwa ta sake tura mishi, sannan ta dawo kan sofa ta kwanta.

Ba ta daɗe a kwancen ba yunwa ta taso mata, wadda kuma ciki ya sa ba za ta iya jure ta ba. Fita ta yi da nufin haɗa ma kanta breakfast, don ta ɗaukar ma ranta ko da Aksha ta yi girki ba za ta ci ba, bare ma Aishar nata da yaranta kaɗai ta haɗa.

Khamis kuwa jerin gwanon texes ɗin Maryam ne suka ɗan sassauta mishi zafin da yake ji a ransa, don har ga Allah faɗansu na jiya ya zauna mishi a rai, saboda tunda suka fara haka, musamman da Aisha ta fara saka yaranta a faɗan, to rabuwar kan iyalansa da bai fata ce za ta afku.

Zaune yake cikin rumfa a wurin saida motocinsa. Kuɗi ya ba Sani ya karɓo mishi lafiyayyar wainar shinkafar da aka dafa miyarta da naman zabo, a wani restaurant da ke kusa da su.

Ba kowace damuwa ce ba ke hana shi cin abinci, don haka sai da ya yi hani’an da wannan waina da nama. Yana gamawa ya sha ruwa tare da wanke hannu.

Gyara zamansa ya yi tare da jingina bayansa da bangon wurin. Wayarsa ya ɗauka tare da shiga message. Saƙon Maryam mai ɗauke da emojies masu nuna alamun damuwa ne ya buɗe, daga ƙasan emojies ɗin kuma ta rubuta, ‘Tsakanin jiya da yau ban san mawuyacin halin da rashin ganinka ya jefa ni ba, don Allah ka ɗaga kirana ko zan samu sassauci a zuciyata.’

Baki ya ɗan taɓe yana ƴar dariyar da za’a kira ta yaƙe.

Wannan shi ne weakness ɗin Maryam da a yanzu ya gano, kuma da shi ne zai riƙa wahalar da ita idan ita ma ta ce za ta riƙa shiga hancinsa da ƙudundune.

A fili ya ce,

“Zan ɗaga kiranki My wife, amma sai kin ci gidanku kema.”

Sannan ya ci gaba da bibiyar sauran messeges ɗin, wanda kuma babu na Aisha ko ɗaya a cikinsu.

Haka Aisha take, idan zai shekara a waje ba za ta neme shi ba, bare har ta bashi hakuri, hakan kuwa na matuƙar damun shi. Ga mace har mace, amma ba kissa irin ta mata, ba wai bata yi ba ne, sai dai bai kai yadda zai ɗauki hankalin namiji ba.

Shi mutum ne mai son kissa, shi ya sa Maryam ta tafi da dukkan komai nashi.

Yanzu haka jin Maryam ɗin yake a ransa, kaso mai yawa na haushin ta da ya fara ji ya tafi. Aisha kuwa rashin damuwa da damuwarshi ya sa yadda take cunkushe a zuciyarshi ba ta motsa ba.

Samun kansa ya yi cikin duba pics ɗin Maryam da ke cike da wayarsa. ‘Nima ina jin damuwa da nisan da na yi da ke sweeeet heart. Ya faɗa a ransa.

Ci gaba da duba pics ɗin ya yi, wani wanda take kwance a cinyarsa ne ya sa shi lumshe idanu, saboda hoton ya yi kyau sosai.

Sallamar da aka yi mishi ce ta sa shi buɗe idanun tare da duban mai sallamar. Abokin kasuwancinsa ne mai suna K.B

“Ya Hajj.”

Ya faɗa yana dariya.

Sai da K.B ya zauna sannan ya ce, “Makkar nan dai Allah ya kai ni.” Khamis ya ce,

“Amin don Nabiyyi Rahmati, amma fa kai ne ba ka so zuwa ba.”

K.B ya ce,

“Allah ne dai bai kira ni ba, kuma ka san hidimar iyali ba ta barin kuɗi. Mata uku da yara goma ai ba wasa ba, school fees ɗin yara kaɗai cinye jari yake.”

Khamis na dariya ya ce,

“Wallahi kuwa, Allah dai ya rufa mana asiri.”

K.B ya ce,

“Amin ya Allah.”

Gaisawa suka yi. Sannan K.B ya jawo Food flask ɗin da ke gaban Khamis mai ruwan gold.

“Me ka ci ka rage?”

Lokaci guda kuma ya buɗa. Yana ganin sauran waina ya ce,

“Kayana sun tsinke a bakin kaba, yau ban yi breakfast ba na fito, gidana ya rikice, tun da Asuba suke faɗa, na gaji da rabo na bar musu gidan su kashe kansu.”

Dariya Khamis ya ƙyalƙyale da ita, amma ba don ya ji daɗin halin da K.B yake ciki ba, sai don tausayin kansu. Shi mai mata biyu ma sun fara rikita mishi lissafi, to ina ga mai uku da yara goma?

“Dariya ka ke mini?”

K.B ya faɗa bayan ya haɗe wainar da ke bakinsa.

Zama Khamis ya gyara tare da riƙe haɓa.

“A’a wane ni, kukan da ka kawo a gidan mutuwa ne ya sa ni dariya. Nima asubar fari na baro musu gidan.”

K.B ya ce,

“Faɗan su ma?”

Khamis ya ce,

“Wallahi kuwa, tara mata ko ɗora ma kai jidali.”

K.B da ya san jidalin gaske ne tara mata ya ce,

“Kai da yanzu ka fara?

Tambayar ni in ba ka labarin asalin jidali ne tara mata. Duk iya ƙoƙarinka sai wata ta ce ba ka yi mata daidai ba, kuma idan ka nemi hujja sai ka ji shirmen banza.”

Khamis ya ce,

“Na yarda K.B, shi ya sa ni dai daga biyu ba ƙari”

K.B na dariya ya ce,

“Ka karaya kenan?”

Khamis ya ce,

“Eh gaskiya, bana son hayaniya.”

K.B ya ce,

“Ni kam sai na cike huɗu da ikon Allah, iyaka idan suka kacame in baro musu gidan.”

Khamis ya ce,

“Ai kai dama ɗan rigima ne, ko ƙwarƙwara ka samu ƙarawa akan huɗun za ka yi.”

Dariya suka gaggaɓe da ita.

Sai da K.B ya gama cin sauran wainar sannan ya labarta ma Khamis musabbabin faɗan matansa. Wai Uwargida da Amarya ne suka haɗe ma ta tsakiya kai, don ta fi su samun kuɗi saboda tana sana’a, lokuta da dama ba ta jiran ya bata, sai ta ɗauka cikin kuɗinta ta yi ma kanta da yaranta hidima, shi ne fa suke jin haushi, suka haɗe mata kai, ba ruwansu da ita. Gulmar ta kuwa sai dai idan ba su haɗu ba, shi kanshi sun sha kawo mishi, don dai bai kula su.

To ana haka kuma faɗa ya kaure tsakanin Amarya da uwar gida, sai tonon asiri suke ma juna. Wai sun haɗa kuɗi a kai ma Malam don waccan ta daina samun kuɗi, shi ne fa uwargida ta kashe kuɗin.

Khamis da mamaki ya sa shi riƙe haɓa ya ce,

“Oh ni Muhammadu Khamis, wai me ke damun mata ne da suke hana junansu zaman lafiya? Ko da yake wani lokaci har da laifin mu maza.”

Ƙwafa K.B ya yi sannan ya ce,

“Duk laifinmu, su ma matan ai suna da kishi gami da rashin tsoron Allah na wasunsu.”

Khamis ya ce,

“Lallai kam, ni kaina sha’anin gidana ya fara bani tsoro wallahi, Allah dai ya daidaita mana su.”

K.B da ya kasa kunne don jin rikicin gidan Khamis, sai ya ji bai faɗa mishi ba. Khamis kuwa tunda bai faɗa ma mahaifyarshi damuwarshi ba, to babu wani mutum da zai iya faɗa ma wa.

“Amin.”

K.B ya ce, suka ci gaba da maganar iyalin. Daga bisani ma sai hirar ta koma kan kasuwancinsu.

Aisha da Maryam kuwa, kowa sai aikin shan ƙamshi da fizge-fizge take yi, da sun haɗu ba mai jin za ta iya ba ‘yar’uwarta hanya ta wuce saboda kowa ji take kamar ta shaƙare ‘yar’uwarta.

Habaici kuwa sun yada ma juna shi sau ba adadi. A cikin haka ne Maryam ta yi ta sakar mata habaici a kan yaɗa sirrinta a media da take yi. Sosai Aisha ta tsargu kuma ta ƙulu, sai dai ba ta tanka mata ba.

Yara na dawowa Aisha ta fara fashe gululunta. Maryam na cikin kallon MBC bollywood, aikuwa su Haneefa suka ce cartoon suke so. A gadarance Aisha ta ɗauki remote ta maida musu MBC 3, kuma ta ƙuduri Maryam na yin magana za ta kwaɗe ta, saboda shekarunsu ba ɗaya ba, Aisha ta girmi Maryam da ‘yan shekaru. Toh sa’ar da aka yi sai Maryam ba ta kula ta ba.

Sai dai suna yin mahaɗa a ƙofar kitchen, Maryam za ta shiga, Aisha kuma za ta fita suka gogi juna a gadarance, har Aisha ta bige ma Maryam hannu da plate ɗin da ke hannunta.

Ba wani zafi Maryam ta ji ba, amma neman magana ya sa ta juyowa tare da fizgo ma Aysha kafaɗa ta ce,

“Halan ciwon makanta ke damunki, har ki ke bige mutane ki wuce.”

Aisha ta ji haushin wannan fizga da Maryam ta yi mata, musamman da ta zo mata a bazata.

“Yarinyar nan idan ba gwada miki na yi ni uwarki ce a rashin kunya ba na lura ba za ki fita idona ba.” Tana rufe baki ta ingiza Maryam dake ta diddira ƙafa da karfi. Baya Maryam ta yi kamar za ta faɗi, Allah ya taimake ta ta riƙe handle ɗin ƙofar kitchen ɗin da sauri.

Sosai ta ji wannan bankaɗa har cikin ranta, domin bayan faɗuwar gaba sai da dan cikinta shima ya motsa, wanda ya haifar mata da riƙewar mara. Gam ta rumtse idanunta tare da ɗan duƙar da kanta saboda ita kaɗai ta san me take ji, cikin ranta ta rika faɗin ‘Wash Allah.’

Aisha kuwa tunda ta ga Maryam a wannan yanayi ta saɗaɗa ta wuce ɗakinta.

Maryam da ke tsammanin har yanzu Ausha na nan ta shiga tunanin me za ta yi mata wanda za ta rama. Zuciya ce ta ce mata ta rabu da ita, don in dai har za ta rama to sai ta ji mata ciwo, wanda kuma daga nan ba a san ina faɗan zai tsaya ba.

A hankali ta buɗe idanunta da suka koma jajaye. Da ƙyar ta cira ƙafarta ta juya tare da kashe gas, duk a daddafen ta wanke taliyar murjin da ta dafa.

Manja da yajin da ke cikin bowls ta ɗoro a kan taliyar tare da ɗangyasawa ta fito.

Ɗakinta ta so tafiya, sai kuma zuciya ta ce mata tunda falon ba na uban Aisha bane ta zauna a nan.

Nan falon ta zauna ta ci gaba da aika taliyarta da ta yi ja saboda yajin da ta cika.

Haneefa ce ta zagayo wurin Maryam, sosai taliyar ta biya da ran Haneefar saboda ta san daɗinta, a can baya tare suke ƙwalamarta da Maryam.

Maryam ta lura da tana so, sai dai ko mutuwa za ta yi ba ta jin za ta iya ba ta. Wani mugun kallo ta yi ma Haneefar tare da faɗin,

“Ya aka yi?”

Haneefa ta ce,

“Ba komai.”

Tare da shan jinin jikinta.

Maryam ta ce,

“To ɓace mini a gani.”

Kamar Haneefar za ta yi kuka ta juya ta tafi ɗakin Aisha. Faɗa mata ta yi Maryam ta koro ta, maimakon Aisha ta yi sababi, sai ta kama yi ma Haneefar faɗan me ya sa ta je wurinta, idan Maryam ta yi mata wani abu to ba ruwanta.

Har ila yau tsanar Maryam ta ci gaba da cusa musu, Haneef ne ya ce,

“Ni dai Mommy na daina zuwa.” Haneefar ma cewa ta yi ba ta sake zuwa, daga nan kuma ta roƙi Aisha ta yi musu taliyar murji da manja, amsa musu ta yi duk don ta lallashe su.

Maryam kuwa sai da cikinta ya ɗauka sannan ta shiga tsarin yadda za ta bi da Khamis, don har ta gaji da kiran shi tare da tura mishi text, saboda ta san ya gani, don har online ta gan shi a WhatsApp.

Ɗakinshi ta shiga ta yi mishi gyara na musamman, don tunda ta samu ciki ta rage kula da ɗakin.

Lokacin da ta gama har an fara kiran sallar la’asar. Wanka da alwala ta yi, sannan ta gabatar da sallah.

Make-up mai daukar hankali ta yi, sannan ta shirya cikin riga bubu ta shadda. Cikinta da ya turo rigar ne ya ƙara mata kyau.

Jikin tagar da ta saba tsayuwa idan tana cikin damuwa ta tsaya. Ƙasan ranta kuma tana ta addu’ar Allah ya maido Khamis. Ai kuwa addu’arta ta amsu, wurin ƙarfe biyar ta ga maigadi ya buɗe gate. hango shi ta yi ya nufi parking space, wani irin daɗi ne ta ji a ranta.

Fita ta yi suka yi suka haɗe a falo. Fuskarta ɗauke da wani irin yanayin da ba za ka kira shi fushi ba, huggin ɗin shi ta yi tare da cewa,

“Sannu da zuwa.”

Ido Khamis ya lumshe yana ci gaba da shaƙar ƙamshin da ke fitowa a jikinta.

Sai dai kafin ya buɗe har ta zare jikinta daga nashi.

Can ya hange ta tana ɗingishi ta shige ɗakinta, da tunanin me ya sa ta ɗingishi ya shige ɗakinsa shi ma.

‘Da kyau.’

Ya faɗa a ransa don ya san aikin gyaran ɗakin na Maryam ne.

Banɗaki ya faɗa ya yi wanka, yana fitowa ya ɗauki jallabiyarsa brown da ke kan gado ya zura, cikin ransa kuma yana faɗin ‘Yau ita ake so na sa kenan’ saboda Maryam ta ce in dai ranar girkinta ne ta fi son ya tsuke cikin ƙananun kaya, kamar yadda ita ma take tsuke mashi.

Fitowa ya yi falo, yana da yaƙinin Aisha ta ji dawowarshi, amma har ya fita shi da yara ba ta fito ba.

Bai kuma sa ran za ta fito ba. Shi kuma ko ɗakin Maryam da ta tarbe shi ba zai shiga ba, bare ita da ta ƙi fitowa.

Maryam kuwa tana hango shi ya dawo gidan saboda Magarib da aka fara kira ta ce a ranta ‘Yau sai na raba ka da wannan fushin.’

Alwala ta yi tare da gabatar da sallar magrib da kuma nafila raka’a biyu. Tana gamawa ta shiga kitchen ta ɗora soyayyen cefanenta a wuta tare da ƙara ɗan ruwa, tsakin masara ta wanke ta aje gefe, sannan ta matso da gyararren bushasshen kifinta a kusa. Spices da maggi ta sa a ruwan, yana tafasowa ta sanya kifinta da tsakin ta cigaba da juyawa, albasa mai yawa ta zuba a ciki ta juya. Sai da ya yi kauri sannan ta rage wutar ta fito.

Isha’i ta gabatar. Sannan ta koma kitchen, sosai faten ya yi kyau da daɗi, wanda kuma take sa ran Khamis zai yaba da shi, don faten tsakin masara yana cikin best foods ɗinsa.

Juye shi ta yi a food flask ta kai dining, sanna ta koma ta kwaso plates da spoons.

A gurguje ta koma ɗakinta ta yi wanka, maternity gown ce fara mai baƙaƙen flowers ta sanya, hular da ke kanta kuma baƙa mai ratsin fari. A falo ta samu Khamis, sosai ta lura da yadda yake kallonta, musamman cikinta da kuma fararen ƙafafunta da ke waje.

Ɗan russunawa ta yi sannan ta ce “Girki na jiranka”.

Murmushi kwance a fuskarsa ya ce,

“To ranki ya daɗe.”

Kusan a tare suka isa dining ɗin. Zama shi da yara suka yi, ita kuma ta yi serving ɗinsu. Har ta gama idanun Khamis na a kanta.Ta san haka za’a yi dama, zama ta yi suka ci faten, tana jin yadda shi da yara ke ta santi, amma ko kallon su ba ta yi ba.

Khamis ya yi mamakin yanayinta, ita ba fushi a fuskarta, sannan kuma ba fara’a take ba, tsaka-tsaki dai kawai. Ya yi niyyar cigaba da fushi da su, amma ɗan ɗauke kan da ta fara yi mishi ya sa shi janye na mshi fushin ba tare da ya sani ba. Yana cikin satar kallon ta ne ya ga ta tashi ta nufi ɗaki.

Har ila yau ɗingishin da take ne ya sa shi tambayar kanshi ‘Wai me ya same ta ne?’

A ggauce ya ke cin abincin. Surutu yara suka fara yi mishi, amma sam hankalinsa na wurin Maryam. Samun kansa ya yi cikin son zuwa wurinta don ya ji me ya same ta.

Yana gamawa ya nufi ɗakinta, kafin ya shiga Haneef ya rugo “Daddy ka zo mu yi kallo.”

Ya san ba za su shiga ɗakin Maryam ba, kuma idan ya tursasa musu akan su shiga ranshi ne zai ɓaci, don haka ya ce,

“Ok, ku tafi ɗakin Mammy, zan zo kiran ku mu yi kallon.”

Tafiya suka yi, shi kuma ya tura ƙofar ɗakin a hankali.

Kwance ya hangi Maryam a kan gado ta juya ma ƙofa baya. Sosai shape ɗin bayanta ya ɗauki hankalinsa, bai wani ɓata lokaci ba ya je gefenta kan gadon ya zauna.

Sunanta ya kira,

“Maryam.”

Sai da ta ɗan ɓata ‘yan daƙiƙu sannan ta amsa, cewa ya yi,

“Tashi zaune.”

Ba musu ta taƙarƙara ta tashi zaune tare da ɗan ware ƙafafu.

Ƙafafun ya kalla ya ce,

“Me ya same ki na ga kina ɗingishi.”

Kawai Maryam sai ta ji kuka ya zo mata,

“Matarka ce mana ta hankaɗa ni na kusa faɗuwa.”

Hankalisa a tashe ya ce,

“Ayshar da kanta?”

Cikin ransa yana fargabar kada a ce ƙudurinta na son zubar ma Maryam ciki na nan.

“Eh.”

Maryam ta faɗa, tare da bashi labarin yadda aka yi har Aishar ta hankaɗa ta.

Jin haka ne ya sassauta mishi fargabar, saboda da Maryam ba ta fara fizgo Aisha ba babu yadda za’a yi ta hankaɗa ta. Ce ma Maryam ɗin ya yi,

“Daga yau kada ki sake biye mata kin ji?”

Saboda ya fahimci Aysha jiran Maryam take ta yi mata wani abu, sai ta huce haushinta a kanta. Kai Maryam ta ɗaga alamar ‘Toh.’

Shirun da suka yi ne ya ba ta damar komawa ta kwanta. Tashi Khamis yayi ya nufi ƙofa. Wani irin ɗaci ne ya taso ma Maryam don a zatonta fita zai yi, sai dai tana jin ya sanya ma ƙofar key ta ji sanyi a ranta.

Idanu ta lumshe lokacin da ya kwanta a bayanta tare da rungumo cikinta.

Janye mashi hannu ta yi tare da yin magana a shagwaɓe.

“Nima na yi fushi.”

‘Yar dariya ya yi tare da maida hannun ya ce,

“Tuba nake bebiyo, tsakanin jiya da yau ban san mawuyacin halin da rashin ki a kusa da ni ya jefa ni ba, ki bari na raɓi jikinki ko zan samu sassauci a zuciyata”.

Sosai ta fahimci reply ɗin text ɗin ɗazu ne ya yi mata a fili. Take ta nemi duk wani haushi da take ji a ranta ta rasa. Sai dai duk da farincikin da take ji bai hanata ɗan ja mishi aji ba.

A susuce ya shiga bata haƙuri da kalmomi masu tsuma zuciya. Daga nan kuma ya faɗa mata bai jin daɗi idan ya ga suna faɗa ita da Aisha, fushin da ya yi kuma har cikin ransa ne, amma ya huce.

Haƙuri Maryam ta ba shi ita ma, tare da yi mishi alƙawarin ba za ta sake tsokanar Aisha ba, bare har su yi faɗa.

Ya ji daɗin haka ba kaɗan ba, yana son idan ya yi ƙorafi a karɓa kuma a gyara, shi ya sa kullum cikin son Maryam ya ke, saboda in dai zai ce ga laifinta, to kuwa za ta karɓa kuma ta bashi haƙuri.

Soyayyarsu mai daɗi suka sha a kan gadon. Ƙarfe tara na yi suka dawo falo da nufin kallon news. A kan cinyarsa Maryam ta ɗora kai shi kuma yana kallon News.

Aisha da mugun takaici ke ci ma rai ce ta fito, saboda su Haneef sun faɗa mata Khamis na ɗakin Maryam.

Ganin Maryam ɗin a kan cinyarsa ne ta ji ina wuta ta sa kanta.

‘Wallahi dole na raba mijina da wannan yarinyar.’

Ta faɗa a ranta tare da shiga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan.

Khamis ya ga shigarta a ƙufule, ya san laifi ne za ta ce an yi mata, to tun kafin ta tuhume shi sai ya sauke nashi girman kan, tana fitowa ya ce,

“Ji nan Aisha.”

Daga can ta ce,

“Ka san dai ba zan zo gabanka ba alhali wannan banzar tana nan.” Ta na faɗin haka ta nufi ɗakinta.

A cikin baccin da ya fara fizgar Maryam ne ta ji sa’adda Aisha ta ce mata banza, ba shiri ta buɗe idanu tare da danne zafin da ya taso mata a zuciya.

Khamis kuwa kai ya girgiza, lokaci ɗaya kuma ya maida dubansa ga TV. Ƙarfe goma na bugawa ya tada Maryam suka nufi ɗakinsa.

A kan gado ya kwantar da ita sannan ya fito, fitilun gidan ya kashe gami da sanya ma ɗakin Maryam key. Ya komawa ya kwanta shi ma. Bacci mai cike da aminci ne ya ɗauke su.

Aisha kuwa kaɗan ta rage zuciyarta ta buga a cikin wannan dare. Abin da ya tsaya mata a rai shi ne, wanda a ka yi ma laifi daban, wanda kuma ake lallashi daban.

Washegari Khamis na dawowa sallar asuba shi da Haneef suka wuce ɗakinta. Zaune suka same ta kan abin sallah tana tahiya. Zama ya yi a ƙasan carpet tare da jingina da sofa suna fuskantar juna, Haneef kuma ya haye gado ya kwanta.

Haneefa da ke ta bacci a kan gado Khamis ya duba, Aisha na shafa addu’a ya ce mata,

“Ita Haneefa ta yi Sallar ne?”

“Um um.”

Aisha ta faɗa a taƙaice, ya ce,

“To me ya sa baki tada ta ba?”

“Haneefar duka guda nawa ce da za’a wani tayar sallar asuba.” Aisha ta faɗa a ɗan hasale, don jiran shi take.

Khamis ya fahimci rigima take ji, don haka ya sassauta murya ya ce, “Ai don ta saba ne, kin ga a gaba tashin ta ba zai ma kowa wahala ba.”

“Uhm.”

Kaɗai ta ce, ta kuma ci gaba da jan carbinta tana ambaton ‘La’ilaha Illallah’ a ranta, Aisha mace ce mai yawan ambaton Allah, sai dai kishi da kuma ƙawaye ya sa ta matuƙar ja baya.

“An tashi lafiya?”

Khamis ya tambaye ta, duk da shi ya kamata ta fara gaidawa, a gumtse ta ce,

“Lafiya lau.”

Daga nan kuma ta ci gaba da jan carbinta, sai dai zuciyarta cike da jin haushin Khamis.

Ya fahimci haka, magana ya yi mata ya ce,

“Aisha na lura haushina ki ke jiko? To kada ki zarge ni a kan laifin da ban yi ba. Na san kina tuhuma ta akan kula Maryam, bayan tare kuka yi laifin, to ita ta iya bada haƙuri..”

Karɓe maganar ta yi ta ce,

“Ni kuma ban iya badawa ba ko?” Ya ce,

“Eh gaskiya baki iya ba. Maryam kuwa tunda ta fahimci na yi fushi ta shiga tura mini texes na ban haƙuri, duk da cijewar da na yi, amma hakan bai hana ta kula ni ba a lokacin da na dawo, ke kuwa ko kallon arziƙi, asali ma jira ki ke ni na zo inda ki ke.”

Baki ta taɓe tare da ɗauke kai, ta kuma ce, “Ita ta ga za ta iya.”

Khamis da ke mata kallon ta rako mata ya ce,

“Haka kika ce?”

Ta ce,

“Eh.”

A hasale ya ce,

“Aisha Kin dai ji haushi wallahi, shekara takwas, cikinta tara, kin kasa fahimtar yadda za ki lallashi mijinki idan ya yi fushi, amma ƙasa da shekara ɗaya wata ta fahimce shi kuma tana neman raba ki da shi, kuma a hakan kike kallon ana tauye miki haƙƙi.”

Tamkar Aisha za ta cije shi ta ce, “Ita ma ɗin da asiri da tsafi ta raba ni da mijin, sai kuma rashin adalcinsa shima.”

Cewa ya yi,

“Na baki dama ki yi duk irin asirin da take yi, wanda ba boka ba malam, ni kuma na miki alƙawarin zan riƙa yin abin da kike kallon rashin adalci ne. Wallahi ni ba zan wulakanta ki ba, amma ina shawartar ki da ki koyi sirrin zama da miji a wurin nagartattun mata.”

A tsaye yake sa’adda ya yi wannan maganar. Bai kuma tsaya saurarar surutan da take yi ba ya fice daga ɗakin.

Ɗakin Maryam ya shiga, inda ya same ta a gefen gado dafe da ciki. Zama ya yi gefenta tare da ɗora hannunsa a kan nata.

“Mene ne?”

Kamar za ta yi kuka ta ce, “Cikin nan na damuna, ba ka ji yadda nake ji a ribs ɗina ba.”

Cike da damuwar yanayin da take ciki ya ce,

“Oh sorry. ciki da ya tsufa dama sai an jure, ko mu je asibiti ne?” Kai ta girgiza sannan ta ce,

“Ranar Tuesday ai zan koma awo.” Ya ce,

“To shikenan ma.”

Da kanshi ya haɗa musu breakfast ita da yara. Girkin rana kuwa order ya yo musu. da dare kuma ita ta yi girkin da kanta.

Aisha kuwa tamkar za ta mutu, tana ganin yadda Khamis da Maryam ke ta sharholiya a cikin gidan. Maryam kuwa sai wata isa-isa take mata.

A ranar girkinta haka Khamis ya ƙaraci jiranta a ɗakinsa, amma har garin Allah ya waye ba ta je ba.

Asubar fari ya shigar mata, ƙorafin rashin zuwanta a ɗakinsa ya yi mata. Aikuwa ta ce,

“Kai da sake ganina sai na koyo zama da miji.”

Tare da ɗora ƙafarta ɗaya akan ɗaya, kasantuwar gefen gado take zaune.

Wani irin jim kansa ya yi, shi kam ya rasa yaushe Aisha za ta zama mace. Dafe kan ya yi tare da faɗin, “Na shiga uku ni Khamis.”

Aisha da ta turo ɗankwali gaban goshi ta ce,

“Wallahi tara ma ka shiga ba uku ba.”

Ranshi a mugun ɓace ya ce,

“To Allah ya fidda ni. Amma kam na ce baki iya zama da miji ba.

Da kin iya wallahi da tuni mun manta da wani faɗa, amma sai wani riƙo ki ke yi.”

Kofa ta nuna mashi,

“Idan ka san baƙar magana za ka faɗa mani to fice min daga ɗaki.” Sosai ta ba shi dariya, cewa ya yi, “Ni kike kora?”

Ta ce,

“Eh.”

Zama ya gyara a kan sofar da yake zaune sannan ya ce,

“To Allah ya baki haƙuri, ni kam in dai da gaske za ki koyo zama da miji, to ni kuma na baki damar fita duk inda kike so ki koyo.”

Maso zuwa birni, bare an aiko sarki na kira. Aisha na lura Khamis da gaske yake, ita ma ta maida gatsen da ta yi mishi da gaske duk don ta samu ƙafar yawo.

Gidan Abdul ta je. Ta kuma labarta ma Fatima abin da Khamis ya ba ta iznin fita a kanshi. Aikuwa ba ƙaramar shawara ta samu a wurin Fatima ba. Nan Fatima ta ke faɗa mata yadda ta raba Abdul da miskilanci a cikin gida, a da yadda kasan ba mijinta ba, ko hira basa yi. amma yanzu har shi ke kawo mata labarin abin da ya faru a waje.

Aisha da ta san Abdul ya canja ta ce,

“Ai ba cikin gida ba har a waje yaya Abdul ya canja.”

Saboda ko su ‘yan’uwansa bai cika yi ma magana ba, amma yanzu haɗuwa suke su sha hira a gidansu. Fatima ta ce,

“To shi fa namiji bai da wahalar canjawa a wurin mace in dai tana son zama da shi. Kowace mace fa tauraruwa ce, sai dai idan ba ta san yadda za ta fito da haskenta ba, ko kuma ba ta ga damar fito da shi ba. Don haka abu ne mai sauƙi ki ƙwato mijinki a wurin Maryam.

Idan ma ta ƙi saki ta ja, kema ki ja, sai ku yi ta jansa a tare, wadda ta jure sai ki ga ta karɓe mijin ita kaɗai.

Sosai Fatima ta ba Aysha shawarwari. Sai dai abin baƙinciki da takaici, tana zuwa gidan Jamsy waɗannan shawarwari suka bi ruwa.

Daga gidan Abdul can ta wuce. Aisha na ganin yadda Hannah, wato Amaryar Jamsy ta ƙara ƙasƙancewa, ta ji itama haka take son ganin Maryam.

A take Jamsy ta haɗa ta da Malaminta, ba kunya ba tsoron Allah, Aisha ta faɗa mishi so take ta raba Maryam da Khamis.

Daga can Malamin ya yi wasu tsubbace-tsubbacensa ya faɗa mata ko za su rabu to ba yanzu ba, sai dai ana iya cusa ma yarinyar tsanar Khamis ɗin.

A ranar dai sai da Aisha ta dangana da gidan Malamin, kuma shi ne karon farko a rayuwarta.

Babban Burinta shi ne a raba Maryam da Khamis ko ta halin ƙaƙa. Sannan Khamis ɗin ya zama mallakinta ita kaɗai.

Kuɗin da ta cire a P.O.S ta ba Malamin, shi kuma ya bata wasu laƙunƙunan da za ta sa ma Khamis. Maryam kuma ya ce da kanshi zai yi aiki a kanta.

Wani irin salo na musamman ta nuna ma Khamis, wanda mugun nufin da ke ranta ya makantar da ita lura da shi. Sosai ta samu kan Khamis har ya kusance ta.

Maryam kuwa ta daɗe suna chat ita da Haupha a daren. Nan take ba Haupha labarin Aisha ta hankaɗe ta, Haupha na masifa ta ce,

“Da ta ƙara taɓa ki, ki faɗa mana, wallahi har gida za mu iske ta mu ci ubanta.”

Maryam na dariya ta ce,

“An gama Yayata, tunda ina da ku to ƙaryarta.”

Hira suka sha sosai. Sannan Maryam ta kwanta, sosai baccin da ke cike da idanunta ya hana ta addu’ar kwanciya.

Bacci ya fara fizgarta ne ji kamar ana knocking ƙofarta, muryar Khamis ta ji yana cewa,

“Buɗe ƙofa Mairo.”

Da tunanin me ya zo yi ɗakinta ta sauka da ƙyar daga kan gadon,

Faɗuwar gaba ce ta riske ta lokacin da za ta buɗe ƙofar, dakewa ta yi ta buɗe, abin mamaki sai ta ga ba kowa,

“Abban bebina?” ta faɗa, a zatonta Khamis ya koma. Wata irin muguwar dariya mai rikitarwa ta ji tana fitowa a kowane saƙo na gidan.

A tsorace ta yi baya tare da rufe ɗakinta. Durƙushewa ta yi tana haki. Cikinta da ke wani irin juyi za ta riƙe, ko kuma muguwar dariyar da take jin ta a kusa da ita..?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kishiyar Katsina 14Kishiyar Katsina 16 >>

1 thought on “Kishiyar Katsina 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×