Littafi Na Uku
Nurat taji gaba daya jinin jikinta ya daskare, ta zamo tamkar mutum mutumi gaba daya idanunta sukayo waje shikam gogan ko ajikinsa daidai lokacin Aazeem takaraso inda suke zuciyarta na wani irin bugawa nurat taja jiki daga kusa da didat tana faman huci tana tunanin yadda zata kare kanta, shiko gaba daya ya kafeta da manyan idanunsa wa,anda ke hanata sukuni aduk lokacin da tayi tozali da su dukan shirin ta na tarwatse wa, tasani shidin talaka ne wanda bai wuci ta tattaka shiba, sai dai tarasa abinda ke rusa mata dukka shirin ta maimakon sauke dukkan makamen data tanada, sai ta ɓuge da tambayar “yaushe kazo, har na ji tsoro jinake bazaka ka zoba, toho mu shiga ciki ta janyo hannunsa yau shine rana ta farko da hakan ta kasance a tsakanin su ko bi ta kan nurat ba tayi ba, haka yasanya nurat ta kara tsorata tasani tabbas yayar ta na fushi da ita, acan cikin zuciyar ta kamar zatayi hauka yadda taga Aazeem rike da hannu didat, yadda take jin wani irin kishin sa ya tabbatar mata da tsananin son da take yi mishi
*****
Tunda suka shiga holl din kallo ya koma kansu, hotunan su kowa ke kokarin dauka, gaba daya didat yayiwa Iyayen nata bazata yawuce duk yadda suke tunani yana da kamala babu alamar wahala atare da shi zuciyar alhaji usman ta nutsu da shi, ammi tadingajin wani sanyi da kaunar didat na ratsa zuciyar ta, ta tabbatar da dolene Aazeem ta kaunace shi musamman. yadda ta santa da kaunar duk wani abu mai kyau alhaji usman kam ya gama tabbatar da cewar surukin nasa zai iya zama jajirtacce, yadan ramkwafo daf da ita,” kema kinga abinda nagani ko? da ina tsoro kada na dorashi akan dukiya ta yazama cinye du, yanzu kam na sami nutsuwa lokaci daya sai Naji ya kwanta mini
Inda aka warema Nurat da Zaruk gune da yafi ko, ina haduwa kujerun kadai da suke zaune akai abin kallone, sun yi mutukar dacewa da juna, kallo daya zaka yiwa zaruk kafahimci tsakanin farin cikin da ya ke ciki yayi shigar kananun kaya yagaji da kyau komi na jikin sa baki takalmi agogo kayan jikin sa a bin ka da farin mutum sai ya kara haskawa bakinnan yaki rufuwa yanaji kamar ya gama mallakar nurat, dolene daga yau tadinga bin duk abinda ya tsara zaidinga juya ta yadda yake so zai shi zai dinga kaita unguwa makaranta kai duk motsin ta zai tabbatar da tare suke yi,yayi dariyar mugunta ya lura da yadda didat ke kallonsa yayi kasa kasa da murya, “waccan shine wanda kike ta hauka akan shi ko? Ta dinga jin kamar yana watsa mata garwashi ya kafeta da ido yana murmushi kumafa sun dace, kamar ni da ke dinnan ,uhmmm kawai tace m.c ne ya katse su da fadin “duk kan mutanen da muke jira sun halarta, yanzu zamu fara, da farko an fara kaddamar da kamfani ,Aazeem aka fara kira tare da Didat don tabbatar da shi a matsayin manaja, mc ya soma fadin yanzu zamu bawa manaja damar tofa albarkacin bakin sa, didat ya karbi sifika da sallama ya fara”nayi farin cikin yaddar da aka bani tare da girmamawa, sai dai abinda zan fada banason ayi min mummunan fahimta ina son zan fara da ban hakuri kowa yasani duk wanda za, a baiwa wannan mukami sai an tabbatar Iliminsa ya kai dan haka ni ban cancantaba, bana tunanin na kama kafar inda ake so dan haka ina mai sake baku hakuri ban cancantaba ya aje lasfikan zaruk ya dubi nurat ya tuntsire da dariya “kaji soko,kanta akasa tana faman latse latsen waya, “wayyo adam Meyasa zaka aikata haka,ta fada a ranta shi kuwa ya bace acikin mutane, mc ya bude murya “wannan matsalar cikin gidane dan haka mu cigaba da gashi.
“Karya yake yi ba haka mara ilimi yake ba alhaji usman ya fada, Aazeem ta koma gunsu zee suna tayi mata ciwon baki mezatayi da mutum irin wannan”ya fita da ban baya karya ina son haka, kunsan me ?kara sonsa nayi ya yi mutukar birgeni kallo ya koma gun su zaruk inda aka tabbatar da baikonsu inda aka tabbatar da cewar nan da wata biyar za, ayi bikinsu ita kam nurat takasa samun nutsuwa sai ware ido take cikin neman inda didat yake har sai da zaruk yaso ya fahimci hakan, yana gaisawa da jama, a ta saci jiki kamar mara gaskiya haka tadinga fakar ido wuf tayi waje zata iya gane motar principal wanda Adamu yake ara cikin sa, a ta gano motar kuma tana a bude da sauri ta bude gidan baya ta shiga bata zauna a kujerar ba durkusawa tayi yadda baza, a hangotaba kusan mintuna goma tana cikin motar taji an shiga a haukace aka ja motar ta tsorata sosai yadda yake figar motar ta rintse idanunta gam Sai da taji tsayuwarsa sannan tabude idanunta sannu da zuwa oga taji ana cewa, “duk wanda yazo nemana bananan abinda taji yana cewa kenan kada kubari ya shigo bana danjin dadi, yafito daga motar baimasan inda yake cilla kafafunsaba
A bathroom ya,ya da zango ya saki ruwa akansa yanajin hakan zaisa yaji dan sassauci babu abinda yaji yafito singlet ya saka sai gajeren wando ya shiga sintiri idanunnan sunrine zuwa jajaye ya koma bakin gado ya zauna yana faman haki, “with out you I don’t think i can live,abinda ya fada kenan a sarari tana jin sa
Tunda ya shiga wanka ta shiga samun gu tayi ta laɓe,mamaki da dairewar Kai duk sun dirar Mata da farko ya kawota tafkeken gida na biyu taji ana cewa dashi oga ,gashi yace duk Wanda yazo nemansa ace baya nan to Mai haka ke nufi can wani tunani ya fado Mata tasani cirani yazo da kuma almajiranci,tasani kuma irin almajirennan suna samun daurin gindin malamai dan dayawa suna saukesu a manyan gidaje kawai da su dinga taimaka musu da addu,a kuma dole masu gadinsu su girmamasu wannan hangen ne ya goge duk wani tamtama nata sai ta dingajin kunyar kayan da ya saka, tinanin yadda zata dosheshi a wannan. Yanayin take rintse idananunta tayi tana tinanin ta yadda zata fice batare da ya ganta ba a hankali ta bude ido yayin da suka yi ido biyu da wani katon muzuru wani irin kara ta kwalla mai karfi hadi da buga tsalle sai gata kane kane kwance a kirjin Didat idanu a rufe gam jikinta na faman rawa, tsayawa yayi saroro ganin komi yake tamkar a mafarki sai sake shigewa take jikin sa hadida sake kamkameshi, ya lumshe idanunsa Yana shakar kamshinta yayin da za zira hannayensa ya rungumeta sosai Yana Mai da numfashi baya fatan farkawa daga wannan daddadan mafarkin kukan da magen ta kyankyara ne yasanyashi dawowa haiyacinsa da sauri ya tureta gefe cike da tsananin kunya nurat mai yasa haka,Mai yasa Kika biyoni batason kallonsa”bansani ba”kina ganin kin kyauta kenan, bakya tsoron sanya kanki cikin matsala? muryarta na rawa idanunta sun rine Sabida kuka, “ban san nazo nan ba “zoki zauna zamuyi magana kinji akan carpet ta zauna takasa dago kai ya lura da hakan ya kuma san dalilin haka ya dauko Jallabiya ya saka ya komo kusa da ita shima zaman yayi Yana dubanta wani irin sonta ne ke yawo acikin jinin jikinsa yana jin kamar ya dauke ta su gudu, ya numfasa, “gaya min kukan me kikeyi alhalin muna tare,gaya min ba haka ne burin muba ? a hankali ta dago kai idanunsu suka gwuraya tsigar jikinsa ne ya dinga tashi, idan ta tino abinda ta aikata tamkar ta nitse ya numfasa, gaya min kukan me kikeyi alhalin muna tare, gaya min ba hakane burin muba a hankali ta dago kai idanunsu suka gwuraya batace komiba yasake maimaita tambayar, tanason tagaya masa yadda take ji game dashi, kiyi magana kinji, tabude baki da kyar”yazanyi ka fahimci Kaine farin cikina, lokaci daya ya daure fuska cikin kafeta da ido har sai da ta tsorata “OK abinda kika zo gayamin kenan?ta jinjina kai,ya daure fuska”bazaki taba birgeni ba tunda kedin matsoraciya ce,idan har da gaske nidin kike so ki bari in shaidawa iyayenki ya koma ya sassauta murya,ki taimaki rayuwar mu ki amince min na shaida wa iyayenki,gaya min kin amince min? da sauri ta kada Kai alamar a,a”Dan Allah ka kara min lokaci mubi komi a sannu”har zuwa lokacin da zan mutu ki auri wannan zaruk din ko,ya katseta da fadin haka,”ba haka bane kafahimceni Mana”ba haka bane gaya min menene to ?mikewa yayi ya motso kasa da ita idanunnan sun yi jajir ahankali ta soma ja da baya karaf taga ya danko hannunta bata San sa adda ta saki wata gigitacciyar karaba tana neman fita daga hayyacinta,tashiga kiciniyar kwacewa sai dai ko motsawa hannun nata beyiba ta rintse idanunta wasu hawaye suka shiga kaikomo daga idanunta tausayinta ya keji hakane yasa dan kansa ya saki hannun.a musulunce da Kuma Al adance babu inda aka tabayin aure da ciki,gashi lokaci daya kin dauki cikina kingani Allah ya tsaga da rabona,kinsan meyasa lokacin da yan ajinku suka rike Miki hannu baki dauki ciki ba? da sauri ta kada Kai idanunta taf kwalla ya saki murmushin mugunta,sabida basu rike Miki hannu da kyau ba kinga ni Kuma na rikeshi sosai kuma,ma tsananin sonda muke yiwa junanmu dale lokaci daya Zaki iya harbuwa da cikina, gaya min kamar wa kike son yar mu tayi?dora hannu tayi aka zata kurma ihu ya daure fuska hadi da dora yatsansa a labbansa “shishhh kada kiyi min kuka ya kai hannu ya sake rike hannunta yana Jaye da ita har suka koma setting room ya zaunar da ita akan kujera kuka takeyi aciki ya zauna yana fuskartar ta yana sonyin dariya sabida yadda ta firgice idanunnan sun rine zuwa jajaye,daga yau ni,ni kadai ne ya halatta na rike miki hannu,itadai kawai binshi take da kallo yanzu gaba daya haushinsa takeji ya mike wani daki taga ya shiga sai gashi ya fito dauke da take away ya ajiye agabanta ya bude kayan snacks ne aciki “bisimillah hawayen dake kwance a cikin idanunta suka karasa gangarowa dakalin fuskar ta cikin yanayin tsiwa”ni Babu abinda zanci ya danyi murmushi”yazama dole kici Kona karayi Miki wani cikin ya kai hannu zai sake riko hannunta da guda ta dauko ta soma ci”ya isheni haka bai ce komiba yashiga nade hannun rigarsa, nafi son ki haifa min yan biyu batasan sa arda ta cigaba da ci ba hannu baka hannu kwarya har sai da taga babu komi a ciki gaba daya ya kafe ta da ido tausayinta yakeji yasani ada tana yin rayuwar ta cikin jin dadi shigowarsa rayuwarta ya lalata mata komi, yasani so takeyi mishi mai zafi wanda zai iya haifar mata da illah rashinsa agareta zai rusa mata duk wani farin cikinta.
“Bazan bari hakan ta faruba ya furta afili,ina mutukar kaunarki. Ko da zan rasa Raina bazan bari na rasaki ba, matsalar kedin yarinya ce baki gama hada hankalinki ba shiyasa kike jin tsoro yakin zai zamo nawa Amman sai kin jure kawai binshi take da kallo batasan inda ya dosa ba”ina son zan koma gida,tace dashi ta mike tsaye sai yanzu ya lura da babu mayafi ajikinta idanunsa kur akan surarta yarinyace karama amman duk wata sura Allah ya mallaka mata yasoma jin wani yanayin da bai tabaji ba zuciyarsa ta shiga aiyana masa kada ya bari tatafi ya dauketa ya gudu da ita suyi rayuwarsu su kadai ta daga idanunta luu tare da dorashi akansa ras gabanta ya buga ga irin yanayin data ganshi gaba daya idanunshi sun sauya sun rikide kamar wanda yasha abin maye,ita dai sai taji tsoro ya kamata batasan meke faruwa da Shiba ta dukar da Kai kasa,zan tafi gida tafada a sanyaye yayi firgigit kamar wanda ya farka daga bacci ya sauke wani dogon ajiyar zuciya bai ce komiba ya shiga daki ya dauko hijabin da ya taba siyama nabila ya mika mata ko agida kada ki dinga cirewa inba haka ba kowa zai San kina dauke da ciki kinga idan muka lallaba komi yayi daidai sai ayi auren mu batare da kowa ya fahimci kin shigo gida na da ciki ba ko. idanunta sukayi raurau,no don’t kinga idan kikayi kuka za,a gane banason kinayin kuka ina son ki zama jaruma”sai ki tashi muwuce gida ko.” Maryam ta zabga mishi harara
“Jibeshi kamar wani mutumin arziki,to malam aika bari na sallameta ko.”
Daki tashiga sai gata da katuwar leda shake da kayan kwalliya ta Mika masa “babu yawa zuwan bazata akayi Mana.”