Skip to content
Part 16 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Misalin karfe 5:30pm na yammaci ranar, Anty Sakina ta shirya za ta koma gida, wasu kudade ta dauko cikin jakarta ta ba wa Mummy, sannan shi ma Abbansu ta bayar aka ajiye masa hade da sakon gaisuwa dayake lokacin da ta zo ya riga ya fice kasuwa, kuma lokacin dawowarsa bai yi ba. Humaira na can dakinta ta ki fitowa bare ta raka Antyn ta ta kamar yadda ta saba, har sai da Mummy ta aika aka fada mata cewa, ta zo ta raka Anty Sakina za ta tafi. Alatilas ta fito, ganin yanayinta kamar ba ta so yasa Anty Sakinar ta ce,

“Aa ta yi zaman tunda aiki take, su Hydar ma za su rakani.”

Tana fada ta ciro naira dubu biyu ta mikawa Humairar tare da cewa, “Ga wannan ko photocopy kin yi a makaranta.”

Babu kunya bare tsoron Allah Humaira ta sa hannu ta karbe kudi tana sakin murmushi, komawa dakin ta yi ta sako hijabi ta fito ta raka ta.

To dawowar Anty Sakina gida kenan, sai ta fada wani sabon tunanin. Tunani take akan yadda bacin ran Usman ya fara illata rayuwarta, har ma ana cewa tana ramewa. Don haka yanzu ya zama tilas ta yi duk me yiyuwa wajen yakice tunaninsa daga ranta, babu shakka idan har ba ta yi da gaske ba to ba iya rama abin zai tsaya ba. Wata cutar ma na iya kama ta ba a sani ba, daga karshe kuma iyayenta za ta dorawa wahala. Yadda cututtukan nan na zamani ba jin magani suke ba, hawan jini da ciwon zuciya yanzu sun zama na zamani, babu babba babu yaro kowa damka suke su galafaitar ko ma su hallakar gabadaya. Don haka dole ne ta nemi mafita, to mene ne mafitar gare ta ? Wannan ita ce tambayar da take yi wa kanta.

A wata ranar Litinin ne suna zaune tare da abokiyar aikinta Anty Zara’u a Staff Room, suna hira. Anty Zara’u ta dube ta ta ce, “Wato na lura kin saka damuwar Usman a ranki sosai, ga shi nan duk  yanayinki ya sauya tamkar wacce ba ta da lafiya.”

Wata rarraunar ajiyar zuciya Anty Sakina ta sauke, babu shakka yanayinta abin tausayawa ne. Nisawa ta yi cikin sassanyar murya ta ce, “Wallahi na rasa ya zan yi na ture wannan abin daga zuciyata, nima kaina na san na canja. Satin da wuce na je gaida su Mummy, ita ma tambaya ta yi ya a kai na rame? Sai karya na yi mata na ce bani da lafiya ne. Anty Zara’u bakin cikin Usman ne zai kashe ni na tabbata.”

“Ki daina fadin haka, insha Allah babu abin da zai faru sai alheri. Amma me yasa ba ki fada wa Mummy abin da yake faruwa ba? Kin ga ko jan kunne ne sai a yi masa kila ya daina ko kuma ya rage.”

“Hmm! Anty Zara’u kenan, duk yadda kike tunanin Usman ya wuce nan wallahi. Iya zance ne da shi, indai za a ba shi dama ya yi magana to wallahi sai kin amince da abin da zai fada miki.”

“Hakane akwai mutane irin su sosai, to amma ina ga da kin jaraba sanar da koda Mummy ne ba wai sai iyayensa watakila su san yadda za su bullied wa lamarin. Domin gaskiya zama cikin wannan yanayin ba zai yiyu ba.”

“Hmm! Ni kam dai ba na jin fada wa wani matsalar Usman za ta yi amfani ko ta sa ya sauya. Bari na son na fitar da abin da yake yi na fada, yin hakan kamar tonan asiri ne. Ni da shi tun abin bai tabarbare masa ba kamar haka nake masa nasiha da nuni akan munin wannan rayuwa da ya dorawa kansa, ba hanya bace me bullewa amma yaki ganewa. Yanzu idan na fada wa su Mummy halin da yake, su ma bacin ran ne zai dame su. Allah Shi ne Wanda Yake da iko akan kowa da komai, Shi Ya san sirrin boye, don haka Shi zan ci gaba da kai wa kukana babu shakka zai share mini hawayena.”

“Tabbas zantukanki hakane, kuma insha Allahu Ubangiji zai kawo miki mafita ba da jimawa ba. Hakurinki zai miki rana da yardar Allah. Sannan ya kamata ki samu karin sani abin yin wanda zai yi keeping din ki busy, kin gane ta hakane ba za ki samu damar yin wancan tunanin ba.”

“Hmm! Anya kuwa akwai abin da zai kauda mini wannan bakin cikin baya ga Usman ya gyara halinsa, ya daina duk wadannan miyagun halayen. To sai dai kuma idan rabuwa muka yi.”

“Kai! Kai! Bari wannan zancen don Allah, rabuwa kuma? Haba! Ki daina yi wa kanki wannan fatan Allah ya kiyaye.”

“Allah kuwa Anty Zara’u da Usman zai sawwake mini da na fi farinciki da hakan, aurensa gare ni bai amfanar da ni komai ba sai kunci da zaman rashin tabbas. Cutukan zamani sun yi yawa, ina tsoron ya je wajen neme-nemen matan banza ya dauko cuta ya goga mini.”

“Insha Allah haka ba za ta taba faru ba, Allah ya kiyaye shi ma Allah ya ganar da shi gaskiya. Abin da nake nufi wanda zai dauke tunaninki daga kansa shi ne, me zai hana ki fara saide-saiden kayayyaki sawa, kamar atamfofi leshi takalma da sauran su? Ina ga idan har za ki yi wannan to hankalinki zai karkata ne ga kasuwancinki, ko da ba ki daina tunanin bacin ran ba, to babu shakka zai ragu sosai. Amma ya ya kika gani?”

“Hakane, to amma kin san wannan harka ce babban, dole sai mutum yana da manyan kudade a hannunsa, kuma sai ya san a wajen wa zai rika sarar kayan.”

“Hmm! Wannan abu shi ya fi komai sauki, kin manta da yaya Ahmad ne? Na san mata akalla sama da goma wadanda yaya Ahmad ne yake ba su kaya idan sun sayar su biya shi kudin ya sake ba su wasu kayan. Kin ga *Hajiya Ta Birni* ma da ta shahara din nan, yaya Ahmad ne ya kafa ta. Babu ko dari ta fara harkar amma yanzu kin ga yadda ita ma ta zama babbar dealer, har wasu take ba wa sarin kayan. Indai za ki yi, to wannan ba damuwa bace ni zan yi masa magana.”

Haka nan dai Anty Zara’u ta yi ta kokarin shawo kan Anty Sakina har ta amince, sannan ta ci gaba da yi mata zantukan masu dadi wanda za su sa ta dan manta da bacin ran da Usman ya dasa mata a zuciya. Babu laifi kuma a ranar sai da walwala da annuri suka bayyana sosai a fuskar Anty Sakina.

Tabbas kawaye irin su Anty Zara’u sun yi a rayuwa, haka ake son kowacce kawata ta kasance duk lokacin da ‘yar uwarki ta shiga damuwa, kema ki shiga, ki taimaka mata da duk abin da za ki iya. Ki ba ta shawarwarin da za su sanyaya mata zuciya, su rage mata damuwar. Wannan shi ne zaman aminci da mutuntaka.

Hakika duk wacce aka jarabta da miji me irin halin Usman, to babu shakka za ta kasance cikin mawuyacin hali. Wajibi ne a tausaya mata sannan a rika dannar kirjinta da kalamai masu taushi tare da taya ta addu’a, Allah Subhanahu Wata’ala ya dude ta da idon rahama ya kawo mata agajinSa, ta samu ta iya cin jarabawar.

A nan nima nake taya Anty Zara’u da dukkan wata mace da take da miji makamancin Usman, Allah ya kara mata hakuri da juriya akan wanda take da shi. Allah ka dubi hakurinta ka kawo mata mafita cikin ruwan sanyi. Allah ya saka wa mata da mafificin alkairi, Allah ka tsare mana su amin.

To bayan kwanaki hudu kenan da zuwan Anty Sakina gida, wato yau Labara kenan. Ita ce ranar da Usman ya tsara cewa Humaira za ta kai masa ziyara can gidansa. Kasancewar ranar Anty Sakina tana wajen aiki, ita kuma Humaira ba sa fara lakca sai rana ta yi. To sai dai duk da hakan Binta ta saba musu da shiga makarantar da wuri a dukkannin ranakun. Sukan yi amfani da lokacin wajen bitar darusan baya, ko kuma su je dakin karatu (library) su yi bincike ko kuma dai su samu wani kasaitaccen wajen su zauna Binta ta rika yi wa Humaira karin haske.

Sai dai a yau kam lamarin ya sauya ba zai tafi kamar yadda suka saba ba, sakamakon yarjejeniyar da Humaira ta kulla da Usman. Saboda haka tun sassafe ta sanar da Binta cewa yau ba za ta samu damar shiga makaranta da wuri ba, Mummy ce za ta aike ta wata unguwa daga can za ta wuce makarantar. Idan Binta ta shirya kawai ta tafi za su hadu a can din. Hakan kuwa aka yi, Mai Adaidaita Sahun da yake kai su, yana zuwa Binta ta yi masa bayani, babu bata lokaci ya sure ta sai makaranta.

Ita kuwa Humaira ta gama shiryawa tsaf! Kawai kiran Usman take jira, mintuna ba su wuce uku ba sai ga kiran nasa. Dagawa ta yi tare da karawa a kunnenta ba ta ce komai ba, shi din ne ya ce, “Ina fatan kin gama shiryawa ko?”

Murmushi ta yi tare da cewa, “Yeah! Expect me in the next 15 minutes.”

“Okay, see you dear! Muah Muah.”
Ya fada tare da huro mata kisses.

Humaira na kashe wayar ta sabi jaka ta yi wajen Mummy ta ce, “Zan tafi.”

“Yau kuma ina kawar ta ki, ba za ta shigo bane?”

“A’a wallahi Mai Adaidaita Sahun da ce yau ba zai samu damar kai mu ba, wai gyara zai je. Ita ma ta tafi yanzu ta yi mini waya.”

“To shike kenan, Allah ya kiyaye sai kin dawo.”

“To Mummy, don Allah ki dan kara mini wani abin mana.”

“Humaira ba ki da dama, yanzu banda abin da Abbanki ya ba ki sai na kara miki wasu kudin? Shin wai ma ina kudin da Sakina ta ba ki?”

“Mummy wani littafi fa nake so na saya da su, don Allah ko kadan ne ki ba ni.”

Ɗari biyu Mummy ta ba ta, karbewa ta yi sannan ta fice, tana isa bakin titi ta tsayar da Mai Adaidaita Sahu, gidan Anty Sakina ta yo wa tsinke, kafin ta karaso ta yi wa Usman waya cewa, “Ga ni nan na shigo layin.”

Ya ce, “Okay, no problem. Kawai ki shigo gidan ba matsala.”

Har daidai kofar gidan aka kai ta, tana sauka ta shige ciki da sauri. Sallama ta yi Usman na zaune a waje kan kujera yana shan iska, singlet ce kawai a jikinsa. Ya dago kai ya kalle ta da wani irin shegen murmushi tare da amsa mata sallamar, murmushin ne ita ma ya fara bayyana a fuskart. Karasowa ta yi inda yake, kujeru biyu ne a wajen dama, sai ya yi mata izini da ta zauna kan dayar yayin da shi kuma ya mike ya je ya dauko ruwa da lemo. Zubawa ya yi a kofuna guda biyu, ya mika mata daya shi ma ya dauki daya.

Karɓa ta yi amma ba ta sha ba, ya dude ta ya ce, “Ki sha mana, ke fa dadina da ke kenan. Ko mu shiga daga ciki ne?”

Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, ya ci gaba da cewa, “Okay, to tashi mu je cikin.”

Kama ta ya yi ta mike ya rungume ta tare da yi mata kiss sannan suka shige falon. To wannan kenan.

Ita kuwa Binta na can makaranta abinta, sai dai ba ta ji dadi ba ita kadai sun saba ko ina su biyu suke tafiya. Saboda haka Café din Sadik ta tafi ko za ta same shi, sai dai kash! Ta yi rashin sa’a ba ya nan, Meenat ta iske tana aiki, shiga ta yi suka gaisa. Dayake Meenat din tana gane mutane, hira suka fara yi har take tamabayar Binta, “Ina kawar ta ki ne?”

“Wallahi da yake ba mu da lakca da safe an aike ta a gida ne sai anjima za ta shigo.”

“Okay, Masha Allah, ya yi kyau. Ya karatun dai?”

“Alhamdulillah! Ya aiki ya fama da jama’a?”

“Aiki Alhamdulillah mun gode wa Ubangiji. Wai ni kam ya ya sunanku ne?”

Murmushi Binta ta yi sannan ta ce, “Ni sunana Binta ita kuma Humaira.”

“Kai Masha Allah! Beautiful names, Binta sunan kakata ne, Humaira kuma sunan wata cousin sister dina.”

Hira suka rika yi sosai tamkar dama can sun san juna, dayake dukkan su mutane ne masu sakin fuska da faran-faran da jama’a. Suna nan suna ta hirarsu sai ga Sadik ya fito daga lakca, dama haka ya yake yi, bai saba da zaman ofis ba. Matukar ba shi da lakca to za ka same shi a Café dinsa, shi yasa da wahala ka same shi zaune a ofis. Wannan shi ne tsarinsa, wanda hakan ya kara masa daraja da kima a wajen dalibai mata har ma da mazan.

Domin akasarin malaman jami’a da ke zaman ofis sannan kuma su rika barin dalibai mata na yawan zuwa ofis din, to babu shakka ba za su taba ketare zargi ba, walau zargin yin lalata da ‘yammata don su ba su maki ko kuma wani zargin na daban. To shi dai Sadik ya kubutar da kansa daga wannan mummunan zargi.

Yana shigowa suka hada ido da Binta, murmusawa suka yi su duka biyun, “Sannu da shigowa.”

Binta ta fada yayin da take sunkuyar da kanta, amsa mata ya yi da cewa, “Yawwa an gaishe ku ya gida ya karatu?”

“karatu mun gode Allah.”

“To Masha Allah, ke kadai ce ne, ina abokiyar tafiyar?”

“Ba ta karaso ba tukunna, dayake sai anjima za mu fara karatu.”

“Ya yi kyau, Allah ya taimaka.”

“Amin ya Allah, bari na tafi ko?”

Khadija ce ta yi saurin karba mata da cewa, “Ban gane ki tafi ba, muna hira za ki wani ce za ki tafi, ko lokacin lakcar ne ya yi?”

Cikin murmushi Binta ta ce, “Aa da sauran lokaci, na ga kina aiki ne.”

“Hmm! To aiki zai hana ni magana ne, kuma ai ga mataimaki nan ya zo. Kawai ki yi zaman ki ba za ki tafi ba har sai Humaira ta zo.”

“Hmm! To shi kenan.”

Zama ta yi suka ci gaba da hirarsu, shi ma Sadik ya hau kan computer din da yake aiki ya fara wasu ‘yan aikace-aikacen.

A nata bangaren Humaira kuwa, tunda suka shige falon nan ita da Usman, suka fara zantuka irin wanda ke motsa fitinanniyar sha’awa bayan sun dan sha lemon da ya zuba musu. Daga nan ya tashi ya koma kan kujerar da ta zauna 3 seater, kissing hade da romancing ya fara yi mata kamar yadda suk‘saba kenan, daga karshe kuma har a kai ga an aikata babban laifin.

To idan da sabo dai yanzu Humaira ta saba da Usman, ya mayar da ita kamar matarsa, kai yadda yake yi wa Humaira a yayin jima’i ko Anty Sakina ba ya yi wa. Sakar masa jiki Humaira take sosai ta bude cinyoyinta ya kwashi ganima son ransa tamkar ya biya sadaki. Wasanni iri-iri da tabe-tabe hadi da tsotse-tsotsen dake wakana tsakanin mace da namiji ba wanda ba sa yi.

Sun fita daga hayyacinsu ba su san make faruwa ba a wannan duniya, nishi jin dadi kawai Humaira take yi. Sallama aka fara yi, “Salama alaikum.”

Amma ina shiru ba su ji ba, sha’aninsu kawai suke yi.

”’Shin wacece me yin sallamar nan, asiri zai tonu ke nan?”’

<< Kuda Ba Ka Haram 15Kuda Ba Ka Haram 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×