*****
Office din principal
“Da na rasata gwara narasa komi, ba dan alfahari ba zan bayyana musu gaskiyar lamari akaina.
Yayi shuru yana faman huci principal zai magana ya katseshi,
Muddin zan Sami Nurat zan basu duk abinda zasu bukata Koda kuwa ace duk abinda na mallaka ne,sabida kawai shashanci irin nasu sai adinga barin Yana fita da ita bata so Amman sai da mahaifinsu ya tilastata, wannan wani irin abune haka.
Yayi ta faman mita ta inda ya shiga batanan yake fita ba yanata huci kamar wani kumurci principal ya dafa kirjinsa
“Ina son mubi komi a sannu idan ita matar kace dole sai ka aureta.
Salim ya dubeshi cikin sanyaya murya
“Biyayyar ka ga ummi dolene ina son ka zama jajirtaccen namiji kamar yadda nasanka, idan kabari rayuwarka ta gurbace akan soyayya mutane da yawa zasuyi asara,ummin ka da mutanen da suke karkashin ka ,Nabila har da bebin da take dauke dashi,gaba daya”.
Didat ya sake ware manyan idanunsa akan salim
“Mai kake son cewa ne?”
“Abinda nake son sanar da Kai ne tinjiya Amman baka Sami damar dagan kirana ba”.
Ya kasa tantance farin ciki yake ko bakin ciki,
“Kuma flight lands iaman haka akeyi dagayin abu sau daya sai ciki ya koma ya zauna”.
Bai sake iya cewa komi ba,ta window principal ya hangi Nurat na tohowa,Salim ya yiwa inkia suka sulale daga office din
Tayi sallama Babu amsa Bata Kuma gane waye a zaune ba sabida ya juya baya gaba daya wani kamshi Mai dadi ya cika office din juyawa tayi zata fita yayi saurin juyowa cikin kausasshiyar muryar da Bata sanshi da shiba
“Sna zaki je?
Kamewa tayi a gun ya Sha gabanta Yana huci
“Gaya min jiya ina da ina kuka je da wannan zaruk din?”
Yanayinsa ya tsoratar da ita sosai takasa cewa komi ya sake bude murya
“Ba za kiyi magana ba?”
Duk ta gama tsorata
“Babu ko ina”.
“Karya kike yi idan baki gayan gaskiya ba sai nasa principal ya zaneki.”
“Kayi hakuri gidan su ya kaini”.
Ya dunkule hannu ya kaiwa bango naushi
“Oh shet gidan kuma,Mai yayi Miki haka kukayi da mutanen gidan ku ba asibiti aka tura kiba?
“nice na dage nace baza ni ba sabida in tsoro kada a gane abinda kace ina dauke dashi.”
ya furzar da huci
“Ko da ace kun je Babu Mai ganin cikin, na boyeshi nawane nini kadai Koda kasar waje za,a kaiki babu Mai gani.”
ya Kai hannu ya riko hannayenta ya dora akirjinsa Aiko jikinta ya hau tsuma kuka takeyi Mara sauti ko ajikinsa,
“Nurat ke ce farin cikina rayuwarta idan kika juyan baya Zaki cutar da, rayuwata kiyi min alkwari zamu kasance tare cikin kowani yanayi.”
Kokarin kwace hannunta take
“Ina son ne kiji yadda wutar sonki ke ruruwa azuciyata bakiji yadda zuciya take bugawa ba ko yaushe sonki zai iya haukata ni.”
ta katseshi cikin muryar kuka
“ni, ina son na haukace hakan sai yafiyi mini sauki, sabida shi mahaukaci bashi da damuwa sabida bai San wayeshiba bai San wata matsalaba,inajin ninkin abinda kakeji shaura kiris na mutu,idan ban kasance da kaiba bazan rayuba, ina sonka fiye da kaina bantaba son wani abu kamar kaba,kaine farin cikina.”
“kuka ya kwace mata wani irin sonsa ne ya dinga fisgarta
“,in sonka ko yakake ina son na rayu da Kai,rayuwa ta har abada,ina rokon Allah in har bazamu rayu tare ba ya gaggwuta dauke rayuwata,.”
bude ido yayi sosai Yana kallonta baiyi tinanin haka daga gare taba,tabbas yau ya tabbatar da son da take masa ya Kai kololuwa,Amman Mai yasa bazata bari ya sanar ba,ya soma magana cikin murya kasa,kasa
“kina da dama nayin maganar wa iyayenki,idan ba hakaba kinaji kina gani zamuyiwa juna nisa,Kuma ita Aazeem rayuwar mu bazai taba daidai ba bazan iya auren taba,ki kwarara. Zuciyarki mufito mugaya musu gaskiya”
“a,a nidai inajin tsoro mune mi wata hanyar dan Allah
gaba daya tausayinta yakeji ya Dan jinjina kai
“shikenan kada ki damu yau zanje garin mu idan nadawo zan nema Mana wata mafitar wadda bazata haifa Mana matsala ba kinji.”
ya dan kafe ta da idanu Yana murmushi,
“yanzu gaya min kinci abinci kuwa?
ta dan jinjina kai
“‘da kyau matar adamu haka nakeso kisaki jiki kinji idan kina takure kanki za,a fahimci halin da kike ciki kinji tawan.”
“tace to.”
“yauwa, Kuma ki dinga barin wayarki akunne idan ba hakaba bazan Sami nutsuwa ba kinga zan danyi nesa da ke haka ne zai Kara min kwarin gwiwa.”
,daga nan sakin jiki tayi suka dinga hira tamkar basuwa cikin matsala kawai binta yake da kallo cike da nishadi wani irin sonta na Kara hudashi yanaji tamkar ya sace ta su gudu sun rabu suna masu farin ciki
**. * ***. ***
Abuja
Kamar yadda ya Saba duk lokacin daya dawo sai ya fara biyawa ta shashen umminsa tukunnan idan ya huta sai ya wuce bangaren sa shashen abude Babu kowa ya zauna akan doguwar kujera cike da tunanin inda umminsa ta tafi a wannan lokacin ya kusa awa daya azaune Yana jira ya gyara zamansa ya duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya mike ya shiga lalleka lungu da da sakon dake gidan duk inda ya duba kamshine ke tashi,
“to Ina tatafi?
Ras yaji gabansa na bugawa cikin rashin kuzari yakarasa shashinsa asetroom yasoma cin tumtube da gwangwani shake da yawu gaba daya ya kware a kafafunsa ga wani irin yauki da wari na tashi tini cikinsa ya soma hautsinawa zaiyi amai kamar zai Sa ihu gaba daya tsigar jikinsa ya gama tashi da gudu ya wuce bathroom din dakinsa ya dinga kwara amai kamar zai amayo hanjin cikinsa bayan ya gama ya cire but din dake kafarsa ya cilla cikin abin shara daganan ya yi wanka har ya gama shirinsa baiji motsin taba,ya hau kan darduma yayi sallah Yana lazumi cike da takaici yasan watarana sai umminsa tayi Dana sanin kaka ba masa nabila da tayi,bai taba tunanin nabila zata kasance ahakaba, azahiri itadan Yar kwalisa ce mai son gayu ga tsurfa Ashe abin duk bigene ayau ya sake tabbatar da kazama ce ta gasken gaske,wani irin tsana yakeyi mata ayau,
ya mike daga dadduma ya nufo bangaren ta bedroom dinta ya kutsa. tana kwance bacci take tamkar matacciya gefenta wani sabon kuttun yawune ga kwanukan abinci a tsakiyar gado da alamun tana gama ci ta bingire agun Dan ga hannunta nan ko wankewa batayi ba,wayyo Allah wannan shine tawa jarrabawar ya juya zai fita sabida bashin da dakin keyi
motsinsa taji ta bude ido ganin shine yasa tayi saurin mikewa tana washe bako
“mutanen kano yau Kuma zuwan bazata akayi Mana.”
kallon inda take baiyi ba ya bar dakin ta rufa mishi baya jiki a sabule tasani yau ba lalle ya zauna agidan ba sai ta koma da baya sai da ta shiga bathroom ta wanke fuska da hammata ta fito ta sheka kwalliya har da su fesa turare ta koma ta nufi shashin sa sai dai me zai faru Gam ta hangi gun a kulle,ta dafa bango ta zauna a kasa tayi zaman dirshan cike da takaici Ashe abinda take zato ba haka bane tana jin cewar darajar cikin dake jikinta wannan karon zataga banbanci,to Amman ko dai Salim bai sanar masa da batun cikin bane,ta sauke ajiyar zuciya tare da kwararawa kanta gwiwa tasani baisan zancen ba ta mike zata koma shashinta ta ci Karo da yawo kwance akasa kudaje sun yayyame shi,gaba daya idanunta sukayo waje,”nashiga uku Ashe su dije basu gyara gidan ba azafafe ta nufi kitchen sai dai Babu kowa ta koma shashin masu aiki nanma ba kowa tayi kwafa tabbas idan tana son zaman lafiya kada tabari ya dawo ya Taras da gidan haka zaima iya tattarawa ya koma inda yafito dole da kanta ta shiga kintsa gidan sai da ta gama ta kunna turaren wuta kamar yadda mom dinta ta koyar da ita ,lokacinda ta kawo mata ziyara ta Tara’s da gidan kaca,kaca shikenan nabila tashiga lodo turaruka irin marasa dadin kamshinnan masu Hawa ka haka take gumbudasu kamar Yar bori yaukam taci wuya duk tayi wujiga,wijiga sai faman haki take abinka da wadda b
Saba ba ga Kuma kiba
Tunda ya fito abakin titi ya zauna zuciyarsa na faman saka masa abubuwa kala,kala yama rasa abinda ke damunsa handset ya dauko yashiga laluben lambar Nurat har tagaji da ringing Bata dagaba,yaja tsaki yaushe ne zasu Sami “yancin soyayya kamar kowa,dolene yakawo karshen lamarin ya cije lebe can yaji shogowar message ya shiga inbox ya bude
“,kayi hakuri ina tare da Ammi dafatan ka Isa gida lafiya
ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya,ya mayar da reply
“nasauka lafiya sai dai kewarki na damuna.kibani abinda zai sanyaya min zuciya dan Allah.
Tarubuta
“ni bani da komi”
ya rubuta
“Kina dashi.
tarubuta
“to gaya min zan baka.
ya rubuta
“ki taimaka min da hoton ki
“,ta rubuta bani da hoto Amman kajira zan dauka yanzu sai turo maka kaji.”
ba,afi mintina goma ba sai ga sakon hotuna ta WhatsApp yaci Karo da hotuna guda biyar duk sanye da hijab tayi kyau sosai hakan yakara mata kima a zuciyarsa ya dinga jero mata godiya ta voice Kiran sallar magriba ne ya Sanya shi baringun masallaci ya nufa sai da ya yi sallar Isha,I ya nufo restaurant ya ci abincin sabida ko ya koma gida umminsa bazata bashi abinci ba cewa zatayi yaci na matar sa,shi Kuma daga yau ya daina cin abincin gidan har sai ta gyara
Wannan karon ma ummi bata dawoba
“,oh God to me hakan ke nufi kenan,ummi bata kaiwa dare haka,Kuma duk inda take kafin magriba take komowa gida.”
,har ya gaji da gwada kiranta a waya domin dukkan layi kanta akashe suke,jiki asanyaye ya koma shashin nabila,sanye take da wasu irin fitinannun Kaya ya raba ta gefenta ya shige,ta koma gabansa ta tsaya kallo daya yayi mata ya kawas da kai
“sannu da zuwa.
batare da ya amsaba yace “
“ina ummita?
“batananne?
ya watsa mata harara
“ina tambayarki kina tambayata.”
ta kwantar da Kai tasan rigima yake nema
“,kayi hakuri kasan banajin dadi, ba mamaki ko tashigo dan ta sanar dani zata fita ta tara’s ina bacci”
mikewa yayi Yana faman zarya Yana Kiran layinkan duk inda yasan tana zuwa sai ai kowa yace bata zoba hankalinsa yayi mutukar tashi yayi saurin ficewa shi kansa baisan inda zashiba Yana faman zaga gari cike da zillumi har shabiyun dare Babu labarinta tilas ya Kama hanyar gida
dai dai lokacin nabila tagama take ciki da magungunan mata har sun soma aiki Babu abinda take bukata irin danamiji
Lokacin da ya shogo babu alamar walwala idanunsa sunyi bala,in rinewa ko gabansa baya gani ya kutsa kawai daki batare da ko kallon inda take ba
alwala yayi ya dinga jero sallolin nafila Yana faman addu ar Allah yasa kada wani abu yasami umminsa
Ta dade tsaye a kofar dakin tanajin tsoron shiga dole ta koma bedroom ta dauko handset ta lalubo lambar mamanta,cikin kuka ta soma magana
“,duk lokacin da yadawo bana samun farin ciki da zan iya dana hakura da aurennan.”
maman ta katseta
“to kinga kibari zuwa gobe zanzo sai mutoho gida kila idan yaga bakyanan zai shiga hankalinsa.”
“a,a mom bani da wannan matsayin idan nayi haka zaiyi farin ciki,ni dai kisama mini wata mafitar,banason narasashi”
“shikenan naji Amman yanzu gaya min Mai ke faruwa?
“mom yadawo dazu Amman ko zaman minti biyar baiyi agidan ba,kamar ma bayason ganina”
“Kai anya kuwa, kin Kuma gaya masa labarin cikin dake jikinki?
“a,a Amman nasan abokinsa zai sanar dashi”
“ba lalle bane yanzu kije ki sanar dashi da kanki kada kiji tsoro gobe zanzo komi zaiyi daidai.
Kabir ne ya fado masa da sauri ya mike zai fita sukayi kicibis da nabila
“naga key din mota Kuma naga dare yayi Ina zakaje?,
bai amsa mataba ya yi waje akan hanyarsa yashiga laluben layin Salim inda ya shiga sanar dashi abinda ke faruwa adaren Salim ya bi kafafen yada labarai don cigiya Kai tsaye shi Kuma ya nufi gidan Kabir kafin Kabir yafito kwantar da Kai yayi jikin allon kujerar mota Yana faman kuka kamar wani karamin yaro can yaji sako yashigo wayarsa ya bude wayar Yana tsammanin jin abinda ya danganci ummin sa ,sakon Nurat yagani kamar haka
“,inaji ajikina kamar wani abu maras dadi yana faruwa da Kai.”
bai karasa karatun ba yaji ana kwankwaso motarsa da sauri ya bude ya fito
Shima Kabir kuka yake wiwi
“ummi ba karama bace ballantana ace bata tayi wannan batan ta manufa ce Mai tayi musu Mai suke nufi da aikata haka agareta,tashiga wahala duk adomin ka,lokacin kana karam bata huta ba yanzu ma ba a kyaleta taba bazan lamunta ba wallahil sai ka nemomin ummina.”
ya hada Kai da garu Yana wani irin kuka, shima kuka yakeyi
“in da za,a dauke min komi nawa adawo min da ummina zan amince bazan jurewa rashin taba itace komina,Allah kada ka dora mini irin wannan jarrabawar.”
ya koma ya janyo Kabir din da har yanzu kuka yakeyi yarungumeshi
“,kada kayi kuka zamu samo mafita bazan bari wani abu yasa metaba da izinin Allah Koda dawowarta zai zamto sanadiyar barina duniya sai na dawo da ita garemu.”
Kabir ya fizge daga jikin Didat ya shige gida kawai Didat ya bishi da kallo
a wannan dare Didat bai rintsaba kulle kanshi yayi adaki kuka yake tamkar wani karamin yaro
nabila kuwa kamar zatayi hauka ga magani yafara aiki ga Babu fuska a gun oga Dan ita sabida tsabar jarabar dake cinta tama mance batun ummin yadda bai rintsaba haka itama tana ta faman murkususu kamar wata mai nakuda Kiran assalatu yaji yayi waje Yana ta faman zaga gari har gari ya fara haske babu alamarta haka ya hakura ya komo gida
tana zaune a set room taci kuka ta koshi ko bita kanta baiyi ba ya shige bedroom ya sake kullewa Yana zaune akam darduma yaji shogowar text da sauri ya mika hannu ya dauki wayar hannunshi har rawa yake ya shiga inbox,
“Idan har ka damu da mahaifiyarka sai ka fansheta da milyan dari uku acikin kwana uku muke bukata idan ba hakaba ranar Monday zaka tsinci gawarta a tsakiyar titi,daga yau zaka fara lissafi. da sauri ya mike tsaye Yana faman Kai komo muryar Kabir yaji a harabar gidan yayi saurin bude kofa a kofar dakin sukayi kicibis da shi idanunsa sunyi jajir sabida kuka ya kamo hannunsa suka shiga ciki akan kujera ya zaunar dashi
Yana faman walainiyoa da idanunsa cike da mamakin kayan alatun dake dakin komi Mai tsada ne ko a cikin Fina finan turawa bai taba ganin dakin da ya Kai wanna haduwa ba saukar hannun Didat ajikin sane yadawo dashi daga dogon tunanin daya shiga
“Didat Amman dai kasami labarin inda mamana take ko?
handset dinsa ya mika masa”duba kagani ya karba wani irin zabura yayi hadi da mikewa tsaye Didat ya kamo shi ya zaunar,
“ka kwantar da hankalinka ummina zata dawo Koda zan rasa komi nawa bazan bar taba inda nasan hakanne da ban shigar wa yan jarida ba”
“Kabir ya dora hannunsa akan hannun Didat,kudinnan yayi yawa tunda akeyin garkuwa da mutane ban taba jin inda aka bukaci tsabar kudi haka ba.”
Didat yayi murmushi Mai ciwo”
“Bakomi ummi tafi komi da kowa muhinmanci acikin rayuwata wallahi Koda Raina suka nema zan sadaukar Kai dai kabani lokaci zan tabbatar na basu abinda suke bukata.”
“Kafin wannan lokacin ya kamata a Kai musui aini , na Dan Sami nutsuwa tunda nasami masaniya akan ta ya fashe da kuka
“Da Babu Kai da bansan ya zanyi ba kagama min komi aduniyar nan samun Dan uwa irinka zaiyi wahala”
Ya rungumeshi Yana gursheken kuka.
Gaba daya gari ya dauka ko Ina ka murda labarin batan mahaifiyarsa Didat aka yi wanda ba,asan waye shiba
Haka labari ya zoga Aazeem murmushi ta dingayi tabbas lokaci yayi da zatasan waye shi Didat dinnan ta sani dolene ko yaki ya bayyana kansa yazama dole ta juyama adamu baya duk kuwa da yadda take mutukar kaunarsa in zai iya hakura tafara auren Didat inta gama cika muradinsa ta dawo suyi Aure sabida shine kadai takeyiwa son da bata taba yima wani ba.