Skip to content
Part 21 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Cike da ɗoki Hafsa ta tashi, kaya kala biyu ta ɗauko in da ta shirya ta saka doguwar abayar ta golden ne kalar ta, a falo ta tarar da Momy tana ta famar mitar jikokin ta da aka mayar da alamu har lokacin Usman bai yadda sun haɗu ba wannan yasa Hafsa saurin wucewa Dinning area ta zubo abincin ta tare da komawa ɗakin ta dan bata son taka sawun ɓarawo tasan kure kaɗan zatai Momy ta hau ta da faɗa.

Tana zaune tana duba wasu formulas dan bata son in Muktar ya zo ya tambaye ta basic abubuwa na course ɗin ta hau zare ido, Sallamar Hidaya yasa ta maida littafin tare da sakin murmushi, “yanzu nake mita a raina kinƙi zuwa bayan na faɗa miki in uku tayi inada abinyi”

Duban agogo Hidaya ta yi kafin ta ce ” ai ban makara ba, tashi muje Allah dai ya sa Bilkisun ta shirya”

Mayafin ta da ke gefen gado ta naɗa a kanta kafin ta ce “amin dai” Sallama suka yiwa Momy suka fice.

A ƙofar gate ɗin su Bilkisu suka tsaya ko minti uku basuyi ba ta fito, sai da suka hau titi sannan Hafsa ta ce “gidan Gwaggon zamu fara zuwa ko kuwa kasuwar kurmin?”

Hidaya ce ta ce “no it’s better mu fara zuwa kasuwar in ya so ko irin munga wani abin ma yi mata tsaraba”

Murmushi Hafsa ta yi Haka ne kuma ta faɗa kafin ta maida kallon ta ga Bilkisu wadda ta maida hankalin ta sosai ga bakin hanya tana tunani.

Hafsa ce ta ce ” Maddam mai ke damun ki tunda kika shigo ina kule da ke you are not on your usual self”

Murmushi ta yi tare da ƙara kallon gefe, kafin tace ba komai kawai banjin daɗi ne”

Shiru Hafsa ta yi sai kuma tace “Tariq ne?”

Ɗan kallonta ta yi kamar zata ce eh sai kuma ta kalli Hidaya wadda idanun ta ke a kanta, girgiza kai ta yi “no kawai banjin daɗi ne”

Kafun Hafsa ta ce wani abu Hidaya ta yi caraf tace ” tunda dai sabida ni ba zaki faɗi damuwar ki ba sai ki dawo normal in mun rabu kya cigaba da damuwar”

Hafsa ce ta yi dariya ” No badan ke bane dan Malam Musa ne, kar yaji ta mato kan namiji” dariya sukai Har Malam Musan wanda ya ce “ah in dan nine sai in toshe kunnuwa” ya faɗa yana ƙokarin faka motar suka fito zuwa kasuwar shi kuma ya fito ya samu tebur ya zauna.

Sosai sukai siyayya kusan rabin kayan na Hidaya ne sabida makaranta da zata koma, yayin da Hafsa da Bilkisu kusan kayan girki ne sai akushi da ya burge su suka siya, Bilkisu ta fara siya sabida Tariq nason har kar gargajiya tana gani ta tuna da shi in yazo wannan satin ciki zata zuba masa abinci abinda ta fara ayyanawa a ranta kenan.

Kusan sai wurin ɗaya suka bar kurmi suka wuce gidan Gwaggo tunda suka baro kasuwar Hafsa ke duba agogo bata son uku ta mata a waje kar Muktar yazo bata nan ya zama stranded dan tasan Mum ba lallai ta wani yi welcoming din sa yaji normal ba.

Tunda ta hango kofar gidan ba tabar Malam taji daɗi dan shine kawai zai tsayar da ita yace sai sun tsaya sunci abincin rana kan su tafi ganin ba tabarmar tasan bayanan.

Hannun ta rike da kayan da ta sayo musu gefen ta Bilkisu ce Hidaya na daga ɗan bayan su, a hankali ta ce “kin ƙi dai faɗan meke damun ki ko?”

Itama shigen irin yadda ta yi maganar ta kwata ” zamuyi waya anjima,” ta faɗa tare da yin sallama sakamakon zauren da suka shiga.

Halima na tuƙa tuwo Gwaggo na yanka alayyahu da alamu na miyar tuwon ne, suka shiga “lale maraba da ƴar gudun hijira” Gwaggo ta fada tana murmushi.

Murmushi Hafsa ta yi ba tare da ta ce komai ba ta aje ledar Hannun ta ta shige ɗaki Halima ta ce “to walllahi karki mun ta’adi”, ta faɗa cikin ɗan ɗaga murya.

“Kaya na kawai zan ɗauko” ta faɗa daga ɗakin, yayin da Hidaya da Bilkisu suka zauna gefen Gwaggo suna gaishe ta fuskar su ɗauke murmushi.

Fitowa ta yi rike da adakar ta ta ɗan rissina ta gaishe da Gwaggo kafin ta ce zaman mai kukai na faɗa muku sauri fa nake”

Hidaya ce ta ce ni gaskiya tuwon nan ya burgeni sai na ci”

Hararar ta Hafsa ta yi “ki ci me, kin taɓa ganin inda mutun yaje gidan mutane rana tsagal tsagal yace zaici abinci basu sa da shi ba, Please taso mu tafi”

Gwaggo ce tasa salati ” ungo nan Bebilo, wato gidan namu ne gidan mutane ko?”

Dariya Bilkisu tasa “Hajiya Bebilo sai kiyi haƙuri muci tuwon nan”

Hararar Bilkisu Hafsan ta fara yi kan ta ce ” kaji Gwaggo da ku aljanu ne?”

Girgiza kai kawai Gwaggo ta yi tana murmushi ” in ba zaki ci ba ke kya iya tafiya” inji Halima.

Turo Baki Hafsan ta yi “ai walllahi da akwai abin da zan faɗa miki na fasa”

Rufe tukunyar tuwon Halima ta yi tare da faɗin “ai zanzo har gida inji komene”

Sai da suka ci tuwon sannan suka baro gidan, tuburewa Hafsa ta yi ita za’a fara kaiwa wannan yasa sai da aka sauke ta sannan Malam Musa ya wuce da su Hidaya.

Tana shiga gida Sallah kawai ta yi, ta shiga kitchen simple abinci ta yi da nemon abarbar da ta sayo ta sanya a fridge kafin ta faɗa banɗaki ta yi wanka.

Kayan ɗazu da ta ciro ta ɗauko ta sa a jikin ta suma ɗin dai doguwar riga ce sai dai wannan na atamfa ne, sun mata kyau sosai sai da tayi sallar la’asar sannan ta ɗebi littattan ta ta yo farfajiya can kasan bishiya ta samu wuri ta zauna ta fara duba wani novel lokaci lokaci ta duba kallon bakin gate.

Shi kuwa Muktar Bayan ya kammala wankin Inna kayan sa yau dubawa kusan duk kayan da yake sawa yau da kullum basu masa ba wannan yasa shi buɗe akwatun da yake sanya kayan da sai Friday ko ɗaurin aure yake sawa, rasa na zaɓa ya yi kafin can idanun sa su faɗa kan wasu sabbin shaddar sa sky blue da kuma milk tsai ya bisu da ido bayan ya fito da su dakyar ya iya yanke shawarar blue ɗin zai saka duda a goge suke da ya ware su yaga sun ɗan cukurkude wannan yasa shi ɗauka ya yi tsakar gida.

A ruwan sitati ya tsoma su sai da ya shanya sannan ya fice, daga gidan bashi ya dawo ba sai wurin biyu ya tarar sun bushe Allah ya taimake shi da wuta ya goge abinsa sannan ya shiga wanka.

Sosai ya yi kyau tun kan ya sanya hula akansa kyansa da cikar kamalar sa suka fito, sai da ya ci abinci sannan ya bar gidan zuwa Gidan su Hafsa.

Ya kusa minti biyar a ƙofar gidan zuciyar sa na tunane tunane kafin ya daure ya iya bugawa, kamar jira Baba Bala yake ya buga kodan Hafsa ta sanar da shi zuwan Malamin nata oho, ya buɗe a mutunce suka gaisa ya ce “Malam Hajiya Hafsa ko?”

“Eh” Kawai Muktar ya ce yana murmushi.

Nuno masa inda take ya yi a nutse ya fara takawa, kamshin turaren sa ne ya sanar mata da dosowar sa wurin ta tun kan gangar jikin sa ta ƙaraso cike da annurin fuska ta miƙe sukai sa’ar saka idanun su cikin na juna, da hanzari Muktar ya cire nasa domin faduwar gaban sa ne ya ƙaruwa lokaci guda lallausan murmushin dake ɗauke fuskar Hafsa ya narkar masa da tunani.

Cikin hanzari ya tunatar da kansa ba ajin su guda ba, karatu ya zo koya mata neman kuɗi ya kawo shi ba soyayya ba, wannan ya bashi kwarin gwiwar ƙarasawa tare da yin murmushi.

A nitse cike da girmamawa Hafsa ta gaishe shi tare da faɗin ina zuwa ta faɗa kafin ta yi bangaren da zai sada ta ga falon su, dadduma ta ɗauko tare da lemo da snacks ta fito ɗakin Momy ta leƙa ta faɗa mata Malamin nata ya zo sannan ta koma farfajiyar.

Can gefe tsakiyar fulawoyi ta shinfida musu dardumar ya tada Sallar la’asar dan tun yana hanya akayi sallar ita kuma ta koma ta ɗebo takardun ta kan kujerar da ta taso.

Sai da ya idar suka kuma gaisawa “kinsan tun jiya nake ɗokin inzo mu ga juna, kwana biyun da mukai bamu haɗu ba duk ba daɗi”

Murmushi ta yi cike da zumuɗi ta ce “ashe bani kaɗai ba, duk sai nake jin kamar mun shekara da sabawa” ko mai suka tuna oho sai kowa ya shiga mutsu mutsu insa ta hau ƙoƙarin zuba lemo shi kuma ya hau bubbuɗe takardun da ta ajiye.

Lemon ta aje masa gaban sa sannan ta ce “ga lemo” ta faɗa tare da turo masa farantin da snacks ɗin suke.
Murmushi ya yi “kinsan Allah a ƙoshe nake.”

Dariya ta yi “to ba abinci bane ai dan haka gaskiya sai ka ci”

Dariya ya yi ” kinsan wani abu da karatu bama fa iya Physics ba, no koma mene, sai kin sa aranki you can do it, kin cire tsanar sa aranki shine zaki iya gane shi yadda ya kamata” ya faɗa a niyar sa na kawar da batun cin abinda ta kawo.

Murmushi ta yi ” tab Physics din zan so, over my dead body”

Dariya ya yi tare da tsare ta da ido “Hafsa kalle ni” ya ce
Duban sa ta yi na ɗan sakwanni tare da saurin ɗauke idanun ta dan gani ta yi ya mata kwarjini sosai “dole kiso Physics in har kina son in koyar dake dan magana ta gaskiya ba zanzo ina koya miki abu kina jin haushi na nida shi ba”

Dariya ta sa ” ah ai bazanji haushin ka ba, kawai I can’t like the course, gaskiya”

Iska ya furzar kafin ya ce “kisa to nine physic in ko kuma wani da kike so, let say your boyfriend ya faɗa” can ƙasan ransa wani abu ya soke shi sauri ya yi ya daure “in kika sa wanda kike so ne zakiyi kokari ki so shi, asannu in kin fara sonsa everything about the course zai zamar miki simple”

Ɗan ɗaga girar ta tayi kamar mai tunani sai kuma ta yi murmushi “tom shikenan zanyi yadda kace baka sha lemon ba” ta faɗa tare da matso masa da shi kusa.

Hoo Hafsa rikici ya daɗa tare da kurɓar lemon wanda sanyi da daɗin sa ya daki kwanyar sa baima san lokacin da ya kuma kurba ba.

Sosai sukai karatun ba laifi ta fahinta dan har Questions din da ya bata ta amsa ta iya amsa uku cikin biyar dedai wannan yasa shi jin daɗi dan sam baya son yana koyarwa ba’a ganewa sai wurin shiga sannan ya tafi.

<< Ko Da So 20Ko Da So 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×