Skip to content
Part 28 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

To, a bangaren Anty Sakina kuwa, ta gaza magana. Kuka kawai take marar sauti, Mummy ta sake tambayar ta, “Sakina wai lafiyarki kuwa? Me ke faruwa ne ina ta magana kin ki ba ni amsa, sai kuka kike yi kamar wata karamar yarinya.”

Cikin yanayin kukan ta ce, “Mummy Humaira, me na yi…” Sai kukan ya ci karfinta, maganar ta gagara fitowa.

“Humaira kuma, me ya samu Humairar? Hatsari ta yi ne?” Mummy ta fada cikin sigar zakuwa da jin halin da Humairar take ciki.

Anty Sakina ta karfafa muryarta ta ce, “Ita da Usman na gani a gida yanzu na koma duba wani abu.”

“Ban fahimci abin da kike fada ba, dazun nan fa Humairar ta ce ta tafi makaranta.”

“Mummy zan yi wa Humaira sharri ne, yadda na gan ta da Usman Allah Ya nuna mini Annabi haka.” Tana fada ta zaro wayar Humairar, ta kunna mata daya daga cikin recording din wayar da suke yi mafi munin ji, sannan ta ci gaba da cewa, “Wannan wayar wace kuma muryoyin su wa kika ji? Mummy wai yaushe Humaira ta fara irin wannan rayuwa? Kuma me na yi mata da za ta ci amanata? Ta rasa wanda za ta kula sai mijina, muna ciki daya da ita?”

Amsoshin tambayoyin da Anty Sakina ba ta samu ba ke nan, domin kuwa bayan Mummyn ta gama sauraren abin da Usman da Humaira suka tattauna a recording din nan, sai wani duhu-duhu da ba ta san daga ina ya faro ba ya rufe mata idanu. Zaune take amma sai ta yi talau za ta fadi ta baya, Anty Sakina ta taro ta cikin firgici tare da fadin, *“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!* Mummy Mummy!”

Ina, Mummy shiru, idanunta sun rufe. Ta suma ne, sai kukan ya zame wa Anty Sakina guda biyu. Ga kukan bakin cikin Humaira sannan ga na suman Mummy, a kidime ta rika jijjiga ta kafin ta tuno cewa Mummyn na da hawan jini. Sai yanzu ta yi nadamar sanar da ita, “Na shiga uku! Me yasa na fada mata wannan maganar!” Ta furta tare da gyara mata kwanciya a nan tsakar gidan sannan ta shiga ta dauko tabarma ta mayar da ita kai. Ta shiga yin ‘yan dabarun da kan iya dawo wa da Mummy numfashinta, amma dai shiru kake ji. Zuwa can sai ta tuno da wani likita makwabcin su Mummyn wanda ya kasance kamar aboki ne a wajen Anty Sakinar, domin tare suka tashi a unguwar.

kiran sa ta yi ya zo, to da ma shi ne yake duba Mummyn idan irin hakan ta faru, zuwansa keda wuya ya yi mata ‘yan allurai kuma ya ba da tabbacin za ta farka ba da jimawa ba. Ba a fi awa daya da rabi ba, cikin ikon Allah sai Mummy ta farka, Anty Sakina na zaune a wajen ko motsawa ba ta yi ba, ta zuba tagumi, su Haidar ma sun dawo daga makaranta.

“AlhamduLillah! Sannu Mummy.” Anty Sakina ta furta, su Haidar ma sannun suka yi mata.

“Yanzu ina Humairar take?”
Mummy ta tambaya cikin rarraunar murya.

“Mummy a bar maganar nan tukunna, ni wallahi mantawa na yi ma tun farko na fada miki.”

“To idan ba ki fada mini ba kina da wacce za ki fadawa ke nan?”

“To ai Mummy da irin wannan halin da kike shiga gara na bar komai a raina, ita kuma Allah Ya shirye ta Ya ganar da ita gaskiya.”

Mummy ta sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da cewa, “Amma babu shakka Humaira ta yi mini bazata! Kuma yanzu shi Usman din shi ne har ya iya sauraren Humaira ya yi lalata da ita? lallai ya tabbata K’UDA BA KA HARAM! To ya je Allah Ya saka mana, babu inda za mu kai shi sai wajen Allah. Yanzu ina Humairar take? Me yasa ba ki sako ta a gaba kun taho tare ba?”

“Wallahi gabadaya raina ya gama baci ne ban san lokacin da na kore ta ba, yanzu a firgice take amma za ta dawo.”

Nan dai suka ci gaba da zaman bacin rai, babu shakka zuciyar Mummy a turnuke take, tsananin kunar zuci take ji. A hannu guda kuma ga tunani da sake-sake sun cika zuciyar makil, ba don taimakon Allah ba da kuma alluran da aka yi mata, to hakika da hawan jinin ya tsananta har ya kai ta ga hallaka.

Wata zuciyar ta ce mata, “Kawai ki tsine wa yarinyar, tunda dai albasa ba ta yi halin ruwa ba. Sannan kuma koda ta dawo ki kore ta, kada ki bar ta, gara ta shiga duniyar kowa ma ya huta.”

Wata kuwa zuciyar sai ta ce mata, “Ya za ki yi da ita? ‘Yarki ce fa! Hannunka ba ya rubewa ka yanke ka jefar! ‘Ya’yan zamani ne ka haife su amma ba ka haifi halinsu ba, mafita daya shi ne ki bar ta da Abbanta ya yi mata dukan tsiya ya karya mata kafar da take fita har ta kai kan nata ga shi lalataccen wofi.”

“Ai ko dai wannan duk ba mafita ba ce, domin idan ya yi mata dukan da ya raunata ta, wa kuka tsugunnar idan ba kanku ba? Kai karshe ma idan ya hau dokin zuciya sai ya yi mata dukan da zai hallaka ta. To wa gari ya waya? Sannan kuma hukuma ba za ta bari ba!” Wata zuciyar ke nan da nata tunanin, yayin da wata kuma ta karbe linzamin tunanin da cewa, “Yo ai da zai kashe ta din ma shi kenan an huta, domin irin wadannan yaran marasa jin magana, masu bata wa iyaye rai, da janyo abin kunya ba su da wani amfani. Da zamansu gara mutuwarsu.

Zuciyar da ta gama tunani kafin wannan ta karba, ta yunkuro da zafinta a fusace ta ce, “Sam! Wannan gurbataccen tunani ne kuma gurguntacce, marar tushe bare makama. Irin wannan tunani babu inda yake dire mutum sai a tashar nadama, son rai ne da son zuciya kawai. Kuma irin abin da ya kai yarinyar ga fadawa cikin yanayin da take a yau ke nan, don haka abu mafi dacewa a nan shi ne, ki nutsu, ki fahimci ‘yarki, ki nema mata shiriya a wajen Ubangiji. Kada ki kuskura ki yi mata baki, domin a yanzu da ba ki yi mata bakin ba ga abin da ta aikata, to ina ga kuma kin aibata ta? Shi bakin mahaifiya ya fi reza kaifi a jikin yaro, ki yi hakuri ki danni kirjinki da addu’o’i. Allah maji rokon bawanSa ne. Sannan kuma batun duka shi ma sam ba mafita ba ne, mafita daya dai ita ce ku yi mata fada cikin nasihohi da jan hankali. Ku nuna mata tsananin bacin ranku, to In Sha Allah fadan zai shiga jikinta ya ratsa kwakwalwarta sai Ubangiji Ya taimake ta ta bari. Allah Ya shirya, Allah Ya kiyaye gaba Ya kuma rufa asiri.” Wannan shi ne tunani mafi kyau da dacewa, kuma shi ne wanda Mummy ta nutsu da shi, a take ta ji zuciyarta ta fara rage radadi. To wannan ke nan.

Lokacin da karfe daya na rana ta yi, aka tashi daga makarantar da Anty Sakina take aiki, ganin har wannan lokaci ba ta koma ba, ya sa Anty Zara’u ta kira ta, tana dagawa ta ce, “Lallai dawa ta yi nama, ki ce har yanzu ba a gama sayen kayan ba?”

Anty Sakina ta dan yi wani murmushin karfin hali me sauti ta ce, “Hmm! Ki bari zan kira ki anjima, ina busy ne yanzu.” Ta fada tare da kashe wayar.

Tunani me zurfi ta afka, “Yanzu wace irin rayuwa za mu yi a cikin gidan nan ni da wannan yarinyar? *ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WAKHLIFLI KHAIRAN MINHA.* Ya Allah!” Cikin ranta ta fada, kafin ta saki wani nannauyan numfashi wanda ya tsayar mata da tunanin cak! Gabadaya kwakwalwarta ta daina iya sarrafa komai, dum kawai take ji sannan kuma kirjinta ya yi mata wani irin nauyi, numfashin na fita da kyar. Addu’ar ta ci gaba da maimaitawa har nauyin kirjin ya fara raguwa numfashin ya daidaita. Sai kuma ta sake dorawa da tunanin yadda za a kasa su a faifai ana tallata su layi-layi, lungu-lungu, gida-gida bisa wannan abin kunyar da Humaira ta dauko musu. Duk yadda suka so akan kada zancen ya fita waje, da wahala hakan ta iya kasancewa, domin magana a wannan zamani ko mutum daya ya yi shi da zuciyarsa, to idan ta bayyana ba za a yi mamaki ba. “Ko me zan fada wa Anty Zara’u? Ta ya ya zan yi mata bayani?” Ta fada a ranta, yayin da kanta ya sara mata har sau uku, ta dafe kan tana cizon lebe.

Mummy ta ce, “Ki rage tunani da damuwa fa, kada ki illata kanki. Addu’a ita ce mafita, ki ci gaba da yin ta. Duk lokacin da kika ji bacin rai zai dame ki sai ki yawaita fadin, *INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!* Allah zai sanyaya miki ranki.

***

To idan muka koma Jakara kuwa, bayan La’asar kadan Binta ta shirya tsaf ta dubi Humaira ta ce, “To ina ga yanzu ya kamata a ce kin koma gida, na san dai ko ma me ke ciki akwai, ita Antyn ta kai maganar gida. Don haka ki je din ki san me ke wakana, zai fi alkairi sama da cigaba da zama a nan.”

“Na shiga uku! Wallahi Allah gabana faduwa yake, ba zan  iya komawa ba.”

“Na ce miki ki daina ambaton shiga ukun nan, hankalinki kike kara tayarwa. Ki nemi taimakon Allah a madadin haka, duk lokacin da kika ji faduwar gaban sai ki ambaci Allah. Ki tashi mu tafi.”

Haka nan alatilas ta mike da kyar, kafafuwanta sun yi masifar nauyi, cira su take yi kamar mai tsohon cikin da ta kusa haihuwa. Suna fitowa bakin titi, Binta ta tsayar da Mai Adaidaita Sahu ta ce masa, Zaitawa zai kai mu, suka shiga ya ja suka wuce.

Zugum Humaira ta yi a cikin Adaidaitar ana tafiya, sam hankalinta ba ya tare da ita. Ta tsunduma cikin wani zuzzurfan tunani dangane da abin da za ta riska a gidan da irin hukuncin da za ta fuskanta, hakan take hakaitowa a ranta. Har suka shigo layin nasu ba ta san an shigo ba, ji ta yi Binta ta taba ta tare da cewa, “To kin ji dai duk abubuwan da na fada miki ko? Kada ki kuskura ki saba koda guda daya ne, Allah Ya tsare Allah Ya rufa asiri, sai yadda ta yi yu.”

Ai tun kafin Binta ta kai karshen maganarta, gaban Humaira ya ba da ras! Yanzu ne ma ta fara faduwar gaba, da can ba komai ta ji ba. Bugun zuciyarta ya kara sauri ainin, kifa kanta ta yi a kan cinyar Binta yayin da gumi ya fara karyo mata, jikinta har ya fara yin dumi alamun zazzabi na son ya rufe ta. Ganin wannan yayin na firgici a tare da ita ya sa Binta ta sauya kudurinta na kin shiga cikin gidan su Humairar, haka nan ta yanke shawarar raka kawar tata har gaban Mummy, ko ma me  zai faru ya faru din.

Da ma dai abu daya da zai hana ta shiga shi ne, kada iyayen Humairar su zarge ta akan lalacewar ‘yarsu. Domin mafi akasarin lalacewar mutum silar kawa ce ko kuma aboki. To amma ba yadda ta iya, ba za ta iya barin kawar tata cikin wannan yanayi na damuwa ba marar tabbas, don haka sai ta ce, “Ya isa haka, tashi za mu shiga tare da ke har cikin gidan, amma ya kamata ki saita kanki kada mutane su fahimci wani abin.”

Wannan magana ta Binta ta dan ba wa Humaira kwarin gwiwa kadan, saboda ta san ko banza ba za a fara yi mata fada a gabanta ba, sannan kuma Bintar za ta ba wa Mummy hakuri, idan kuwa har haka ta faru to zafin da Mummy ta dauka zai ragu. Don haka sai ta kwarara jikinta ta yunkura ta sakko daga Adaidaitar suka shiga cikin gidan.

Binta ta kwada sallama, “Assalama Alaikum.”

Daga cikin falo Anty Sakina ta amsa sannan ta fito don ganin waye, ido suka hada da Humaira, wata harara mai tsananin razanarwa ta aika mata, yayin da ita kuma Humairar ta tsaya cak hade da sunkuyar da kai kasa. Binta ta ce, “Sannu ina yini.”

Harara kawai Anty Sakina ta bi ta da ita ba ta ce komai ba, Binta ta dora da cewa, “To Humaira, na kawo ki har gidanku, idan kin ji abin da na fada miki kuma kin yi aiki da shi, na tabbata su Mummy za su yafe miki.

Ta fada tare da juyawa za ta fice, Humaira ta rike ta gam. Anty Sakina ta dubi Binta a wulakance ta ce, “Ke din kuma wace ce ke da har kike ba ta tabbacin za a yafe mata? Ai da gani duk kwaryar sama ce da ta kasa, lalatattun banza kawai.”

Binta ta ji zafin maganar nan matuka amma sai ta dake zuciyarta, har da sakin murmushi amma fa na takaici ta ce, “Anty ki yi hakuri, duk abin da ya faru ya riga ya faru. Kaddara ta riga fata, na sani yanzu kalamaina ba za su iya gamsar da ke komai ba. Abu daya zan maimaita miki shi ne, ki yi hakuri. Ni kawar Humaira ce, a makaranta muka hadu, kodaya ba ni da hannu cikin wannan al’amari, ke hasalima ba don ita ta fada mini da bakinta ba, to wallahi Allah musu zan yi cewa sharri ne ake yi mata. Humaira ba ta kula kowa a makaranta, mu biyu muke tarayyarmu kowa ya sani. A yadda ta yi mini bayanin abin ya faru, ba ta da laifi, azal ce da iftila’i suka fada mata. Kuma koda Humaira na da laifi, to shi fa Usman din ya fita, bai kalli matsayinta ba a wajensa? Tamkar kanwarsa ta ciki daya take, ai ana barin halak ko don kunya. Koda ma a ce halinsa ne haka, to babu shakka da ya duba halacci da ya kauda kansa akanta koda kuwa ita kai kanta wajensa, bare ma na sani wallahil azim babu yardarta cikin wannan lamari. Saboda haka ina kara rokon ki a karo na biyu, don girman Allah ki yi hakuri ki yafe wa kanwarki, wannan magana a kashe ta a cikin gida, kada bacin rai ya sa a yi abin da suna zai baci.”

Mummy da ke cikin falo ta jiyo dirin sautin maganar Binta amma ba ta dauki murya ba sannan ba ta fahimci zancen ba, don haka sai ta ce, “Ya ya aka yi ne waye?”

“Au ashe Mummy na nan ma.” Binta ta fada, nan suka rankaya cikin falon, Humaira ta rakabe daga bakin kofa tana zubar da wasu marayun hawaye masu tsananin dumi. Kallo daya za ka yi mata ka fahimci tana cikin tsananin tsoro da firgici. Babu shakka suffofin nadama sun bayyana karara a tare da ita.

“Ina yini Mummy ya gida?”
Binta ta fada cikin yanayin damuwa, ta sunkuyar da kanta kasa cike da zakuwar jin yadda Mummyn za ta amsa mata. A tunaninta dai za ta sha magana fiye da wacce Anty Sakina ta fada a muni, to amma abin mamaki sai ta ji sabanin hakan. Cikin karamci da mutuntaka Mummy ta ce, Lafiya kalau Binta.”

Jin hakan ya ba ta kwarin gwiwa, ta gyara tsugunnon da ta yi ta ce, “Mummy na san kin fi kowa sanin halin Humaira duk fadin duniyar nan, kuma na san ba ki taba ganin wasu alamomi da za su sa ki yi zargin Humaira da aikata irin wannan laifi ba. Ina son ki duba wannan dalili ki karbi uzirinta, wallahil azim ko a makaranta ba ta da saurayi, ba ta kula samari. Wannan abu kaddara ce. Kuma kamar yadda ta yi mini bayani, shi Usman din ya yi amfani da dabaru ne kafin ya iya cin nasara akanta. Ina rokon ki Mummy don girman Allah ki yafe wa Humaira.”

Binta ta dan yi shiru domin ta huta, yayin da Mummy ta shiga nazartar zantukanta. Maganar ta taba mata zuciya sosai, kalamai ne masu matukar nauyi wanda ba kasafai ake jin su daga bakin mai karancin shekaru irin Binta ba. Nasiha ce mai kyau kuma ta daure ta da jijiyoyin jikinta, “Babu shakka abin da ta fada game da Humaira gaskiya ne.”

Wannan ne tunanin da Mummy ta yi, yayin da Binta ta ci gaba da cewa, “Ke Humaira ga Mummy nan ki ba ta hakuri, ki nemi yafiyarta. Sannan ita ma Anty ki roke ta ta yafe miki.”

Kuka kawai Humaira take idanunta sun kumbura sun yi jajir kanta ya fara mata ciwo, zazzabi ne mai zafi ya rufe mata. Binta ta mike tare da cewa, “To ni na tafi Allah Ya rufa asiri, Allah Ya kara kiyayewa.”

Humaira na durkushe tana barin hawaye mintuna kamar biyar, zazzabin nan ya gama rufe ta ruf! Su ukun sun yi zugum kowa da irin nau’in radadin da yake ji a ransa. Zuwa can Anty Sakina ta nisa tare da cewa, ‘Ni ban ga rashin yardarki a wannan lamari ba  munafuka ce ke, kin boye mana hakikanin halayenki ne. Idan duk jikina kunnuwa ne ba zan taba yarda babu amincewarki ba don kina matsayin ‘yar uwata. Saboda akwai wata rana da kika taba zuwa gidana ba na nan, kika yi jira na, bayan na dawo na iske ki kina barci cikin wani yanayi, tun a wannan lokacin na yi zargin faruwar irin haka. Ba irin tambaya da dabarar da ban yi miki ba akan ki fada mini gaskiya ba amma kika ki.”

Ta dan tsahirta da yin magana, yayin da Mummy ke girgiza kai hade da jinjina lamarin, takaici da bakin ciki sun hana ta cewa komai. Anty Sakina ta mayar da dubanta ga Mummyn ta ci gaba da cewa, “Mummy Usman ba shi da hali mai kyau, zai iya aikata abin da ya fi wannan ma, idan da kanwarsa ya aikata haka ma ba zan yi mamaki ba. Ina hakuri ne da shi, ban taba kawo muku korafinsa ba, amma neman matan banza yake. Ba ya kwana a gida sosai, sai ya rika yi mini karyar aikin kwana aka mayar da shi. Sannan ba ya jin nauyin yin waya da matan a gabana, duk wadannan na bar su ne a raina domin ba na son yadda ni raina yake baci kuma naku ya rika baci. Addu’a nake kawai Allah Ya kawo mini mafita, Ya yaye mini wannan bakar kaddarar, kuma addu’ata ta karbu. Zama tsakanina da Usman ya kare har abada.”

Wani dunkulallen abu ne ya taso wa Humaira ya zo daidai kahon zuciyarta ya tokare, ga ciwon kai da zazzabin nan suna tsananta. Yunkurawa ta yi ta mike da nufin ta isa gaban Mummy ta ba ta hakuri, taku daya, biyu, ta daga kafa kafin ta aje taku na uku ta yanke jiki ta fadi bayan ta daina ganin komai, numfashinta ya dauke cak!

<< Kuda Ba Ka Haram 27Kuda Ba Ka Haram 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.