Kira ya shigo wayarsa mirginawa ya yi tare da miƙa hannunsa gefen da wayar ta ke ya janyo wayar sunan Nabila ya gani ya yi tsaki tare da ajiye wayar ya sauko daga kan gado banɗaki ya shiga ya yi wanka ya fito yana sharci kansa da ƙaramin tawol aka sake kira ya matsa wajan gadon yana dubawa Nabilar ce dai tsaki ya sake yi a karo na biyu yana faɗin,
“Idan har ba ɗagawa na yi ba yarinyar nan ba barina za ta yi na huta ba.” Gab da kiran zai tsinke ya ɗaga kiran tare da danna amon Muryar wayar ya ajiye akan madubi ya buɗe man shafawar shi yana shafawa cikin raunin murya ta ce,
“Me ya sa ko yaushe ka ke son wahalar da zuciyar da bata san komai ba bayan soyayyar ka, Uhm! Yaya Hafiz laifi ne dan ina son ka da har na zama abar wufantarwa a wajan ka?”
Lumshi idanunsa ya yi ya ja numfashi tare da furzarwa a hankali cikin sassanyar muryarsa ya ce; “Nabila ya kamata ki fahimcini ba wai ina wufantar da buƙatar ki bane domin hakan ya zama wulaƙanci ba a’a kin sani ni mutum ne da bana son ɓata lokaci a kan abinda ba zai zama tabbatacin abu a rayuwata ba.”
Ya ɗan sihirta kafin ya ci-gaba da faɗin “Dan me zan yaudare ki da abinda babu shi a zuciyata, ke ɗin ƙanwata ce saboda ƙanwar abokina ce dan haka ki yi haƙuri ki tsaya a wannan matsayin ba wancan matsayin da babu shi a raina ba, yaudara ba halina bane ba kuma zan fara akan ki ba, dan haka ki yi haƙuri ina maki fatan alkhairi.”
“Ya… “ Tsinki kiran ya yi yana faɗin “Kanana da ku tun kan ku tafasa kuke son ku ƙona, banda fitsara irin ta wa su matan yanzu mace ce take buɗar baki ta fara taran namiji da kalmar so mtsw! Allah ya kyauta”!.
*****
Nabla ta ji ɗib janye wayar ta yi daga kunninta tana kallon wayar hawaye masu zafi suka zubo a kan fuskarta zama ta yi gefen gado ta fashe da kuka ‘wace irin ƙaddara ce wannan? Zuciyarta sam bata ma ta adalci ba da har ta rasa wanda za ta so sai wanda sam bai san darajar so ba wanda bai san darajar zuciyar masoyi ba, mutumin da kansa kawai ya sani bai damu da damuwar wani ba’ ƙanenta Fa’iz ya shigoɗakin da gudu yana faɗin “Aunty Nila Yaya na neman ki.” Ya yi turus ganinta zaune tana kuka, juyawa ya yi da sauri ya samu Safwan zaune a kan kujera yana ƙoƙarin sauya tasha “Yaya Aunty Nila kuka take?”
“Kuka” Safwan ya maimaita kalmar kukan ciki da mamaki, tashi ya yi ya nufi ɗakin Nabila ya samu har yanzu tana zaune tana kuka, zama ya yi gefenta tare da kai hannunsa ya dafa kafaɗar ta a tsoraci ta juyo ganin yayanta ya sa ta yi a jiyar zuciya tare da kwantar da kanta a kan kafaɗar sa cikin damuwa ya ce, “Me ya faru? Me ya ke damun ki?”
Cikin shisshiƙan kukan ta ce; “Yaya, Yaya Hafiz ne.” Cikin tsoro ya ce, “Wani Hafiz ɗin?”
“Abokin ka” ɗago ta ya yi daga jikin shi yana kallonta ido cikin ido ya ce; “Me ya ma ki? Kenan ba ki ji maganata ba ko?”
Ƙasa ta yi da idanunta cikin rauni ta ce; “Ka gafarceni Yaya Safwan na kasa tanƙwarar zuciyata ne kamar yanda ka umurceni har sai da na faɗa masa sirrin da ya ke ƙasan raina, sai dai tun da na faɗa masa gaba ɗaya ya sauya min, na rasa ta yanda zan shawo kansa zuciyarsa yanda ka san zuciyar danƙo hakan take da wuyar tanƙwaruwa.”
Cikin jin haushi ya ce; “Me ya sa ba kya jin magana Nabila, ai shi kenan kin je kin zubar da mutuncin ki kinyi farin ciki ko?” Ya mike tsaye yana ci-gaba da harararta ya ce, “Bari ki ji yanzu haka an tsayar masa da mata ‘yar’uwarsa dan haka sai ki natsu ki kama kanki ki kuma fidda rai da abinda ya ke gaibu ne a gare ki.” Yana gama faɗa ya fita daga ɗakin ciki da haushin ƙanwar tasa.
Tunda zancen tsayar da matar ya faɗa kunnenta bugun zuciyarta ya ƙaro tamkar zuciyar za ta fasu ƙirjinta ta fito, wani irin sanyi da bata taɓa ji ba ya ziyarto jikinta sai karkarwa take, kwanciya ta yi a kan gado ta janyo bargo ta lulluɓe jikinta hawayen idanunta su ka tsaya cak sai zugin yaji da take ji su na ma ta, wani irin so takewa Hafiz da har take ji a ranta idan ta rasa shi za ta iya mutuwa, shi ɗin tamkar magaɗisin rayuwarta ne.
*****
Da dare suna zaune su na dena a falon Daddy bayan sun idar Daddy ya ɗauke ruwan gora ya kafa a bakin shi ya sha bayan ya sha ya ajiye yana kallon Hafiz ya ce; “Hafiz me ya yi saura a kammala asibitin na ka?” Ajiye cukalen hannunsa ya yi yana faɗin “Daddy dama maganar da nake so na maka kenan komai ya kammalu har kayan aiki duk abinda a ka yi oder sun ƙara su yau da yamma In Sha Allah gobe za mu ƙarasa shirya komai In Sha Allah.”
“Ma Sha Allah to Allah ya sa albarka a ciki, ina ga to a saka ranar bikin buɗe asibitin watan biyu ko?”
“Hakan ya yi Daddy Allah ya nuna mana.” Khadija ƙanwar Hafiz da ba za ta haura shekara sha shida ba ta ce, “Yaya nima idan na gama karatuna a asibitin ka zanyi aiki sai ka dinga biyana albashi mai tsoka.” Dariya ya yi marar sauti yana faɗin “Ai bakin ki ne mai tsoka, da wannan ƙwaƙwalar taki ta kefe ne za ki iya karatun likita.” Ta turo baki cikin shagwaɓa ta ce, “Kina jinsa ko Momy ni ce mai ƙwaƙwalwar kefe ni da nake yin ta biyar.”
“Ƙyaleshi Khadin Momy ba kya ma son asibitin ta sa kema ta ki za a buɗe maki wacce ma tafi ta shi komai da komai.” Cikin farin ciki ta ce, “Yawwa Mommyna hakan ya mun kowa ma ya ji da na shi.”
“Yanzu ta biyar ɗinne har ki ke wani faɗa irin da ji da kan nan kamar kinyi wani ƙoƙari, ni tunda na fara karatu daga na ɗaya sai na biyu na ke yi, dan haka ki ƙara ƙoƙari idan har kina so ki zama likita karatun likitanci ba na marassa ƙoƙari bane na masu ƙwaƙwalwa ne.”
“Uhm Yaya zan baka mamaki kuwa na tabbata ko matar nan taka ‘yar ƙauye ba za ta fini ƙoƙari ba.” Cikin faɗa Daddy ya ce, “Idan na sake ji kin ce da ‘yar’uwar ki ‘yar ƙauye sai ranki ya ɓaci kinji ko?” Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba, Hajiya Turai ta ɗaure fuska har a cikin ranta ta ji haushin Daddy a kan me zai yi wa ‘yarta faɗa a kan bagidajiyar yarinyar nan, kallon Hafiz Daddy ya yi kafin ya ce, “Ka fara shirin auren ka dan bana so a ɗauki dogon lokaci, wata biyu ko uku da fara aikin ka sai a yi bikin.” Hafiz ya kai duban sa wajan da Hajiya Turai take a zaune ai kuwa ta sake ɗaure fuska, Daddy ya kula da yanayin Hajiya Turai hakan ya sa ya miƙe tsaye Hafiz ya ɗaga kai ya kalleshi zai yi magana Daddy ya ɗaga ma sa hannu yana faɗin, “Ni zan fita, ka kasance cikin shiri wata biyu ma su zuwa In Sha Allah za a yi bikin na ku.”
Ta shi ya yi ya biyu bayan Daddy yana amsawa Daddy, bayan fitar su Hajiya Turai ta ja numfashi ta furzar da ƙarfi “lallai wato Alhaji so ya ke ta ƙarfi sai anyi auren nan, shi kenan a yi auren wallahi daga ita har uwar ta sai sunyi dana-sanin Auren.”
“Momy ina bayan ki kina ganin yanda tun kan yarinyar ta zo Daddy ya ke yi min faɗa kamar zai dakeni ni wallahi har na ji na tsane ta tun kan ta zo, wannan ai inaga idan ta zo rabamu da Daddy za ta yi kamar ma ya fi sonta da mu wallahi.” Cikin takaici ta ce; “barni da su Khadija ai uwar ta ta san wace ce Turai dani da uwarta kar ta san kar ne, na tabbata ba za ta yi gigin kawo ‘yarta gidana a matsayin sirika ba, idan har kuma ta yi wannan gangancin tabbas ta san abinda ta yi!”
Gyaɗa kai Khadija ta yi ciki da gamsuwa da kuma jin daɗi dama tun suna yara ba shiri ta ke da Zhara ba, ta tsane ta haushin ta take ji yanda gaba ɗaya tafi ta kama da Daddyn ta lokacin idan ta zo hutu gidan kowa ya ganta cewa ya ke sak Daddy, shi kuma Daddy rasa ina zai sa ta ya ke dan so, kawai dan tana da sunan Maman su Daddy, ta ƙudurci a ranta matuƙar Zhara ta aure Yayanta sai ta ɗanɗani kuɗanta a wajanta.
*****
A ranta tana jin son Hafiz fiye da tunanin mai tunani, sai dai kuma kunyarsa ta ke ji gayan hakan ya sa take kasa sakin jikinta da shi, idan ya kira waya daga eh sai A’a hakan zai ƙarata surutun sa ya gaji su yi sallama, idan ya zo ba ta wani sakewa da shi, sai dai duk zuwan da ya ke suna samun saɓanin haɗuwa da Halima hakan ya sa har yanzu ba su ga juna ba, koyaushe ba ta da labarin da ya fiye yi mata daɗi irin zancen Hafiz wani irin so take ma sa da ba za ta iya kwantata irin sa ba. Tafe su ke a kan hanyar su ta dawowa bikin ƙawar su Zainab, Zhara ta ce, “Shi kenan kamar yanda Zainab ta rasa damarta ta karatu ta yi aure hakan za ta kasance dani.”
“Waye ya faɗa maki hakan? Ai ba za ki haɗa kan ki da Zainab ba dama ita kin sani tun a makaranta ta sha faɗa aure ne babban burinta ba karatu ne a gabanta ba, ke kuma kina da burin karatu na tabbata daga Yaya Hafiz har shi kan shi Daddy ba wanda zai hanaki karatu dukan su ma su tsaya ma ki tsayin daka ne wajan ganin burin ki ya cika.”
“Uhm! Allah ya sa, kin san me? Ina son karatuna sosai amma kuma son da nake wa Yaya Hafiz idan har ya ce ba ya da ra’ayin na yi karatu tabbas zan iya haƙura da burin karatuna na a jiye shi a gefe.”
Halima ta jinjina kai tana faɗin, “Na sani ai wallahi ki dinga kama kan ki Zhara wannan lokacin da mu ke ci ki ba a yi wa namiji irin wannan son domin su ɗin ba tabbas ne da su ba.”
“Na yarda maza ba su da tabbas amma ba duka a ka taro a ka zama ɗaya ba, ina da kyakyawan zato da yaƙini a kan ɗan’uwana Hafiz” dariya Halima ta yi kafin ta ce, “Uhm! Ke dai ki dinga sassauta zuciyar ki karki yi zurfin da ba za ki iya yin iyun da za ki fitar da kanki ba” shi kenan tunda har kina musu a kan Yaya Hafiz zo ki ki ji… Halima ta tsaya gaban Zhara tana murmushi ta ce, “Ba za ki iya ba,”
“Zan iya mana, ai da ba zan iya ba da ba zan faɗa ba.” Gyaɗa kai Halima ta yi, su ka ci gaba da tafiya suna ci gaba da fitar Hafiz.
Maman Zhara sosai ta shiga damuwa ta rasa ta wace hanyar za ta bi dan ta rusa maganar auren nan, bata isa ta nunawa Baban Zhara bata so ba ta tabbatar ko auren ta za ta iya rasawa a kan maganar, ta kuma fuskanci Zhara na son Hafiz duk da ƙoƙarin ɓoyewa da take sai dai shi so a bu ne da ko ka so ɓoyewa ba zai ɓoyu ba, dama Hausawa su kan ce a tambayi fuska labarin zuciya, dan haka fuskarta da yanayin ta ba za su ɓoye abinda ya ke zuciyar ta ba duk da ƙoƙarin hakan da take, bata da wata mafita da ta wuce ta dage da addu’a domin Allah kaɗai ne zai kawo mata mafita, amma har cikin ranta tana jiyewa Zhara tsoron zama da Hajiya Turai.
*****
Da yamma bayan ya fito daga asibiti a gajiya ya je liƙis dan yau C.S uku ya shiga ga marar lafiya da ya duba sosai, ya so ya wuce gida ya samu ya huta sai dai ba yanda zai yi dole ya biya ta gidan su Safwan ya duba mahaifiyar Safwan da bata jin daɗi, hakan ya sa ya karya kan motar sa zuwa Fage gidan su Safwan. A ƙofar gidan ya yi parking ya fito motarsa kenan Motar Safwan ta fito cikin gidan ganin Hafiz ya sa ya yi parking gefen motar Hafiz ya fito yana murmushi ya ce, “Fitowar nan da na yi Allah asibiti zan je wajan ka.”
“Lallai kuwa da ka dake garwa, daga can na fito na ce bari na zo na duba jikin Mama.”
“Ok mu ƙarasa ciki, Mama ta ji sauƙi kasan Asma lokacin ruwan sama ya fi matsa mata.” Suna tafiya ya ce, “Hakanne Allah ya bata lafiya, akwai wata allura In Sha Allah idan har a ka dace za ta samu sauƙi sosai ciyon sai dai ya zama tarihi.”
“Gaskiya da na ji daɗi wallahi ciyon yana matsa mata, kaga jiya babu wanda ya yi tsammanin za ta waye gari irin yanda numfashin ta ya dinga kai da kawo.” Suka ƙarasa cikin babban falon da sallama a bakin su, Rufaida da take zaune a kan kafet tana gyaran faruttan hannunta ta amsa Sallamar cikin fara’a ta ce; “Sannu da zuwa Yaya Hafiz, Ina wuni?”
“Lafiya lau Rufaida ya gida ya karatu?”
“Alhamdulillah Yaya.” Zama su ka yi a kan kujera Safwan ya ce; “Ji ki kira Mama.”
“To” ta faɗa tare da miƙewa tsaye, bayan ta kira Mama ta tafi ɗakin su da sauri ta samu Nabila tana kwanci a kan gado tana kallon hotonan Hafiz a wayarta, Fatima tana zaune tawayar Rufaida tana zaune a kan kafet tana karatu, Rufaida ta kai wa Nabila duka tana faɗin “Albishirin ki” Nabila ta harareta tana faɗin “Shi ne kuma dan za ki yi min albishir sai kin dakeni, yarinyar nan ba ƙaramin raini ne ya shiga tsakanina da ke ba wallahi.”
“Aunty masifa aunty son girma kamar gyanmbo, duka shekara ɗaya da ‘yan kai ne fa tsakanina da ke babu dole ma na kira ki a Aunty kawai dai dan Yaya Safwan ya tilastani ne kema kin san da ba ki kai na kira ki da Aunty ba.” Tashi ta yi da sauri za ta kai mata duka Rufaida ta kaucewa dukan cikin faɗa Nabila ta ce; “Daɗin abun dai ko da kwana ɗaya ne na riga wata shan iskan duniya, ki riƙi Aunty ban so marar kunyar banza kawai!”
“Shi kenan dama abinda ki ke so na zo na faɗa maki tunda ki ka min masifa na fasa faɗa maki sai bayan wucewar abun, idan kuma na faɗa daga baya kar ki ga laifin kowa kiga laifin ki.” Ta juya za ta fita da sauri Nabila ta janyota cikin lallashi ta ce; “Yi haƙuri ƙanwata ƙawallina faɗa min me ya in har albishir ɗin mai daɗi ne zan baki goro na musamman.” Murmushi Rufaida ta yi kafin ta ce; “Kinyi alƙawari ko me na ce ina so za ki bani?”
Cikin gyaɗa kai ta ce, “Na yi in dai abinda za ki faɗa ya kai na baki duk abinda ki ke so ɗin zan baki”
“Na ma san za ki bani ɗin dan ya kai, Yaya Safwan ne ya zo tare da Yaya Hafiz.” Zuciyarta ta bada dum! Ta kafe Rufaida da idanu harma ta rasa me za ta ce da Rufaida, “Ya dai Aunty Nabila?”
Cikin sanyin murya ta ce, “Da gaske ki ke dan Allah?”
“Wallahi da gaske na ke, yanzu haka suna babban falo” ta fita ɗakin da sassarfa ta nufi falo Fatima ta tashi da sauri tana hararar Rufaida tabi bayan Nabila gab da za ta shiga falon ta riƙo hannunta ta juyo da sauri taga Fatiman “Me ye?”
“Aunty Nabila tare su ke da Yaya Safwan fa, kin manta gargaɗin da Yaya Safwan ya maki kafin ya fita, kuma ya kamata ki dinga tuna ke ɗin mace ce da Allah ya yi wa tarin daraja, sannan mace a na so kunya ta zama a do a gare ta, kar ki bari zuciya ta dinga rinjayar ki ko yaushe tunani ya rinjaye zuciyar ki Aunty Nabila” shiru Nabila ta yi tana kallon Fatima yayinda zuciyarta da tunaninta su ke kai da kawo ta rasa makamar ɗauka, yayinda zuciyarta ta zaƙu da son ganin abinda take so, tunaninta yana tuna mata gargaɗin da Yaya Safwan ya ma ta, komai zai iya faruwa idan har taƙi bin abinda zuciyarta take so ko kuma ta tsallake umurnin Yayanta.
Da kyau Gwanar iya tsara labari.
Masha Allah!
Masha Allah, Allah yakara hazaka
Masha Allah aunty Allah😊Allah yakara basiya munayinki💯
Masha Allah
Mashaa Allah,Allah ya qara basira
Yayi kyau
Fatabarakallah
Masha Allah nice story
Allah ya kara basira
Madallah dake aminiya, Allah ya kara basira, labari yana dadi sai son barka, muna biye dake
Labarin Yana dadi Allah ya kara basira
Ma sha Allah
Masha Allah 💯
Ma sha Allah Allah ya Kara basira babbar marubuciya