Skip to content
Part 30 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Shɑfi nɑ 30

Nan take Anty Sakina ta ce, a dauki nata jinin a gwada idan zai yi sai diba a kara wa Humairar. Aka dauki samfurin jinin aka gwada, sam ba zai yi ba, kuma ko irin a yi musayar nan da wani ma ba zai yi yu ba. Ita kuwa Mummy ba ma a jaraba daukar nata ba saboda larurarta. Anty Sakina ta rikice sosai ta shiga damuwa, nan ta kira Abba a waya ta sanar da shi.

Kai tsaye ya yo wa asibitin tsinke, yanzun ma dai tare da Najib suka sake zuwa. Da zuwansu likita ya dauki jinin Abba aka gwada, shi ma hakan take, wato ba zai yi wa Humaira ba. Najib da ke wajen ya dubi likitan ya ce, “To ko za a jaraba nawa a gani ko zai yi?”

“Me zai hana?” Likita ya fada.

Nan aka dauki jinin Najib din, cikin sa’a kuwa, shi jinin nasa irin lamba daya din nan ne. Wato dai zai iya ba wa kowanne mutum jininsa. lita guda aka kwasa a jikinsa, aka nufi dakin tantancewa aka yi duk gwaje-wajen da za a yi. Babu wata matsala a tare da shi.

Misalin karfe biyu na rana, mahaifiyar Najib ta yo abinci mai rai da lafiya ta kawo wa su Mummy. A lokacin an fara kara wa Humaira jinin, kuma su Najib ba su kai ga barin asibitin ba sakamakon likitan ya ce kada ya yi garajen yin tafiya ko kuma wani aikin, kasancewar an taba jininsa akwai bukatar ya huta sosai.

“Ikon Allah! Ashe dai abin babban ne haka? Har da karin jini? Mahaifiyar Najib ta fada, lokacin da Mummy ta kai ta da nufin ta sake ganin jikin Humairar.

“Wallahi kuwa kin ga dai lamarin Ubangiji!”

“To da ma wai ba ta da lafiya ne ko kuwa?”

“Wallahi lafiyarta kalau fa, jiya-jiyan nan da rana ta yanke jiki ta fadi a sume, to daga wannan faduwa ne kuma sai abubuwa ke faruwa, daga wannan sai wannan.”

“To Ubangiji Allah Ya sawwake, Allah Ya sa zakkar jiki ce.”

“Amin, kuma an sa ki dawainiya, Allah Ya saka da alkairi.”

“Ah haba dai! Wallahi babu komai, ai an riga  an zama daya, wannan duk yi wa kai ne.”

Sai bayan La’asar suka tafi gabadaya, wato da Abba da Najib da kuma ita mahaifiyar Najib din, suka koma kasuwa ita kuwa ta yo gida. Wannan ke nan.

Yinin yau gabadaya Anty Zara’u ba ta shiga makaranta ba, kasancewar ba ta jin dadin jikinta, ta tashi jikinta duk ciwo yake tamkar wacce aka yi wa dukan tsiya. Tun safe take kwance kuma wayarta a kashe take. Ta kashe wayar ne domin kada a dame ta, sai yanzu da yammaci ta dan ji kwarin jikinta; ta mike ta yi sallah sannan ta bude wayar da nufin ta kira Anty Sakina, ta ji ya ya makarantar ta yini? Domin har kawo yanzu ba ta san me ke faruwa ba a bangaren Anty Sakinar.

Tana kiran layin bugu daya ya shiga, Anty Sakina ta daga tare da cewa, “Assalama alaikum.”

“Wa alaikumus salam warahamatuLlah.” Anty Zara’u ta amsa.

Anty Sakina ta dora da cewa, “Don Allah ki yi hakuri, tun jiya da na ce zan kira ki ban kira ba. Wallahi bayan na baro ki din nan a makaranta, wata matsala aka samu a gida. Humaira ce ba ta da lafiya, shi yasa ban dawo ba a jiyan kuma yau ma a asibiti muka yini.”

Cikin sigar firgici da tashin hankali Anty Zara’u ta ce, “SubhanAllah! Me yake damunta? A wane asibitin kuke?”

“Wallahi larura ce dai ga ta nan, muna nan asibitin Murtala.”

“Allah Sarki! Allah Ya ba ta lafiya. Wallahi ni ma kin ga yau haka na tashi jikina sam ba na jin dadinsa, ban ma je aiki ba. Shi ne na ce bari na kira ki.”

“Assha! Allah Ya sawwake, ai haka ake ta fama wallahi.”

“Yanzu zan shirya In Sha Allah zan zo asibitin.”

“A’a da kin bar shi ma, tunda ke ma ba lafiyar gare ki ba.”

“Haba! Me kike fada haka? A kwantar da Humaira a asibiti na gaza zuwa na duba ta? Ni ai nawa ciwon mai sauki ne, ciwon jiki ne ba wani abu ba. Ga ni nan yanzun nan.”

“To shi kenan sai kin karaso.”

Anty Sakina ta fada tare da kashe wayar. Nan da nan Anty Zara’u ta mike ta wartsake jikinta sannan ta shirya ta nufo asibitin, a hanya ta tsaya ta hada kayan dubiya masu yawa sannan ta iso. Wayar Anty Sakina ta kira ta ce mata, “Na karaso, ina bakin kofar asibitin. Kuna wane bangaren ne?”

Anty Sakina ta ce, “To, bari na na zo na yi miki iso.” ‘Yan dakiku kalilan ta iso wajen da Anty Zara’u take tsaye. Gaisawa suka sake yi sannan suka isa tare. Anty Zara’u ta gai da Mummy cikin girmamawa tare da tambayar ya mai jiki? Kasancewar ba a wajen Humairar suke zaune ba, tana can dakin majinyata a kwance.

Duk da cewa Mummy da Anty Sakina suna matukar kokarin boye damuwar da ke ransu, amma akan dan fuskance ta kadan a tattare da su, musamman Anty Sakina wacce har rama ta dan fara yi. Sun dan jima suna hirar jajantawa juna, kafin daga bisani su shiga wajen marar lafiyar. Anty Zara’u ta yi wa Humaira sannu da jiki tare da nuna tausayawa. Bayan sun fito ne Sakina da Anty Zara’u suka dan kebe waje guda, suka fara tattauna batutuwan da suka shafe su na wajen aiki. Cikin tattaunawar ne Anty Zara’u ta ce, “Shin wai da ma Humaira ba ta da lafiya ne amma ba ki fada mini ba har sai da aka kwantar da ita a asibiti?”

Anty Sakina ta yi shiru, takaici ya sake mamaye mata zuciya, wanda har alamun hakan suka bayyana a a fuskarta.

“Ya ya dai na ga kamar ranki ya baci? Na ga yanayinki ya sauya kamar ke ma din ba ki da lafiya?”

Ajiyar zuciya Anty Sakina ta yi hade da fesar da wani numfashi mai dumi, yanayin bacin ran ya karu ainun, ta nisa tare da cewa, “Wai me ya sa wani namijin gara danbunsuru da shi ne? USMAN K’UDA NE BA YA GUDUN HARAM! Allah ya isa tsakanina da shi ba zan taba yafe masa ba!” Ta karasa jumlar da sakin wasu marayun hawaye.

“SubhanAllah! Ban fahimci zancenki ba, ki daina kuka.”

“Usman dan haram ne! Humaira ya rika nema da lalata har asirinsa ya tonu, ni da kaina na kama shi hannu dumudumu, da idona na gan shi ba fada mini aka yi ba.”

Wata walkiya mai jijjiga kai hade da jiri suka kama Anty Zara’u, kanta ya fara juyawa tamkar sitiyarin mota. Saboda tsakanin kaduwa wayar hannunta ta fadi kasa amma ba ta sani ba, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN.”

Addu’ar da bakinta ya rika maimaitawa ke nan fiye da tsawon mintuna uku, Anty Sakina ta dora da cewa, “Ciki har ya yi watanni uku a jikinta, sanadiyar firgicin da ta shiga sakamakon tunanin hukuncin da za a yi mata ya janyo ta suma har cikin ya zube.”

Wani nannauyan numfashi Anty Zara’u ta sauke sannan ta ce, “To barka, Allah Ya ba ta lafiya. Kuma ina fatan dai babu wanda ya san maganar ko?”

“E to, akwai makwabciyata Zainab wacce da taimakonta ne ma asirin nasa ya tonu, amma ba mai surutu ba ce. Sai dai bayan faruwar abin, Humairar ta ji tsoro ta gudu gidan su kawarta, ita ce ma ta kawo ta gida, amma ita ma yarinyar watakila ta gari ce.”

“To Allah Ya rufa asiri, a kashe maganar nan a binne ta. Shi kuma ya je don kansa, zai gani a kwaryar cinsa In Sha Allah! Ki yi hakuri ki dauki dangana, Allah zai miki sakamako kyakkyawa mafi alkairi.”

“Na gode sosai da kulawarki, ya su Hajiya da Yaya Ahmad?”

“Suna nan lafiya kalau wallahi, Hajiya ma ta ce a yi wa Humaira sannu.”

Har Magariba suna tare suna hira abinsu, hakan ya dan rage wa Anty Sakina damuwa kadan. Ana kiran sallar Magariba, Anty Zara’u ta mike da nufin ta komo gida. Har kofar asibitin Anty Sakina ta rako ta.

To mahaifiyar Najib kuwa, tana komawa gida ta dasa tukunya ta fara shirya abincin dare domin kawo wa su Mummy. Zuwa Bayan Magariba kafin Isha ta gama komai, ta dauko ta fito titi ta tari Mai Adaidaita Sahu zuwa asibitin. Babu bata lokaci ya kawo ta. Ita ma Anty Zara’u komawarta gidan ke da wuya ta sa aka makare wasu manyan kulolin zuba abinci, bayan ta yi sallar Magaribar ta sake juyowa zuwa asibitin. Tsakaninta da mahaifiyar Najib ba tsayi, bai wuce mintuna biyar ba zuwa bakwai ba. Haka nan zamanta ke da wuya sai ga Abba da Najib sun biyo domin sake duba jikin Humairar kafin su wuce gida. Nan dai aka yi gaishe-gaishe aka taba hira.

Haka dai Maman Najib da Anty Zara’u suka rika dawainiyar kai abinci asibitin ba dare ba rana. Kwanansu biyar aka sallame su, lokacin jikin Humaira ta fara jin kwari.

***

Dan uwa rabin jiki, in ji masu iya magana. Babu shakka wannan maganar haka take, domin mun ga tabbaci a tare da Anty Sakina. Tsawon zaman da suka yi a asibiti, kafatanin duk kudaden da aka kashe, a lalitarta suka fita ta zuge bakin jakarta sai fita kudi suke ba tare da ta ji ko dar! A ranta ba, bare ta ji haushin Humairar. Kai hasalima yanzu tana matukar son kanwar tata, tana tausaya mata.

Washegarin sallamar su daga asibiti ne, Binta ta shirya domin ta zo gidan su Humairar. Saboda hankalinta ba a kwance yake ba, ba ta san irin hukuncin da za a yi wa kawar tata ba, ko an hana ta fita ne? Ko kuma an hana ta kula kawaye ne? ire-iren wadannan tambayoyin ne makare a zuciyarta. Yayin da a hannu guda kuma ta matsu matuka da yin tozali da ita, don haka dai ta yanke shawarar za ta zo din, domin hakan ne kawai zai fayyace mata shin tarayyarta da Humairar ta zo karshe ne ko kuwa za ta ci gaba? Ita dai sam ba ta kyamar Humaira akan wannan al’amari, domin jarabta ce ta rayuwa wacce babu wanda ya ketare ta. To amma idan har iyayen Humaira suka yi mata togaciya da ‘yar tasu, to babu shakka za ta hakura su raba gari.

Misalin karfe 11:00 na safe ta isa gidan da sallamarta, Anty Sakina ta amsa mata daga falo, daidai lokacin tana ba wa Humaira magunguna tana sha. Mummy kuma tana daki tana dan taba barcin hantsi. Binta ta isa kofar falon, dayake Anty Sakina ta gane muryarta sai ta ce, “Bisimillah shigo mana.”

Binta ta daga labule ta shiga ta zauna kan kujera tare da gai da Anty Sakina. Cikin sakin fuska ta amsa mata.

“Ya ya mai jiki? Ashe ba ta da lafiya?”

“Wallahi kuwa, jiki da sauki.”

Anty Sakina ta fada tare da ficewa daga falon domin ta dan ba su waje su tattauna. Binta ta matso kusa da Humaira ta ce, “Me ya faru da ke haka?”

Cikin rarraunar murya Humaira ta ce, “Ke! Na tsallake rijiya da baya, na tafka kuskure amma na yi nadama sosai. Bayan kin tafi ranar nan, ban sake me ke faruwa ba sai tsintar kaina na yi a asibiti.”

“To! Ikon Allah, Ubangiji Allah Ya kara kiyayewa. Abin da zan fada miki gaskiya shi ne, ki rage son zuciya. Domin duk wanda ya ce zai biye wa son ransa, to wallahi zai kai kansa wajen da babu mai iya zuwa bare ya taimaka masa. Shi namiji da kike gani ba kowanne ba ne yake da kunya. To amma ki sani duk rashin kunyarsa sai kin tsaya kin saurare shi har zai kawo miki irin wadannan kazaman bukatun. Da zarar kin fahimci mutum shashasah ne, to ki kaurace masa kawai, sai ki zauna lafiya.”

“In Sha Allah zan kiyaye, na gode sosai wallahi da kulawarki. Allah Ya bar zumunci. Ya ya Baba? Da fatan tana nan lafiya?”

“Lafiya kalau wallahi! Ban ga Mummy ba ko ba ta nan ne?”

“Tana daki barci take; kila kafin ki tafi ta tashi.”

“Haka ne.”

Shiru suka yi kamar mintuna biyu, zuwa can Binta ta katse shirun da cewa, “Makaranta saura kwanaki shida a koma.”

Humaira ta dan ciji lebe tare da cewa, “Ai ina jin ni da makaranta har abada ke nan! Zai yi wahala ba a saka mini mari ba, fita waje ma gagara ta za ta yi.”

“E haka ne, gaskiya abin ne babu dadi, wai mahaukaci ya ci kashi. Babu shakka yanzu dole ne su Mummy su kara saka ido matuka a kanki, amma watakila wannan ba zai hana a bar ki ki karasa karatun ba, domin rashin ilimin ma yakan jefa mutum cikin tasgaro.”

“Ai gaskiya ni dai na fitar da rai ma, na hakura. Koda ma an ce na koma zan ce musu na hakura kawai, tunda kin ga ni ba ma fahimtar karatun nake ba.”

“Ki daina fadar haka, kina da fahimta mana, matsalarki daya dai ba ki mayar da hankali ba ne. Kin saka wasa a ranki ne, amma matukar za ki sa wa ranki cewa ga abin da kika je nema, kuma ki rika bibiyar darusan baya to za ki fahimci komai da sauki wannan shi ne dalili kawai.”

“Haka ne, to amma gaskiya ni dai ba zan yi maganar makaranta ba, idan an ce na koma zan koma, bare ma ni ina ganin abin da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.”

Murmushi Binta ta yi mai dan sauti sannan ta ce, “To ya ya batun Najib din naki?”

Murmushin ita ma Humairar ta yi kafin ta ba ta amsa da cewa, “Ke dai bari, ai Najib dan halak ne na ajin karshe! Har jininsa aka diba aka kara mini fa, sannan kuma Mamansa ta rika jigilar kawo mana abinci safe da rana da kuma dare. Gaskiya yanzu ina cikin nadamar rashin ba shi kulawa a baya, kunyarsa ma nake ji sosai yanzu. Sai dai ba na jin ya san me ya faru da ni, haka ma mahaifiyarsa. Su dai abin da suka sani shi ne ba ni da lafiya, amma ba su da labarin abin da ya haddasa rashin lafiyar.”

“In Sha Allahu ko sun sani ma ba za su nuna rashin fahimta ba, musamman shi Najib din idan har yana son ki to zai iya kauda kai. Matsalar dai watakila mahaifiyarsa din ta nuna ba ta amince ba, amma Abbansa ma zai amince tunda su maza ba su da tsugudidi kamar mata “

“Ai Abbansa ya rasu, shi ne yake karkashin kulawar Abbana a kasuwa tun yana karami har ya girma.”

“Allah Sarki! Allah Ya jikan sa. Duk da haka babu wata matsala, da yardar Allah ita ma mahaifiyar tasa za ta fahimci abin kuma ba za ta kawo tutsu ba. Ki ci gaba da addu’a kina tuba ga Allah, In Sha Allah Ubangiji zai shiga lamarin.”

“To shi kenan Allah Ya tabbatar mana da alkairi, na gode matuka wallahi, na ji dadin zuwan nan naki, ban san ma ta ya ya zan yi miki godiyar ba!”

Binta ta yi murmushi ta ce, “Allah Sarki! Kada ki damu, ai mun zama ‘yan uwa. Ni da ke babu godiya a tsakaninmu, Allah dai Ya tashi kafadunki kawata ta kaina!” Dariya suka yi gabadaya.

Duk zantukan da suka tattauna a cikin kunnuwan Anty Sakina, tana zaune a tsakar gidan tana saurarensu, domin ita har yanzu ba ta gama yarda da Binta ba. Gani take kamar ta dalilinta ne Humaira ta zama haka, to sai dai wannan hira da ta ji yanzu, ta kore mata duk wani shakku ko zargi dangane da Bintar. Ashe kawar kirki ce, abokiyar tafiya ce ta kwarai. Kuma hakan ya kara tabbatar mata da azal ce dai ta fada wa kanwar tata.

Binta ta jima sosai suna ta hirarsu har kusan Magariba sannan ta koma gida.

<< Kuda Ba Ka Haram 29

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.