Skip to content
Part 12 of 20 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Zaman suka yi a kan kujeru nan waje domin su jira a rage layin da suka tarar a wajen. Suna zaunen suka fara hirarsu iri-iri suna ta kallon jama’a kala-kala na ta kai da kawo, kowa da hidimar da ya sa gaba. Cikin hirar da suke har zance ya zo kan batun karatun sakandire da yadda kowannensu ya rubuta jarabawar kammala sakandiren wato (WAEC). A nan ta ne Humaira take tambayar Binta, “Wai ni kam wace makaranta kika gama?”

Binta ta nisa tare da cewa, “GGSS JOGANA, amma ba ma a wannan shekarar na Candy ba. Shekarar da ta gabata ne, to matsala aka samu a lokacin da muka rubuta jarabawar darasin lissafi an samu bulllar satar amsa da yawa a ranar. Dalilin da yasa aka soke duk jarabawar makarantun da ke wannan shiyya.”

“Ayya! Allah sarki, ashe kina gaba da ni kenan. Sannan kuma ga shi makarantar kwana, gaskiya na jinjina miki kin yi kokari sosai. Ai ni ba zan iya matsa wa na bar Mummyna ba har a kai ni makarantar kwana ni kadai babu wanda na sani. Kuma ga shi an ce ana ladaftar da mutane da duka sosai, hatta Perfects ma duka suke, lallai kin yi kokari.”

“Hmm! To ya za ayi dole mutum ya yi hakuri wataran sai labari, yanzu ni ba ga shi ba kamar ban yi ba. Ke wacce kika yi ne?”

“Ai ni a cikin garin ma ina kusa da gida, GGSS MASAKA ce, ko ihu na yi za a jiyo daga gidanmu a kawo mini dauki.”

Dariya suka yi gabadaya, Binta ta dora da cewa, “Ke amma ba ki da dama wallahi, to me zai same ki ma. Kuma ni duk zuzuta wahakar boarding school da ake ban gani ba, wani abin ma mutane ke kara wa. Amma sam ba haka abin yake ba, kawai dai abinda makarantar kwana ta fi jeka ka dawo shine halin da’a da nagartar karatun. Babu shakka daliban Boarding school sun fi na Day discipline da kuma academic performance.”

“E haka ne kuma gaskiya akwai wannan bambancin, tunda kin ga kuna can makaranta a kambame dindindin na tsawon zangon karatu, babu wani abu da za ku yi idan ba karatun ba.”

“Yawwa kin gane ke nan, shi ne da ma don haka dole mutum ya yi karatu koda baya so.”

Suna nan a zaune suna ta hirar kimanin mintuna goma sha biyar sai ga wani mutumi nan ya tunkaro inda suke. Sadik kenan shi ne mai cafe din. Tun kafin ya iso ya hango Humaira, idonsa akanta ko kiftawa baya yi. Kai tsaye ya karasa daf da su ya tsaya bisa kan Humaira tare da cewa, “’Yanmata sannu da hutawa.”

Daga kai Humaira ta yi ta dube shi a yatsine ta kauda kai ba ta ce masa komai ba. Binta ce ta amsa da cewa, “Yawwa sannu dai.”

“Aiki kuka kawo ne?”

Ya tambaya yana me kara kallon Humaira sama da kasa, ita yake son ya ji ta yi magana amma ko kallonsa ma ba ta sake yi ba. Binta din ce dai ta sake amsa masa da cewa, “E wallahi aiki ne muka kawo to kuma ga shi akwai jama’a a gabanmu shi ne muke jira idan sun ragu sai ayi mana.”

“Ayya! Allah sarki, akwai cinkoso ne sakamakon duk dalibai na yin registration lokaci guda, sabbi da kuma masu sabunta wa. Ku din me za ayi muku? Ko kuma registration din ne?”

“Kai malam gaskiya ka dame mu fa da tambaya sai ka ce dan jarida. Kai ma ka ji da kanka mana haba!”

Humaira ce ta yi wannan maganar cikin sigar fitsara da wulakanci, yayin da Binta ta yi saurin karbe zancen da cewa, “Ke haba don Allah meye hakan? Tambaya ce fa ya yi ba wani abu, abin da muka sani shi za mu fada masa.”

Murmushi  Sadik ya yi tare da cewa, “Ba komai, haka mutane suke kowa da irin yadda yake fahimtar abubuwa. Ba laifi ta yi ba, hakan ma daidai ne ana son mace me jan aji. Wannan siffa ce ta wasu matan babu yadda za ayi da su.”

“Ka yi hakuri don Allah, ka ga wallahi mu ma aikin registration din muka kawo, mun yi wa ita me aikin magana shi ne ta ce mu jira ta dan rage aiki sai ta yi mana.”

“Ba komai, yanzu ina scratch card din yake? Ku taso mu shiga ayi muku.”

Mikewa Binta ta yi za ta bi shi, Humaira ta galla mata wata kafurar harara tare da cewa, “Wai ke me kike yi haka ne? Daga an yi magana sai ki ce to, kina kokarin tashi.”

“Ba haka bane, tunda ya ce mu taso mu je ya yi mana kika sani ko ya santa ne zai nema mana alfarma ta yi mana? Ki duba fa mutane sai karuwa ake yi, ya kamata mu je ayi mana kafin rana ta yi gaskiya.”

“To shi kenan ai, ke sai ki je. Ni zan jira ta har ta gama ta kira ni koda zan kai yamma a nan din.”

Ganin yadda Huamira ke nuna taurin kai yasa Binta ta karbi scratch cards din ta wuce ta bi shi cikin kwantainar, budurwar nan da ke yi wa mutane aiki sunanta Khadija, ta yi masa sannu da zuwa. Ya amsa sannan ya wuce ya zauna kan wata computer dake dama da ita, ya umarci Binta da ta zauna kan wata kujera da ke dubansa. Kunna computer ya yi ya fara yi mata registration din.

“Ina kawar ta ki, ba za ta shigo ba?”
Ya fada yana duban Binta, murmushi ta yi sannan ta ce, “Hmm! Ai ka ganta nan wata irin shu’uma ce, miskilancinta ya fi karfinta.”

“Hmm! Haka ne, kin san wasu mutanen ba sa son hayaniya ba su saba da jama’a ba sosai, hakan da take yi ba laifi bane.”

“Haka dai ka ce, amma ita na ta halin ba rashin sabo bane, ka yarda da abin da na fada maka miskilanci ne tsagwaransa. Idan ta gaji da zaman ita kadai za ta shigo ne.”

Khadija ce ta dubi Binta ta ce, “Ba ku ne kuka ce za ku jira ba a rage layi ayi muku, ina kawar ta ki? Ko rakiya ta yo miki?”

Binta ta ce, “Aa wallahi kodaya, ita ma registration din za ta yi. Tare muke tana waje ta ki shigo wa ne, wai sai kin kira ta tukunna.”

Dariya Khadija ta yi tare da cewa, “Tana da gaskiya ai, bin ka’ida ne tunda ta yi mini magana bai kamata ba kuma wani ya zo ya ce shi zai yi mata. Amma ki ce ta shigo tunda ga shi ya zo yanzu za mu sallami kowa, dama mu biyu ne muke aikin.”

Mikewa Binta ta yi ta fito wajen Humaira ta ce mata, “Ke da kike son yi wa wannan mutumi rashin kunya to shi ma a wajen yake aiki, ga shi can ma yana yi mini. Watakila ma wajensa ne, kuma wannan budurwar da muka yi wa magana ina jin kanwarsa ko kuma budurwarsa. Ta ce ki taso ki shigo ayi miki, kuma ina ga shi din ne zai yi miki.”

“Hmm! To sai me kuma, can ya karata shi ya sani. Ke ni fa da ba ki ba shi card dina ba ma sai na canja waje kawai, don ba dole ba ne sai a nan.”

“To na ji, yanzu dai ki tashi mu je ki yi hakuri.”

“Ko na shiga ita ce za ta yi mini, tunda ita ce da bakinta ta ce mu jira ta, ba wai mu jira wani ba. Idan kuma ba za ta yi mini ba, to a bani scratch card dina na je wani wajen ayi mini tunda ba su kadai bane a makarantar.”

“To na ji dai tashi mu shiga.”

Haka dai Binta ta lallabo ta suka shiga cikin kwantainar suna shiga mutumin nan ya dago kai suka hada ido da Humaira, wani murmushi ya saki wanda ya kara harzika zuciyarta. Daure fuska ta yi tare da kauda kanta, suka karasa ciki Binta ta koma kan kujerar da ta tashi yayin da Humaira ta nufi wajen Meenat, ta ce, “Sannu da aiki.”

Ta amsa mata da cewa, “Yawwa sannu dai, dama cewa na yi ki shigo kema tunda Mai gidana ya zo sai ya yi muku gabadaya ga shi ma ya fara yin na kawarki. Ki zauna idan ya gama yi mata sai ya yi miki ko?”

Wani kwarjini da cika ido Meenat ta yi wa Humaira, sai ta ji sam ba za ta iya musanta mata ba. Alatilas ta zauna din tare da cewa, “To shi ke nan ba komai ai duk daya ne.”

Murmushi kawai Binta take yi hade da kallon Humaira, wacce takaici ya turnukewa zuciya amma ta ki bari ya bayyana a fuskarta. Shi ma mutumin murmusawa kawai yake domin dama burinsa kenan ya yi wa Humairar da kansa, tunda ta ki kula shi a waje ya yi mata magana ta yi banza da shi to yanzu ga ta a hannunsa wajibi ne ta amsa tambayoyin da zai yi mata wajen cike online form din.

Sadik na kammala wa Binta ya dubi hunairan yana cizon lebe ya ce, “To bisimillah ko.”

Binta ta mike yayin da Humaira ta maye gurbinta ta zauna tare da sunkuyar da kanta kasa tana danna wayarta. Ce mata ya yi, “Ni za ki kalla ki fada mini cikakkken sunanki.”

Cikin sigar yanga da yauki ta ce, “sunana Huamira Adam.”

“Me kika ce? Ban ji ba sosai ki daga muryarki.”

Ya fada yana murmushi, wato ya ji sosai, yana tsokanar ta ne kawai so yake sai ta saki ranta ta daina fishi.

Zumburo baki ta yi tare da cewa, “Na ce maka Humaira Adam.”

Ta fada cikin sautin da ya dara na farko. Haka ya rika tambayar ta dukkan bayanan da ake bukata wajen cike online form din har aka zo wajen daukar hoton passport. Nan ma sai da aka yi drama kafin a dauki hoto. Binta dai na zaune tana kallon ikon Allah, yanayin yadda yake wa Humairan yasa Binta ta fahimci akwai wani a kasa. Da alama dai yana son kulla wata alaka tsakaninsa da ita. Ita kuwa Meenat aikinta l kawai take ba ta lura da wannan dramar da ake ba.

Bayan ya kammala musu ya fito musu da takardunsu gabadaya ya mikawa Humaira, sai ta bata rai ta ki karba, Binta ta karba da sauri tare da cewa, “Yawwa sannu da kokari, to nawa kenan gabadaya?”

Murmushi ya yi tare da yi musu nuni da hannu cewa su tafi kawai su bar kudin, ya yi musu kyauta ne.

Binta ta ce, “Aa gaskiya ba za ayi haka ba, ka fada mana abin da za mu ba ka. Taimakon da ka yi mana na yi mana aikin da wuri mun gode sosai.”

Kasa-kasa ya yi da muryarsa ya ce, “To shi kenan mu je daga waje sai na karba.”

Ba ya son Khadija ta san me ke faruwa, domin muddin ta san cewa kyauta ya yi musu aikin to babu shakka zai sha ruwan masifa. Allah ne kawai zai karbe shi a hannunta. Saboda haka sai su Binta suka mike, Humaira ta dubi Meenat ta ce, “To zamu tafi an gama mana, nawa ne kudin?”

“Masha Allah, dubu daya ne (₦1000).”

Nan take Humaira ta zaro naira dubu daya ta mika wa Khadija tare da cewa, “Mun gode Allah ya saka da alkairi.”

Tana fada ta ja hannun Binta suka fice da sauri, suna fita Binta ta ce, “Wai don Allah me yasa kike haka ne? Ni fa ban san ki da irin wannan halin ba, koda ma boye mini kika yi? Mutum yana miki magana cikin sakin fuska yana miki wasa amma sai daure rai kike yi.”

“Hmm! Ba wani daure rai, ni shi din ne na ji bai yi min ba, amma ba wulakanci nake masa ba.”

“To mu dan jira shi kadan mana zai biyo bayanmu.”

“Ya biyo mu kuma? To me zai yi mana bayan mun biya su kudinsu. Kawai mu tafi.”

Suna tsaka da wannan ja-in-ja, tuni ya fito ya har ya cim musu, sallama ya yi ta bayansu, Binta ce ta amsa masa. Cike da murmushi ya ce, “Idan babu damuwa ina son ku dan ba ni mintuna biyu kacal na ce wani abu duk da na san kuna da uzuri.”

“Laah! Babu komai wallahi ai tunda muka yi registration din mun gama da me wahalar, sa hannu a hankali ma rika yi, muna sauraren ka.”

Gyaran murya ya yi tare da yalwata murmushin fuskarsa sannan ya ce, “Sunana Sadik Abubakar, kamar yadda kuka gani wancan cafe dina ne. Sannan kuma ni malami ne a tsangayar koyar da aikin jarida ta wannan makaranta. Ina son idan ban makara ba a dan ba ni dama a karbi tayina.”

Shiru suka yi na dan wani lokaci yayin da zukatan Humaira da Binta suka shiga tafasa lokaci guda. Zuciyar Humaira na tafasa ne saboda tsanar da ta yi masa sannan kuma ma ya ce yana son ta! Duk da cewa ta ji matsayinsa yana daya daga cikin malaman makarantar amma hakan bai sa ta risina ba. Ita dai ba ta son sa.

Ita kuwa Binta tun lokacin da ta fara yin ido hudu da shi ta ji ya dan shiga ranta saboda kyawun dirinsa da cikar kamalarsa, to sai dai dama ta lura da take-takensa dole a karshe zai nuna yana son Humaira ganin yadda hankalinsa ya karkata gare ta, tatsuniyar gizo ba ta wuce ta koki. Idan ka ga kare na shinshina takalmi to idan ya samu dama dauka zai yi. Zuciyar Binta ta yi mata kuna ne sakamakon Sadik ya bayyana muradinsa akan Humaira ba ita ba. Hakika tana jin son sa a ranta matuka, dama ita ya zaba.

Haka nan ta daure ta yi ta maza tana murmushin yake, wanda ya fi kuka ciwo ta ce, “Hmm! Ranka ya dade kenan.”

Ya karbe zancen da cewa, “Wane ni, ai wannan suna naku ne, kune sarakunan. Ina fata dai za a duba bukata ta.”

“Kada ka damu insha Allah, babu damuwa Allah ya datar damu.”

Wata zazzafar harara Humaira ta bi Binta ta ida tare da cewa, “Ke ni fa zan tafi kin ji na gaji da tsayuwar nan haka.”

Sadik ne ya cafe zancen da cewa, “Okay, to shi kenan bari na kyale ku haka ko, sai zuwa yaushe kenan? Au ga kudinku ma”

Ya mika musu dubu dayar nan da Humaira ta biya kudi aikin da aka yi musu, Binta ta ce, “Aa ka bar shi kawai ai kudin aiki ne, Khadija muka ba wa ba kai ba.”

“To ai ni na yi aikin ba ita ba, kuma ni don Allah na yi lada nake nema. Ba na son mu yi jayayya da ku, ku karba.”

Karbar kudin Binta ta yi tare da cewa, “To shi kenan mun gode, Allah ya saka da alkairi sai anjima ko zuwa gobe.”

Tana fada suka sara suka yi gaba shi kuma ya juya ya koma ya ci gaba da taimaka wa Khadija, dandanan suka rage cinkoson da ke wajen.

<< Kuda Ba Ka Haram 11Kuda Ba Ka Haram 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×