Yadda ta gaji jiya sabida yawon da suka sha, yasa take ji tamkar kar ta tashi, sai dai kasancewar ta yi missing ɗin class ɗin BIO1202 da yawa yasa ta daurewa ta tashi tsaf ta shirya cikin doguwar rigar ta Ja da aka mata adon ruwan gold ta yi mata kyau sosai kofin tea ɗin da ke hannunta ta ajiye lokacin da taga bakwai saura minti goma tasan in ba zuwa ta yi ta tashi yaya Usman ba tas zata makara, Malam Musa ya je garin su wannan yasa take mannewa yayan dan ya sauke ta kafin ya wuce faculty. . .