Kukan da Khairi ke ta faman zabgawa Momy ta faman lallashin ta yasa Usman da ke zaune yana faman duba takardun ɗaliban sa miƙewa, falon ya fito a nutse ya ɗauki yarinyar Momy bata ce komai ba zaton lallashin yarin yar zai yi ɗakin Hafsa ya nufa inda ya fito riƙe da hannun Khalil wanda ke ta wasa abinsa.
Tsallen murna yaron yake ya biyo Usman ɗin a baya yana tsalle suka fice a baya ya sanya Khairin shima Khalil kusa da ita yaja ya zauna inda Usman ya hau mazaunin driver ya ja motar Khalil ya le. . .