Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu.
Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne."
kusan duk ba su ji wanda ta ce ba, saboda murya ƙasa-ƙasa ta yi magana.
Cikin tsananin fushi Asabe ta ce "Wa kika ce?"
Jikinta na kyarma ta ɗago kai ta dube su, don har yanzu fargabar faɗa ta ke.
"Habeeb ne, kuma ya ce sai ya kashe ni idan na faɗa."
"La'ilaha. . .