Da ƙyal Hajiya Mairo ta iya kai kanta gida, saboda tsananin tashin hankali akan halin da ta ji Habeeb na ciki, Sannan ga ƙarin baƙin cikin da sai a wurin abokan gabanta ne ta ji.
A bakin ƙofar ɗaki ta tsaya tare da jawo ƴar ƙaramar kujera ta zauna tana fuskantar Gwaggonsu dake zaune can cikin ɗakin, ɓangare ɗaya kuma hannunta ɗauke da maficin kaba tana saƙawa.
Ganin yanayin Hajiya Mairo ya sa Gwaggo aje maficin dake hannunta, Sannan ta yi magana cikin sigar damuwa.
“Hala basu baki Alhajin kun yi magana ba?”, don ta san abu ne mai wahala su kwashe ta lafiya da su Asabe, saboda kowa jiran kowa yake.
Jiƙaƙƙun idanunta ta buɗe, sannan ta yi magana cikin kuka “Mun yi magana da Uwanin.”
“Toh ya jikin Habeeb ɗin” Gwaggo ta yi saurin tambayarta.
Wata irin bugawa ƙirjinta ya shigayi, gaba ɗaya ta fidda rai da Habeeb saboda aiki a zuciya ba kamar aiki a ƙafa ko hannu ba ne.
“Habeeb sai wani ikon Allah ya rayu, yanzu haka aiki ake mashi a zuciya” Idanunta cike da ƙwalla ta ƙarasa maganar.
Hannu Gwaggo ta shiga tafawa tare da sallallami ta ce “Oh muna ga rasulu mata su ƙi maza, wane irin ciwon zuciya ne ya samu Habeeb haka.”
Shiru Hajiya Mairo ta yi, itama cikin ranta tana tunanin sanadin wannan ciwo na Habeeb.
“Kai mai rai dai yana cikin tashin hankali, Allah ka ba Habeeb lafiya ka sa a yi aikin a sa’a,” Gwaggo ta faɗi haka tare da taƙarƙarawa ta fito waje.
Bakin ƙofar itama ta tsaya tare da jingina bayanta da bango, lokaci ɗaya kuma idanunta na kan Hajiya Mairo da ke ta sharɓar kuka, wanda ba na komai ba ne sai na fargabar rasa tilon ɗanta.
Cikin sigar lallashi da tausayawa Gwaggo ta ce “Ki dena kuka Mairo, da ikon Allah zai samu sauƙi.”
“Yanzu don Allah gwaggo abin da Alhaji ya yi mani ya kyauta, a ce har rashin lafiyar Habeeb ta kai wannan mataki, amma ni mahaifayarshi bani da arzkin da zai faɗa mani, duk don taƙamar bamu tare, toh wallahi akan wannan ba zan taɓa yafe ma shi ba.” Kuka mai tsuma zuciya ne ya ƙwace mata, ita kaɗai ta san irin tashin hankalin da take ji a ranta, wanda bata ƙi ta buɗe ido ta ga Habeeb a gabanta ba.
Gwaggo kam ta san ba inda Alhaji Mainasa ya yi rashin kyautawa, tunda da kuɗinta ne ta sayi duk abin da ya yi mata, kuma in dai ramuwa ce, toh a cikin goman abin da ta yi mashi, bai rama ko ɗaya ba.
Ɗan shiru Gwaggon ta yi, cikin ranta kuma ta ƙudiri faɗa mata gaskiya ko da zata ji haushi, mai yiwuwa ta gane tun kafin wuri ya ƙure mata.
Ajiyar zuciya Gwaggon ta sauke sannan ta ce “Mairo a wannan lamari fa ke ki ka ja ma kanki.”
A ɗan fusace ta ce, “Kamar ya ni na ja ma kaina Gwaggo?” Ta ɗan ji haushin maganar, wanda kuma bai damu gwaggon ba.
Amsa ta bata da “Ta hanyar kashe aurenki, yanzu idan da kina gidanki haka zata faru? Ke kin san ƙafarki ƙafarshi zaku gano ɗanku, toh son zuciya ne ya kai ki ya baro, akan abin da bai taka kara ya karya ba. Yanzu ko da sharri ne aka yi ma Habeeb, ai da yanzu abin ya wuce, bare kuma yaran yanzu baka shaidar su.”
Haƙiƙa kam da a gidanta take, toh ko da tsiya ne sai ta je, bare kuma ta arzikin ma zata je tunda Alhaji Mainasara mutum ne adali.
Ko kusa ba ta yi ja a cikin zancen gwaggo ba, domin ta tafka kuskure a rayuwarta. Nadama ce wadda tuni ta zame mata jiki ta shiga yi ƙasan ranta, bangare ɗaya kuma a zahiri ta na ta kuka, yanzu abincin da zata ci ma mai kyau ma neman gagararta yake, saboda kuɗin dake gare ta ba su da yawa, balantana kuma sauran abubuwa na more rayuwa, waɗanda bata san matsalarsu ba a lokacin da tana gidan aurenta.
Zancen zuci ta shiga yi “Haƙiƙa na zalunci kaina, kuma na zalunci mijina, wanda wannan kadai bai isa ya zama sakayya ba.”
Tsoro sosai ya kama ta, saboda ta ga halin da Hajiya Sa’a ta faɗa, wanda idan bata yi gaugawar istighfari ba, toh sai ta fada a mahiyinsa, saboda ta cutar da mutane masu yawa, tun daga gwaggo dake gabanta, wadda suka cutar ita da ƙannenta mata, sakamakon auro ta da mahaifinsu ya yi bayan mutuwar mahaifiyarsu, makirci iri-iri, kai hatta ƙanensu wanda suke uba ɗaya sai da suka kusa kashewa don yana namiji, saboda a ɗakinsu ba maza.
A bangaren Alhaji Mainasara ma ya ci mugun abu na asiri. Sannan ga satar mashi dukiya da ya zame mata jiki, ba damar ya shigo da kuɗi a gida, ba tare da ta ɗibi kasonta ba, tun yana cigiya har ya dena, daga ƙarshe ma ya dena shigo da kuɗi a gida sai wanda za’a buƙata.
Toh yanzu ga makomar dukiyar satar nan waɗanda suka fi su mugun hali sun kwashe. Uwani kuwa yanzu haka akwai layu dake cikin ɗakinta, wanda ake bata tsoro don ta bar gidan.
Kai tsayawa faɗin mugun halin Hajiya Mairo barnar baki ne, don haka ba ta ga komai ba muddin ba ta nemi yafiyar mutane ba, musamman su Asabe da ta san Habeeb ne ya yi ma Jummai ciki, sabodo hoton Ahamad da na Habeeb ɗin basu da maraba, amma don kada ta bada kai a wuraren abokan gaba, sai ta yi ƙememe ta ce ba shi bane, sannan ta haɗa su da bita da ƙullin tozarci da wulaƙanci, wanda ya yi sanadin mutuwar Malam Amadu.
Duk a zaton gwaggo kukan da take akan Habeeb ne, lallashinta ta shiga yi, ta ce “Ki yi haƙuri, anjima zan je gidan Asaben sai a bani Lambar Alhajin, ni zan mashi magana ya taimaka ki tafi wurin ɗanki, tunda jiyyar ɗa sai uwa.”
Haka kuwa aka yi, yamma na yi Gwaggo ta dogara sandarta ta nufi gidan Asabe, cikin girmamawa suka tarbe ta, don duk tsaurin idon Asabe bata yi ma tsoffi rashin kunya.
Number Alhaji Mainasara Gwaggo ta buƙata, Asabe ta ce “Toh Mairo kam ta ci arzikinki gwaggo, da ba za’a bata number ba, ta je can wurin wani ta nema, tunda ba mu muka ɗora ma ɗanta ciwo ba, kuma muddin tsautsayi ya sake kawo ta a gidannan, toh sai mun bige ta wallahi”, hannunta na danƙwanshin ƙasa ta ƙarasa maganar.
Ɗan kaɗa kai Gwaggo ta yi tare da gajeren murmushi mai sauti ta ce “Toh ni kuwa na gode da wannan arzki da Mairo ta ci a dalilina,” ƙasan ranta kuma tana ganin duk ƙuruciya ce har yanzu bata sake su ba, shiyasa suke ta cutar kawunansu basu sani ba.
Number Alhajin haɗe da ta Habeeb Uwani ta rubuta ta bata, godiya ta yi musu, sannan ta kama sandarta ta miƙe da nufin tafiya, Abincin suka ce ta jira a zubo mata, amma ta ce a ƙoshe take. Godiya ta yi musu sannan ta dogara sanda ta fice daga gidan.
A ƙofar gida ta taras da Hajiya Mairo, don ba zata iya zama cikin gidan ba, number ta karɓa aka sanya a cikin wayar jikan gwaggo, sai dai ba wadda ta samu shiga, duk wayoyin a kashe suke.
Ido ta lumshe lokaci ɗaya kuma tsoron da ke cikin ranta yana ƙaruwa. Bakinta na kyarma ta shiga faɗin “Allah ka jiyar da ni alkhairi dangane da ɗana, ka bashi lafiya mai ɗorewa Allah.”
“Amiin ya Allah.” Gwaggo ta ce, sannan suka shiga cikin gidan su duka.
A dai-dai wannan lokaci ne kuma Alhaji Mainasara ya kai maƙura wurin kai kukansa a wurin Allah Mai Girma da Ɗaukaka, domin ya ba ɗansa Habeeb lafiya.
Tunda ya yi sallar la’asar hannunsa ke sama yana ta kwararo addu’o’i, don a yanayin da aka shiga da Habeeb a ɗakin thiyater, ba lallai ne ba a fito da shi da ransa.
“Allah ka tashi kafadun Habeeb, Allah kada ka raba ni da ɗana, duk da shi mai laifi ne a wurinka, ka yafe ma Habeeb laifukansa, sannan ka warkar da shi daga ciwon da ka ɗora masa ya Allah,” addu’ar da bakinsa ke ta maimaitawa kenan, bayan yabon Allah da kuma Salatin Annabi S.A.W da yake ta haɗawa da su acikin addu’ar.
Yana gamawa ya shafa, tare da dafe kansa da ya yi masa jingim saboda kuka. Yana nan zaune magarib ta yi, ita ɗin ya tashi ya gabatar, Isha’i ma tana yi ya tashi ya gabatar da ita.
Asibitin ya tashi ya nufa, shigarsa kuma ta yi daidai da lokacin da aka fiddo Habeeb daga ɗakin thiyater sakamakon gama aikin da aka yi a wannan lokaci.
Hankali tashe ya dafe gadon da Habeeb ke a kai suka cigaba da turawa shi da Nurses da kuma su Isma’il, lokaci ɗaya kuma idanunsa na a kan Habeeb ɗin wanda ya zama tamkar gawa.
A daidai ƙofar ɗakin da za’a shiga da Habeeb Nurses suka dakatar da su, domin a wannan yanayin likitoci da Nurses ne kaɗai aka yadda su shiga.
Yana ji yana gani aka rufe ɗakin bayan likitoci sun rufa ma gadon Habeeb ɗin baya.
Tamkar mace ya koma a wurin gaza ɗaukar nauyin raɗaɗin da ke ransa. Kuka sosai ya riƙa yi, wanda ba wanda ya ga laifinsa kasantuwar duk an ga yanayin da aka shigar da Habeeb, su Isma’il ma kukan suke yi, aka rasa wanda zai ba wani haƙuri. Hakan ya nuna tasirin da Habeeb yake da shi a cikin zuciyar mahaifinsa da kuma abokansa.
Alhaji Mainasara yana matuƙar son Habeeb, son da ko da za’a haife masa duniya toh ba zai so sauran yaran kamar yadda yake son Habeeb ba. A can baya ya juya masa baya ne don ya nuna masa girman kuskuren da ya aikata.
A wurin abokansa ma suna ji da shi saboda ƙoƙarin da yake da shi a fagen karatu, sannan kuma ya iya mu’amala da mutane, kasantuwar bai cika fito da halinsa na rainin wayau ga wanda yake son zama da shi ba.
Addu’a sosai suka cigaba da yi mashi, ɓangare ɗaya kuma suna kallon yadda likitoci suka zagaye shi ta glass.
Dr. Umar ne ya fito, haƙuri sosai ya ba Alhaji Mainasara tare da tabbatar mashi da akwai alamun nasara a cikin aikin da ikon Allah.
Godiya Alhaji Mainasara ya yi mashi, don tabbas ya yi ƙoƙari wurin ganin Habeeb ya samu lafiya ba tare da an yi masa aiki ba, sai dai kuma abin da Allah ya so ba makawa sai ya faru.
A ɓangaren su Alhaji Lawwali kuwa, tuni sun yanke hukuncin kashe Jummai tunda taƙi yarda ta shiga ƙungiyarsu, duk da kuwa baƙar azabar da suke gana mata.
Cikin muguwar siffa shi da Hajiya mai gidan abinci suka bayyana a gabanta, lokacin kuma tana ɗaure a jikin wannan icce na ƙaya.
“Ke mai taurin kai ko, an yi maki tayin ƙungiya kin ƙi karɓa, ƙarshe ma kuka kai mu wurin mai magani, toh zamu nuna maku ƙaryar mai maganin mu kashe ki, sannan mu koma kan waɗancan dangin naki suma mu kashe su”, wannan doguwar magana Hajiya mai gidan abinci ce ta faɗe ta, cikin isa da kuma gadara.
Shi kuwa Alhaji Lawwali kafe ta da jajayen idanunsa ya yi, wanda babu alamar ɗigon imani a cikinsu, cikin ransa yana jin baƙincikin rashin samunta a matsayin mata.
Kallo mai cike da tsana Jummai ta jefe su da shi, sannan ta ttaro yawun bakinta da ya garyawa da jini ta watsa ma Hajiya mai gidan abinci a fuska, sannan ta yi magana da shaƙaƙƙiyar muryarta ta ce “Idan akwai abin da yafi kisa, toh ku yi mani shi don ba zan shiga ƙungiyarku ba.”
Nuna su Aunty da take hange daga nesa suna zagaye da gangar jikinta ta ce “Waɗancan sun fi ƙarfinku wallahi, kuma ku sani su ne zasu ga bayanku, ba ku ne zaku ga bayansu ba da yardar Allah.”
Rufe bakinta ya yi daidai da lokacin Hajiya mai gidan abinci ta fizgo mata gashin kai da ƙarfi “Ke ƴar banza, Uwarki kika watsa ma yawu ba ni ba”, a yadda ta ƙwalalo idanu tana magana, kai ƙwayar cikinsu faɗowa zata yi ƙasa.
Duk da azabar zafin da Jummai ke ji sakamakon damƙar gashin bai hana ta maida ma ta martani ba “Wallahi ke na watsa mawa, domin ke dabbace ba mutum ba, muguwa azzaluma, ku sani ƙarshen zaluncinku ya zo.”
Shi kuwa Alhaji Lawwali sai ƙara tsuma yake da baƙinciki, saboda mugun taurin kan Jummai.
Sarƙar da ke hannun Hajiyar ya fizge tare da haɗa wuyan Jummai da wannan icce ya cigaba da ɗaurewa, lokaci ɗaya kuma bakinsa na faɗin “Kashe ki zan yi na huta, yadda ban same ki ba, haka wancan likitan dake kwana da tunaninki ba zai same ki ba,” yana magana yana cigaba da ɗaure ta.
Ita kuwa ta sadaƙas da kwananta ya ƙare, kuka ta nema a cikin idanunta da ke ta ƙara fitowa saboda zafin maƙara amma ta kasa samu.
Neman agajin Allah ta shiga yi a cikin zuciyarta, sannan ta haɗa da kalmar shahada domin jiran lokaci kawai take.
A sadda hankalinta ya fara gushewa daga jikinta ne ta tsinkayi wasu halittu, waɗanda baza ta iya faɗin kamanunsu ba. Da gudu ta ga sun durfafo kan su Alhaji Lawwali tare da dannesu suka cigaba da cizo suna yagalgala naman jikinsu, daga nan kuma bata sake sanin inda kanta yake ba, domin har a lokacin wuyanta ɗaure yake da sarƙar.
Aunty da gangar jikin Jummai ke gabansu ta dubi Ameer da kamanunsa suka sauya saboda tashin hankali ta ce “Ameer ƙila kafin goben ma yarinyar nan ta mutu”, domin motsin da take yi ma ta dena.
Idanunsa da suka ƙanƙance ya lumshe, sannan ya riƙe wrist ɗinta don jin idan tana da rai, halbawar da jijiyarta ke yi ne ya sa shi sauke ajiyar zuciya, cikin raunin murya ya ce “Insha Allah ba zata mutu ba Aunty, komai ma ya zo ƙarshe, tunda malamin da zamu kai ta wurinshi babban malami ne wanda Jama’a sun gamsu da aikinsa.”
Kasa cigaba da magana Aunty ta yi, sai dai kuka kawai, don lamarin rashin lafiyar Jummai kullum ƙara muni yake.
Kusan a kanta suka kwana, ba abin da suke mata sai addu’o’in waraka suna watsa mata, cikin ikon Allah kuwa sai gata ta farfaɗo, sai dai kuma ba abin da take sai kuka tare da faɗin “Wuyana”, Aunty ta ce “Me ya samu wuyan kuma?”.
Jumman ta ce “Ɗaure ni suka yi da sarƙa a wuyan zasu kasha.”
Nannuyar ajiyar zuciya su duka suka sauke, cikin muryar tausayawa Ameer ya ce “Toh ki yi haƙuri, wuyan zai dena ciwo.”
Kuka ta cigaba da yi tana faɗin “Toh ku kwance ni.”
Addu’a suka cigaba da tofa mata, tare da lallashinta da magana mai daɗi.
Washe gari tunda safe suka shirya sai Unguwar Filin Samji, gidan shahararren Malamin nan mai bada maganin duk wata cuta da ta danganci Iska, wato Malam *Ahamad Filinin Samji*
Malamin ya tausaya ma lamarin Jummai, domin a kafaɗa Ameer ya saɓo ta, saboda bata iya tafiya, Aunty kuma bata iya ɗaukarta, shi ɗin ma ba don ya so ba, sai don lalura, ita kuma ta shafe komai.
Bai wani ɓata lokaci ba ya shiga yi mata karatun Alƙurani mai girma, bayan ya Umarci Ameer da ya riƙe ta, don a zatonsa matarshi ce.
Aunty kuwa tana gefe, ita da ɗaya daga cikin matan Malamin suna kallon ikon Allah.
Wani irin kuka ne mai muryoyi daban-daban Jummai ta shiga yi, ko kusa wannan kuka bai sa malamin ya tsagaita da karatun ba, sai da ya yi nisa sannan ya tsaya tare da jero tambayoyi ga muryoyin dake fita a jikin Jummai “Su waye ku, kuma miye sanadin shigarku jikinta?”
Rige-rigen bada amsa muryoyin suka shiga yi, aikuwa ya daka musu tsawa ya ce “Ɗaya daga cikinku ya yi Magana.”
Nan fa ɗaya ya shiga zayyana yadda aka yi suka shiga jikinta, cewar su Alhaji Lawwali suka basu ita su shanye mata jini don taƙi shiga cikin ƙungiyarsu.”
“Waye haka?” Malamin ya sake tambayar su.
Aljanin ya ce “Shi wani matsafi ne da ya haɗa kai da wata mai gidan abinci, aikinsu shine ɗaukar mata aiki da kuma sanya su cikin ƙungiyarsu ta tsafi, yadda aikin nasu yake shi ne, duk wanda suka kusanta ko ya kusance su, toh zai rasa jininsa, sun kashe maza da mata masu yawa”, sosai Aljanin ya yi ma malamin bayanin irin muguwar ta’asar su Alhaji Lawwali.
Sannan sai da ya bayyana irin mummunar alaƙar da ke tsakanin Alhaji Lawwali da kuma Jumman, wadda daga baya ta guje shi tare da cigaba da zaman kanta, hakan ne ya basu sa’ar cin galaba a kanta cikin sauƙi.
Wannan bayani ne ya tabbatar ma Malam da Jummai ba matar Ameer ba ce, sai dai ko ƙanwarsa.
Aunty kuwa da Ameer kunya ce da baƙinciki suka turnuƙe su, ji suka riƙa yi kamar su nutse ƙasa, ashe duk yadda suke zaton lalacewar Jummai ta fi haka.
Shi kuwa Malamin bai gushe ba sai da ya ji dukkanin sirrinsu Alhaji Lawwali, da kuma wuraren da suke aikinsu na tsafi, domin a kwai matakin da yake son ɗauka.
Yana gama ji ya cigaba da kwararo karatu, bai dena ba sai da aljannun suka kwance ɗaurin da aka yi ma Jummai, sannan kuma ya cigaba, sai da ya ƙone su ƙurmus sannan ya tsagaita.
Bacci mai nauyi ne ya ɗauke Jummai, pillow matar Malamin ta ɗauko aka sanya mata, don tasha wahala.
Shiru ce ta ratsa ɗakin, kowa da abin da yake saƙawa. Kusan Malam da Ameer tunani ɗaya suke yi, wanda bai wuce yadda zasu hukunta su Alhaji Lawwali ba.
Gyaran murya Malamin ya yi, aikuwa gaba ɗaya suka maido hankulansu gare shi.
Ce wa ya yi “Alhamdulillah, mun samu nasarar raba ta da shaiɗanun dake jikinta, sai dai idan ana son kada su dawo, toh sai ta bi dokokin Allah sau da ƙafa, sai ta dena mummunar rayuwar da ta tsoma kanta, sannan ta tsaida sallah, ta kuma riƙi karatun Alƙurani da azkar, sannan ta dena shigar tsiraici, batun kallace-kallace ko ratun batsa duk ta dena, jin kiɗa shi ma ta dena, idan akwai hotuna a inda take rayuwa toh a cire su”.
Bayani sosai ya yi musu akan yadda zata gyara rayuwarta, daga ƙarshe ya ce “Idan da hali ma toh ta yi aure, domin shi ne rigakafin da zai hana ta komawa rayuwar ba”
Su Aunty sun gamsu da bayanansa sosai, godiya suka yi mashi, da kuma alƙawalin kiyaye duk abin da zai maida ta a wannan hali.
Suna cikin maganar ne Jummai ta falka, wani irin aminci ne ta ji a jikinta, wanda rabon da ta ji irinsa shekara uku kenan.
Sunanta malamin ya kira lokacin da ta tashi zaune, bayan ta amsa ya ce “Ya jikin?”, cikin sanyin murya ta ce “Da sauƙi”.
Sake tambayar ta ya yi “Yanzu akwai inda ke maki ciwo”, kai ta girgiza “A’a’, sosai ya yi mata tambayoyi akan ko tana jin wani abu, kamar ciwon kai da sauran su.
Tabbatar mashi ta yi da yanzu garau take jin kanta. Godiya su duka suka yi ma Allah, domin da ikonsa matsalar ta zo ƙarshe.
Nasihohi ya yi mata akan ta ji tsoron Allah, ta kuma gyara rayuwarta.
Tashi suka yi shi da Ameer suka fita, domin tattauna yadda zasu yi da su Alhaji Lawwali.
Aunty kuma da matar Malam suka zauna wurin Jummai, faɗa sosai suka shiga yi mata, ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba, kuka Jumman ta riƙa yi kamar ranta zai fita, nadama ce ta rufe ta akan baƙar rayuwar da ta tsoma kanta.
Jin motsin su Ameer ya sa su tsagaita yi mata faɗan, suna shigowa Malamin ya shiga wani ɗaki ya ɗebo magunguna na Islamic, tare da yi musu bayanin yadda za’a sarrafa su.
Godiya suka yi, sannan Ameer ya yi ma malamin transfer kuɗin maganin a account ɗinsa a take.
Shirin tafiya suka yi, matar Malam ta ce “Ku tsaya ku ci abinci mana”, Aunty tana dariya ta ce “A’a, a bamu ruwa dai”, ruwa da lemo aka kawo musu suka sha, sannan suka yi bankwana da zimmar bayan sati biyu zasu dawo, kamar yadda malamin ya ce.
Tunda suka shiga mota Jummai ta ƙumshe kanta cikin Hijabi ta cigaba da kuka, Aunty na jinta, amma ko kallon ta bata yi ba, bare kuma ta bata haƙuri.
Ameer ma ko a jikinsa wannan kuka, tunda dai na faɗan da aka yi mata ne, kuma ko zata ƙarar da hawayenta ba za’a dena yi mata faɗa ba, har sai rayuwarta ta yi kyau.
Ko da suka koma gida kowa ya shige ɗakinsa. Tunda Jummai ta shige itama ta dasa kukan baƙinciki da nadama, Ammu ne ya shigo ya ce “Aunty na kiranki”, share hawayen ta yi, sannan ta bi bayanshi suka nufi ɗakin Auntyn.
Zaune take akan gado, Ameer kuma yana zaune a kan kujera.
Ƙasa ta zauna tare da maida kanta cikin Hijabi, saboda wata irin kunyarsu take ji.
“Ki fito daga Hijabin nan, magunguna za’a gwada maki yadda zaki yi amfani da su”.
A hankali ta fiddo kanta, magungunan da zata yi wanka da su ne aka nuna mata, na sha da hayaƙi kuma aka ce sai ta ci abinci.
Ana cikn gwada mata ne wayar Ameer ta fara ruri, ta shi ya yi ya fita da nufin amsa wayar, cigaba da gwada mata Aunty ta yi.
Bayan ta gama ne suka yi shiru, daga bisani Aunty ta ɗan fara yi mata nasiha, don a ɗazu sun zazzage mata ta cikinsu ita da matar Malam, yanzu kuma sai lallashi.
Aunty ta ce “Fateema don Allah ki gyara rayuwarki, ko da wasa kada ki kuskura ki maida kanki cikin muguwar rayuwa, kin ga dai na farko da na biyu duk sakamakon bai da kyau, kin yi ciki ba riba, bai kamata kuma ki sake kai kanki a wurin namiji ba, toh yarinta ta ɗebe ki kin kai kanki wirin matsafa.”
Kukan dake maƙale ne a zuciyar Jummai ya ƙwace mata “Aunty wallahi idan na aikata kuskuren farko da son raina, wallahi na biyun ba da son raina bane, rashin gata ne da kuma tsangwama suka maida ni a hali na biyu.”
Kuka mai tsuma zuciya ta cigaba da yi, tare da ba Aunty labarin rayuwarta, tun daga lokacin da mahaifiyarta ta gane tana da ciki, da kuma irin baƙar tsangwamar data nuna mata, har zuwa lokacin da ta haƙurinta ya ƙare.
Sannan ta bata labarin wahalar da sa ta koma rayuwa da su Alhaji Lawwali. Duk tana kuka take ba Aunty wannan labari, sosai Aunty ta tausaya mata, ce wa ta yi “Toh wannan ƙaddararki kenan, kuma tunda ƙarshenta ya zo, sai ki yi ƙoƙari ki gyara rayuwarki ta gaba.
“Insha Allah Aunty ba zan sake ba, na yi nadamar kuskuren dana aikata” cike da nadama ta faɗi haka.
Duk wannan maganganun akan kunnen Ameer, ya zo shigowa ya ji kukan Jummai tana magana, sai ya koma baya don ya san kwarjini yake mata.
“Allah ya sa kin bari da gasken” ya faɗa a ransa.
Tun daga wannan rana Jummai ta fara gyara rayuwarta, tashin farko sallah ta fara gyarawa, da lokaci ya yi zata shiga ɗakinta ta gabatar, tana gama farilla zata ɗora da nafila. Karatun Alƙurani kuwa shine ya zama abokin hirarta, banda wanda gidan ake sanyawa.
Azkar da salatin Annabi kuwa sun fara kama halshenta. Kan kace me rayuyarta ta inganta, nutsuwa ta shige ta, banda wani haske da Allah ya saka mata a fuska, sakamakon komawa da ta yi gareshi.
Mu’amalarta tsakaninta da mutanen gida ma gwanin birgewa, duk wani aikin gida da ita ake yi, hira kuwa da su Altine kamar dama ta sansu.
Rashin lafiyar da take yi kuwa har ta fara mantawa da ita, sai dai mafalki da take ɗanyi, shima Aunty na rubuta mata addu’a shikenan ta yi bankwana da shi.
*Addu’ar ita ce :- Allahumma inni a’uzu bika min su’il ahlami, wa astajiruka min tala’ubi sshaiɗani, fil yaƙzati wal manami*
*Ma’ana:- Ya Allah, Lallai ni ina neman tsarinka daga mugun mafalki, kuma ina neman kariyarka daga wasan shaiɗanu, a cikin bacci ko a falke*
A lokacin da ta bata addu’ar ta ce “Muddin kika lazimce ta, idan zaki kwanta bacci, toh kin yi bankwana da miyagun mafalkai”, kuma haka aka yi.
A ɓangaren Ameer kuwa sabon ginin son Jummai ne ya tashi a zuciyarsa, wani irin farinciki yake ji idan ya shigo ya ganta, don ma duk walwalarta raguwa take idan ta ganshi, saboda kunyarsa take ji.
Aunty ya samu har ɗaki ya roƙe ta da ta gabatar da shi a wurin Jummai, don ya gaji da kwana da tunaninta ba tare da sanin makomar tunanin ba.
Aunty ta ce “Wallahi maganar da nake son yi maka kenan, bana so yarinyar can ta kuɓuce mana, don duk wanda ya same ta a yanzu, toh ya yi sa’a a rayuwarsa,” Ameer ya ji daɗin yadda Aunty ta goyi bayansa.
Jummai na kitchen tana gyara cefane Aunty ta shigo ta ce mata “Idan kin gama ki same ni a ɗaki ina son zamu yi wata Magana,” tana gama faɗin haka ta juya ta fita.
Faɗuwa gaban Jummai ya yi, cikin ranta ta riƙa tunanin maganar da zasu yi. Da hanzari ta gama gyaran cefanen, hannunta ta wanke sannan ta nufi ɗakin Aunty.
Zaune ta same ta kan kujera tana fasa ma Ammu da Ahamad ledar sweet, cikin ranta tana jin daɗin irin kulawar da suke nuna ma Ahamad, duk da sun san ba a hanyar kirki aka same shi ba. Cikin ladabi ta zauna ƙasa tare da jingina bayanta da gado ta ce “Aunty na gama”.
waje Aunty ta tura su Ammu, sannan ta juyo gareta.
“Dama wata magana ce nake son zamu yi dake, wadda babu tilasti a cikinta, idan kin amince muna godiya, idan kuma baki amince ba, babu damuwa ko ɗaya a tare da mu.”
Zama Jummai ta gyara, cikin ranta tana ganin ai babu wata buƙata da su Aunty zasu nema a wurinta, kuma ta kasa yi musu ita, ɗan rausaya kanta ta yi alamar “Toh”.
Aunty ta ce “Ameer ne dama yake son ya fara neman aurenki”, da sauri ta kalli Ainty, lokaci ɗaya kuma ƙirjinta na wata bugawa, don bata taɓa zaton jin haka ba.
Cigaba da magana Aunty ta yi, duk da ta ga yanayin da ta shiga “Ki je ki yi nazari kafin ki yanke hukunci, amma kada ki ƙwari kanki.”
Ƴar a jiyar zuciya Jummai ta sauke, tare da ɗan lumshe ido. Lallai wannan magana bata buƙatar nazari, domin su Aunty sun mata halaccin da ko daga waje suka yi mata miji zata amince, bare kuma daga cikinsu, kuma Ameeer ma, wanda ya tausaya mata tun a karon farko, wanda taga yana kuka a lokacin da ya ganta cikin ƙunci a gidansu, Ameer ya mata halaccin da babu wani najimin da ya yi mata shi.
Duk mazan da ta sani ɓata mata rayuwa suka yi, shi kuwa abin da suka ɓata mata ne zai gyara don haka ko bata son Ameer zata amince ta aure shi, bare kuma ya cika qualities ɗin da za’a so namiji saboda su.
Ɗan nisawa ta yi tare da duban Aunty dake danna waya “Aunty na amince da buƙatarku,” da ɗan hanzari Aunty ta dube ta “A’a Fateema, ki je ki yi nazari tukunna, kada ki yi gaugawar yanke hukunci.”
“Aunty ai wannan baya buƙatar nazari, idan ma har yana buƙata, toh kun riga kun yi mani, sai da kuka ga cancantar abin sannan har kuka tunkare ni da maganar, don haka na amince.”
Wani irin daɗi ne ya kama Aunty, take ta ji son Jummai ya ƙaru a ranta, Lallai Jummai ta cika ɗiya har da rabi da ɗoriya.
Zancen na komawa kan kunnen Ameer ya kama rawar murna, Aunty ta ce “Lallai ka kamu da yawa Ameer.”
Bakinsa har kunne ya ce “Ai Aunty na daɗe ina dakon son Fateema a raina, kin ga dole in yi murna tunda lokacin sauke sa ya zo.”
“Hakane” Aunty ta faɗa, suka kama dariya.
Jummai kuwa daren ranar kasa bacci ta yi, zullumi ta shiga yi akan yadda zata yi soyayya da aure tare da Ameer, ita dai kunyar sa take ji, sannan a matsayin yaya ta ɗauke shi, haka ta kwana da wannan zullumi.
Tun daga wannan rana kunya ta fara shiga tsakaninta har da su Aunty, duk wannan walwalar ta rage ta, ba don komai ba sai don kada Ameer ya ritsa ta.
A ranar da aka ware kuwa zasu haɗu da Ameer kasa sukuni ta yi, daga ƙarshe ma ta ce ma Aunty “A bari kawai ba sai mun haɗu ba.”
Aunty ta fahimce ta, ƴar dariya ta yi sannan ta ce “Haɗuwa dole ne Fateema, ta haka ne zaku fahimci juna.”
Da yamma ta shirya cikin riga da zani na wani lace nata kalar Indigo, lace ɗin ya mata mugun kyau, pink ɗin gyalenta ta yafe sannan ta zura plat shoe ɗinta suma pink.
Ɗan turare mai sanyi marar ƙarfi ta fesa sannan ta fito. Aunty da Altine sun yaba da kyan da ta yi, Altine na washe baki ta ce “Ashe haka kike da kyau Fati”, dariya kawai ta yi ta zauna.
Shi kuwa yana can ya ƙure wanka a cikin Ash ɗin Getzner wadda aka zuba ma aikin hannu, hularsa wadda aka sirka saƙarta da ash ɗin zare da fari da kuma baƙi ya sanya, sannan ya zura takalma baƙaƙe ya fito.
Waya ya yi ma Aunty cewa yana Garden, don haka Jumman ta fito.
Aunty na faɗa mata ta ji kamar ta nutse, a hankali ta tashi ta nufi Garden, wanda tun kafin ta isa take shaƙar ƙamshin turarensa mai sanyaya zuciya. Da idanunsa ya kafe ta har ta zauna, cikin ransa yana yaba kyau irin nata.
Kanta na ƙasa ta gaishe shi, cikin sanyin murya ya amsa gaisuwar.
Shiru ce ta ratsa wurin, shi dai wata irin nutsuwa yake ji, ita kuma faɗuwa kawai gabanta ke yi.
Katse musu shirun ya yi, tare da gabatar da kansa a wurinta, da kuma irin son da yake mata, ya ce “Fateema tun ganina da ke na farko a lokacin da kuka zo asibiti na ji na fara sonki, rashin sanin inda kike ba ƙaramar matsala ya jefa ni ba, bayan kuwa na sake ganinki da kuma sanin inda kike, sai na yi burin idan kin haihu zan nemi aurenki, domin fidda ki daga ƙangin da kike ciki, sai dai kuma Allah bai nufa ba, saboda auren da aka yi maki, wanda mutuwa ce kaɗai ban yi ba saboda kishi da kuma takaicin wanda ya cutar da ke ne aka aura maki.”
Kasaƙe ta yi tana sauraron kalamansa, waɗanda suka tabbatar mata da maza ba halinsu ɗaya ba, akwai na gari irinsu Ameer, waɗanda suke tausaya ma mace, wato a lokacin da kowa yake gudunta, a lokacin ne shi yake kusanta kansa gare ta, duk don ya fidda ta a damuwa.
Katse mata tunani ya yi da “Komai da ya faru muƙaddari ne daga Allah, fatanmu Allah ya yi mana mai kyau a rayuwar duniya da ta lahira.”
“Amiin” ta ce a hankali.
Shiru suka sake yi, sosai ya ga tsagwaron kunyarsa da take ji, domin har yanzu kanta na ƙasa, tunani ya shiga yi wannan kunyar fa zata cutar da shi, don ba zata bari ta bashi kulawa ba.
Kafeta ya yi da idanu sannan ya ce “Fateema,” “amsawa ta yi kanta na ƙasan.
Ya ce “Ki ɗago kanki mu yi Magana.”
A hankali ta ɗago, suna haɗa ido ta ga yana mata wani irin mayen kallo, da sauri ta maida kan ƙasa.
Dariya ya yi yana mamakin wannan kunya, wai ta yi yawon barki kenan, toh ina ga idonta bai buɗe ba.
“Ki taimake ni ki cire wannan kunyar don Allah, don zata cutar da ni” cikin magiya da ƴar shagwaɓa ya faɗi maganar.
Ƴar dariya ya bata, wadda har sai da ta fito, ya kuwa ji daɗin dariyar.
Hira ya cigaba da janta, wata ta bashi amsa, wata kuma ta yi shiru, a haka har suka tashi daga wurin.
Ƙudiri Ameer ya yi sai ya raba Jummai da wannan kunyar, haka kuwa aka yi, salo-salo na kulawa ya riƙa bata, wanda har kunyar ta ragu, itama ta riƙa bashi kulawa.
Sosai suka fahimci juna kuma suka haɗe kansu, hakan kuwa ya yi ma Aunty da maigidanta daɗi, don ya dawo daga UK ɗin da ya tafi.
Fidda lokaci aka yi cewar za’a maida Jummai gida, wanda itama ta ƙagara ta ganta wurin mahaifiyarta da danginta, sai dai bata taɓa maganar ba, don ba ta son su Aunty su yi tunanin ko ta gaji da su.
Kafin ranar ta zo ne Salma da Aisha suka dawo daga makaranta, saboda strike ɗin da ASSU suka yi, sun yi farinciki da ganin Jummai, don basu yi zaton haka ta haɗu ba, saboda suna jin labarinta.
Tamkar ƴan uwa suka koma, Aunty sama Aunty ƙasa saboda sun ji Ameer ne zai aure ta, Ahamad kuwa sun ɗauke shi kamar ƙanensu da suka fito ciki ɗaya.
A ɓangaren Alhaji Mainasara kuwa, tsaye yake a kan Habeeb yana mashi a addu’a domin har yanzu bai farfaɗo daga aikin da aka yi mashi ba.
Kamar raɗa Habeeb ya riƙa jin muryar Abbanshi a kusa da shi, ko kusa bai gazgata abin da yake ji ba, domin ya saba gani da jin kowa ma a ɗakin, sai ya yunƙura zai tafi gare su sai ya ji ya kasa, ƙarshe ma ya ga ba kowa.
Cigaba da jin muryar ne ya sa shi motsa hannunsa wanda ya yi daidai da sadda Abbanshi ya kalli hannun.
“Habeeb” Abban nashi ya faɗa tare da riƙe hannun don gazgata abin da ya gani, lokaci ɗaya zuciyarsa cike da farinciki.
Jin an riƙe hannun ya sa Habeeb ɗin buɗe idanunsa a hankali, tabbas Abbanshi da ya gani gaskiya ne domin har yanzu hannunsu a cikin na juna suke, ɗayan hannun ya ɗago tare da nuna Abbanshi da ya ɗaga hannu sama yana godiya ga Allah.
Magana Habeeb ɗin ke son yi, amma ya kasa, sai dai farinciki cike da zuciyarsa wanda bai misaltuwa.
Yunƙuwara ya yi zai tashi, Abbanshi ya maida shi “Ka kwanta Habeeb, ina kusa da kai, ni ne Abbanka”. Farinciki fal da zuciyarsa ya faɗi haka.
Kafe juna suka yi da idanu, wasu hawaye ne suka riƙa gangaro ma Habeeb, ashe akwai lokacin da Abbanshi zai zo inda yake, ashe mafalkan ganin mahaifinsa da yake gaskiya ne “Allah kasa mafalkan Fateema su zama gaskiya suma”, cikin zuciyarsa da ke aiki kaɗan-kaɗan ya faɗi haka.
Hannu Abbanshi ya sa tare da share mashi hawayen dake fita a idonunsa, “Ka da sake kuka saboda zuciyarka bata buƙatar damuwa ko kaɗan, ka kwantar da hankalinka duk abin da kake so zaka same shi muddin ina raye.”
A hankali Habeeb ya lumshe idanunsa, don ji yake sun masa nauyi.
Dr. Umar ne ya shigo, murna cikin ransa kamar ya taka dutsen arfa, don farfaɗowar Habeeb ba ƙaramar Nasara ba ce a gare shi. Maganganu ya faɗa ma Habeeb, cewar Kada yasa wata damuwa a ransa domin zuciyarsa bata son wahala a yanzu.
Kulawar da ta dace ya shiga bashi, sati biyu na cika aka sallami Habeeb, domin ya warke garau, sai dai jikinsa ba ƙwari, kowa ya yi farinciki da samun lafiyar Habeeb, musamman Abbanshi da da su Isma’il.
Kan abin sallah Alhaji Mainasara yake zaune a hotel ɗin da ya kama, shi kuma Habeeb ya na kwance akan sofa yana bacci, saboda nan ya dawo.
Wayar Alhaji Mainasara ce ta shiga ruri, baƙuwar number ya gani, yana ɗagawa ya tsinkayi muryar Hajiya Mairo tana kuka “Yanzu Alhaji abin da ka yi mani ka kyauta, wane irin zalunci ne wannan, zaka raba ni da ɗana.”
Habeeb ya kalla da ya tashi zaune ya ce “Ni kam ban raba ki da ɗanki ba, na hana ki zuwa inda yake ne?, na ce dai hanyar jirgi da ta mota daban.”
Kuka ta fashe da shi, ya ce Mairo kenan “Yau ko raba ki da ɗanki na yi ai ban rama ba, kin tuna irin mugun abin da kika yi, wanda kika raba ni da mahaifana, kin manta in tuna maki ne?”
“Don Allah a dena tone-tone Alhaji, don Allah komai ya wuce, ka yafe mani.”
Ajiyar zuciya ya sauke, tare da miƙa ma Habeeb waya, don bai jin akwai abin da zai wuce a tsakaninsu, ɗanta dai ne gashi.
Muryar Habeeb ta ji ba ta Alhajin ba, murna wurinta kamar me, shima Habeeb ya yi murna da jin muryar mahaifyarsa, saboda ya kira layinta amma bai samu ba.
Ƙasa Habeeb ya durƙusar da gwiyawunsa bayan sun gama wayar, cike da nadama da ƙasƙantar da kai ya dubi Abbanshi ya ce”Abba don Allah ka yafe mana ni da mahaifiyata, domin mun cutar da kai da yawa. Haƙiƙa ni na aikata abin da ake zargina, ni na yi ma Fateema ciki, ɗanta ɗana ne Abba, na ƙi karɓar sa ne saboda tsoron fushinka, don Allah ka yafe mani Abba,” idanunsa cike da ƙwallah ya ƙarasa maganar.
Gwauron numfashi Alhaji Mainasara ya sauke, don ya san indai suna raye, toh wannan rana sai ta zo “Na yafe maka Habeeb, yanzu yafiyar Fateema ya rage maka ka nema da iyayenta.”
Goge hawayen da suka zubo mashi yayi sannan ya ce “Na gode Abba, itama zan nemi yafiyarta, sannan don Allah Abba ka maida aurena da ita, ita nake so, ita ce sauran rayuwata, idan na rasa ta na san mutuwa zan yi Abba.”
Haƙiƙa ko bai faɗa ba ya san Jummai ce sanadin ciwonshi, kuma tunda bai fatan rasa ɗansa dole ya shiga lungu da saƙo don nemanta.
Albishir ya yi mashi da zai maida masu auren. Murna Habeeb ya kama yi saboda ita ce farincikinsa.
Sati ɗaya suka ƙara, Suka fara shirin dawowa hada Habeeb ɗin, saboda ya ɗauki hutu sai ya ƙara murmurewa.
A ranar da da jirginsu Habeeb ya taso, a ranar ne kuma su Jummai suka cika mota ƙwai da kwarkwata suka nufi garinsu Jummai, domin maida ta gida, da kuma nema ma Ameer aurenta.
*Allah ga bayinka masu rauni, don tsarkin mulinka ka tsare mu daga wannan muguwar cuta, waɗanda ka ɗora mawa ka yaye musu ya Allah.*
Maman Mu’azzam