Skip to content
Part 14 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Binta ta ce: “Kin ganni nan kofar gidanku na zo wajenki yanzu mummy ta ce wai kema kin tafi gidanmu.”

Cikin rawar baki da kame-kame Humaira ta ce: “E e a e hakane, amma da na zo ban same ki ba sai… Sai na tafi gidan su wata kawata.”

“Okay, to ba komai ina ne gidan sai na zo mu hadu a nan din ko?”

Humaira ta sauke wani irin numfashi me cike da firgici sannan ta ce: “Aa ki bari kawai ba sai kin zo ba, gobe Lahadi zamu hadu kawai.”

“Lafiya dai na ji kamar kina yin haki? Idan gidan babu nisa ni yanzu ba abin da zan yi a gida kawai ki fada mini na zo kin ji.”

“Aa fa na ce miki, kawai ki bari sai gobe za mu hadu koma mene ne ki ji abin da nake fada miki.”

“To shi kenan ba komai da yau da goben duk daya ne a wajen Allah.”

Tana fada ta kashe wayar ta nemi Mai Adaidaita Sahu ya dawo da ita gida abinta, Shigowarta gidan ta yi tsammanin Baba Abu za ta fada mata cewa Humaira ta zo ba ta same ta ba, amma sai ta ji shiru. Hakan ya sa ta tambayi Baba Abun ,“Humaira ta zo mun yi sabani ko?”

“Ban gane sabani ba? Ni ma yanzu nake shirin tambayar ki, har kin je gidan nasu?”

Wannan tambaya ta Baba Abu ta sa Binta ta fahimci lallai Humaira ba ta zo nemanta ba, akwai dai inda ta nufa ba ta so a sani ne. Wani zancen Binta ta soko da shi domin wanda ya kauda na zuwan Huamira. A zuciyarta kuma ta nutsatsa tunanin to me zai sa Huamira ta yi mata karya? Har ba ta son su hadu? Kuma ga shi ta cewa Mummynta ga inda za ta je amma ba can ta nufa ba?

To ita kuwa Humaira da ke can kwance a tube haihuwar uwa da uba, Usman ne ya ci gaba da shafa jikinta yana tambayar ta,  “Wacece wannan ta kira ki a waya?”

“Wata kawata ce, wallahi na manta mun yi alkawari da ita zan je gidansu, ta ga ban je ba har rana ta fara yi shi ne ta kira ni.”

“Okay, to babu damuwa.”

Yini suka yi cir! Su na abu daya, har barci suka yi. Sai kusan la’asar sannan suka farka, nan Humaira ta shiga toilet ta yi wanka ta gyara jikinta sosai. Haka nan shi ma gogan naku ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya mayar da kayansa.

A da can Humaira ba ta iya hada ido da Usman indai suka aikata wannan lalatar, kunyarsa take masifar ji, amma yanzu ba wannan batun sarai take kallonsa idonta cikin nasa. Don haka bayan sun gama shiryawa, zama suka yi a gefen gado tana kallonsa shi ma yana mayar mata da kallon tamkar mata da miji a dakinsu na aure.

“Wallahi ba na son rabuwa da ke, da ma mu yi ta zama a nan tare.” Usman ya fada cikin sigar murmushi yana lumshe jajayen idanuwansa.

Cikin yanayin murmushin Humaira ta ce: “Allah ko?”

“Wallahi da gaske nake ba na son mu rabu.”

“Hmm! To ya yi kyau, ai ba rabuwa za mu yi ba, muna tare tunda akwai wani lokacin.”

Ya sake lumshe idanu tare da cewa, “E hakane kuma, to amma yanzu yaushe za mu sake haduwa kenan? Kin ga idan kuka fara lakca ba ki da lokaci kenan, sai dai weekend kuma ba zai yiyu ba ace duk za ki rika fitowa, za a iya ganewa. Zai fi kyau a rika canja ranakun ko ya kika gani?”

“To yanzu dai ba zan iya cewa komai ba tukunna, sai mun fara lakcar za mu ga yadda za ayi.”

“To shi kenan, no problem. Anyway, there must be a solution. Tashi mu tafi ko, yamma ta yi sosai na san akwai aikin abinci ko?”

Kama ta ya yi ta mike ya sumbace ta hade da rungumar ta sannan suka fita, wajen mota suka nufa suka shiga ya yi reverse ya fito daga hotel din. Daidai shataletalen gidan Baban Gwari ya yi parking. Ya ba ta kudade masu dan dama, ta saka likaf ta rufe fuskarta sannan suka yi sallama ta fito shi kuma ya yi gaba. Mai Adaidaita Sahu ta tsayar ta hau tare da cewa, “Zaitawa za ka kai ni.”

“To bisimillah kudinki naira dari da hamsin.”

“Hmm! Muje dari biyu zan ba ka amma ka yi sauri ka ji.”

“An gama, Allah ya kai mu lafiya.” Ya fada tare da jan Adaidaita Sahun.

*****

Hakika Humaira ta ji dadin kasancewa da Usman a yau din nan, babu shakka ba shi ba ma da ya bayyana bukatarsa ta rashin son rabuwa da ita, ita ma kanta ba da son ranta suka rabun ba, kawai dai babu yadda ta iya ne. Amma tunda ya gano musu dabarar haduwa a hotel, babu shakka hakan za su rika yi domin sun fi samun sukuni da sakewa, babu wata fargaba. Tunanin da ya mamaye zuciyar Humaira kenan, wanda ya sabbaba bayyanar farinciki da nishadi a fuskarta. Kallo daya za ka yi mata ka fahimci ranta wasai yake babu wata damuwa a ranki tare da ita.

Babu damuwa ko fargaba a ran Humaira koda ta daukar cikin da ba ta shirya masa ba, domin ta yi amanna da wani maganin hana daukar ciki da Usman din yake ba ta. Tun yana bata shi a boye har ta kai ta kawo ya sanar da ita, don haka da zarar ya daga ruwan cikinta bayan ya gama biyan bukatarsa sai ya ba ta shi, to ciki ba zai shiga ba. Wannan shi ne abin da shi da ita suka dogara da shi suke tsula tsiyarsu.

Babu jimawa Mai Adaidaita Sahu ya kawo Humaira gida misalin karfe biyar ba na labarin yammaci 5:00pm ,ta shiga gidan lokacin Mummy ta fara shirye-shiryen hada abincin dare. Sallama Humaira ta yi, Mummyn ta amsa mata tare da cewa, “Sai yanzu? Ai kina fita babu jimawa kawar ta ki ta zo nan.”

“E wallahi sabani muka yi ne, nima ina zuwa gidan na su aka ce ta taho nan, har na fito zan dawo sai ta yi mini waya ta ce na jira ta ga ta nan. ‘Yan aikace-aikace na taya ta lokacin da muka gama kuma rana ta take sosai shi ne kakarta ta ce na bari sai an yi la’asar na tafi.”

“Madalla, da fatan suna lafiya?”

“Wallahi lafiya kalau, ita kadai ce a wajen kakarta, iyayenta sun rasu gabadaya.”

“Allah sarki! Allah Ya yi musu rahama.”

“Amin ya Allah.”

Nan Humaira ta shiga dakinta ta cire hijabinta bayan ta gama shirga wa Mummy karya, ta fito ta kama aikin girki wanda dama aikinta ne.

Shi ma Usman gidan ya koma da gadararsa ya shiga, koda ace Anty Sakina za ta tare shi da tuhumar ina ya je ko kuma wata maganar da ba za ta gamshe shi ba, to zai yi mata kaca-kaca ne ya ci mutuncinta har sai ta yi dana sani. Ita kuwa sam baya gabanta yanzu, ta daina jin kishinsa a matsayin mijinta. Rokon Allah dai kawai take Tana dube ta da rahamarSa ya kawo mata mafita.

Sallama Usman ya yi ta amsa hade da yi masa sannu da zuwa, a ciki ya amsa mata. Ganin yanayinsa a tijare yake yasa ba ta sake tofa komai ba, to dama kusan haka zaman na su yake ‘yan kwanakin nan tun lokacin da ta fara zargin akwai wata alaka tsakaninsa da Humaira. Bugu da kari kuma akwai batun hargitsa shimfidar gadonta da samu anyi a wata rana can baya.

A wannan dare na yau din Usman bai fita yawon da ya saba ba, kwanciyarsa ya yi ya sha barcinsa. Kin fitar da ya yi ne wani tunani ya darsu a zuciyar Anty Sakina, “Anya kuwa mutumin nan fitar nan da ya yi dadi ba lalatar ya je ya yi ba da ranar Allah?”

Tunanin da ya tsaye mata a raina kenan, domin ko runhu mutum ya riko ba zai iske Usman a gida ba da dare, yana can wajen shake ayarsa. Kullum ta Allah sai ya fita babu fashi tamkar ibada, to amma ga shi yau ya ki fita. Bugu da kari ma kuma a weekend, wato ranar da aka fi shagaltuwa kenan. An ce a dukkannin ranakun hutun karshen mako (Asabar da Lahadi), condom da giya da dakuna a hotel karancin suke yi sosai a unguwar sabon gari, sakamakon yawaitar masu sharholiya. To Allah Ya kyauta Ya kuma shirya amin.

Washegari Lahadi Binta ta yi tsammanin gani ko kuma jin kiran Humaira, dangane da cewar da tayi ta bari sai yau za su hadu, sai dai ta ji shiru. Ga shi kuma ba ta da kudi a waya bare ta kira Humairar ta ji za ta zo din ko kuwa, har rana ta yi sosai kusan Azahar babu duriyar Humaira sannan kuma ba ta kira Binta a waya ba.

Tafi-tafi har karfe biyu, karfe uku kai har dai aka yi la’asar shiru babu gilmawar Humaira bare kiran wayarta, daga nan Binta ta fitar da rai akan ba za ta zo ba.

Ita kuwa Humaira shaf! Ta manta da batun Binta, yini ta yi tana sharar barcinta, tun bayan da ta kammala aikace-aikacen gida ta yi girkin abincin rana, misalin karfe 12:00pm ta kwanta sai la’asar ta tashi ta yi wanka ta yi kwalliya sama-sama. Sai a wannan lokaci ne ta tuna da cewa ta yi wa Binta alkawarin za ta je gidansu.

Waya ta dauka ta lalubi lambarta ta kira, Binta ta daga da cewa, “Salama alaikum.”

Humaira ta amsa ita ma da cewa, “Wa alaikumus salam warahamatullahi, baiwar Allah kin ganni shiru ko? Wallahi barci ne ya sace ni lokacin da na gama aiki ina shirin na kira ki na ji yaya za ki zo din kuwa ko ya ake ciki?”

“Hmm! Na zo kuma? Ai Baba Abu ba ta bar ni ba na fita har sau biyu a jere zuwa gidan su kawa ba makaranta ba, gaskiya ba zai yiyu ba, ni dama na yi zaton da kika ce sai gobe, ke ce za ki zo.”

“To na ji, me yasa kuma ba ki yi min waya ba tun da wuri kin tuna mini sai na zo din ai.”

“Hmm! Ba ni da kudi ne shi yasa.”

“To shi kenan yanzu dai yamma ta yi sai dai gobe Litinin kawai idan kin zo. Ina jin ba mu da lakca sai karfe 11:00am ko?”

“E watakila kusan hakan ne, kodayake timetable din ba complete bane wannan da muke da shi kwata-kwata iya na department ne, akwai na General Studies shi ma.”

“Okay to ki yi wa Mai Adaidaita Sahu waya ya zo ya kai mu da wuri, ma rage signing dinmu kafin lokacin fara lakcar, bari na yi miki transfer din credit yanzu.”

“To shi kenan babu damuwa na gode sai Allah ya kai mu, ki gaida su Mummy.”

“Yawwa za su ji insha Allah!”

BAYAN SATI BIYU

Bayan sati biyu lakca ta fara kankama, su Humaira na yin lakca a dukkanin kwanaki biyar na aiki, wato daga Litinin zuwa Juma’a. Kuma kusan duk lakcocin suna farawa ne da safe misalin karfe tara 9:00am ban da ranar Laraba, ba su da lakcar safe a wannan rana sai karfe 1:00pm suke fara lakca. Haka nan suna gama karatu ne a kullum da misalin karfe 4:00pm na yammaci.

Binta ta fi Huamira saurin fahimtar karatu, ko kusa ba za a hada kwazonsu ba. Ba wai Humaira kadai Binta ta fi kokari ba kusan dukkan daliban ajinsu da suke karanta fannin Business Administration, babu me fahimtar Binta. Ta fi dukkan daliban ba da amsa yayin da malami ya yi tambaya, haka nan ta fi su yin tambayar akan duk abin da ba ta gane ba.

Wannan ya sa cikin kankanen lokaci kowa ya san Binta, daga malamai har su daliban. Bisa al’ada ta dalibai wasu sun yi farinciki da hakan har ma suka nemi kulla kawance da ita, wasu kuwa akasin hakan ne, bakin ciki da hassada ne suka cika musu zukata. Cikin wadanda suka nuna sha’awarsu ta kulla kawance da Binta akwai wata matashiya wacce shekarunta ba za su wuce na Bintar ba, sunanta Asma’u. Ita kadai Binta ta ba wa fuska sakamakon ta fahimci babu wasa a tare da ita, sannan kuma tana son karatun.

A cikin sati biyun nan da suka yi a makarantar, Binta ta yi kokarin jan Humaira su je Café din Sadik, domin su gaisa amma ta ki yarda. Duk lokacin da Binta ta dauko maganar sai Humaira ta ce ita ba za ta je ba, idan Bintar ta ga za ta je ba ta hana ta ba, ga hanya bisimillah.

Watarana suna zaune akan irin kujerun nan da ake gina su da siminti a cikin manyan makarantun gaba da sakandire, na hutawar dalibai. Binta na yi wa Humaira karin haske akan wani darasi da aka yi musu, Sadik ne ya zo wucewa rike da takardu zai shiga aji. Ban su ankara da shi ba, haka nan shi ma bai gane su ba sai da ya zo daf da su sannan ya lura su ne. Cakewa ya yi cak! Akansu ,su duka suka dago kai, wani lallausan murmushin jin kunya Binta ta saki tare da sunkuyar da kanta, yayin da ta dan bata fuska kadan, kanta ta sunkuye ita ma. Shi ma Sadik murmusawar ya yi tare da gyara tsayuwa.

“Sannu ina yini?”

Binta ta fada a yanayin jin kunya ba tare da ta dago kai ba.

“Yawwa sannu dai, ya karatu? An fara lakca kenan?”

“Wallahi kuwa an fara, ga mu dai muna dan yin bita ne.”

“Very good, haka ake so. Amma dai karatun da sauki ko?”

“Hmm! Alhamdulillah, wallahi da sauki kam, muna ganewa sosai.”

“To ya yi kyau, a ba da himma sosai ban da wasa ko shashanci. Karatu irin wannan ya dara wanda kuka yi a sakandire, a nan akwai ka’idoji da tsare-tsare wanda ake bukatar dalibi ya bi su domin cim ma burinsa. Ina yi muku fatan alkairi, Allah ya taimaka.”

<< Kuda Ba Ka Haram 13Kuda Ba Ka Haram 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×