“Mai yasa kika taimakeni alhalin bakisan niba.?
matar tayi murmushi.
“gaba daya naga kin tsorata ne Kuma na lura da cewar ke din bakuwace.”
“Aikuwa naji dadi na gode kwarai .”
Wannan kusan shine Karo na farko da ta tabayi wa wani dan adam godiya.
yanzu gaya min Ina zan kaiki ta gaya mata .
har kofar gidan su takaita sannan tayi mata umarnin da ta shiga batayi musuba.
“Sunana Aisha.
“ni sunana Aazeem nazo ne daga kano,kina da kirki.”
Aisha tayi murmushi.
“aikin fini kirki.
Gaba daya suka yi dariya lokaci daya suka Saba tamkar sun dade da sanin juna ba,a dadeba maman Aisha ta dawo daga unguwa nanma suka gaisa.sannan itama tace zatayi wanka Aisha ta Kai mata ruwan wanka .tare da nuna mata dakin da zata shiga ta shirya kanta
Tana bathroom mamakin kirki irin na su Aisha takeyi daman akwai mutane irin haka,
dole zata ga haka domin ita ba shiga rayuwar mutane takeyi ba ballantana ta ga cewar ana da kirkin tana tunanin yadda zuciyarta take haka ta kowama take hirar Aisha da mamanta takeji sama sama a inda ta tsinci muryar Aisha na fadin.
“mama hankalina bazai kwanta ba sai na tozarta Kabir kamar yadda ya tozartani sai yaji kunyar cin amanar da yayi ni wallahi bantaba ganin dabba butulu irin Saba.
bayan ta fito daga wanka ta kutsa dakin da aka umarceta ta shiga arba tayi da wani tanka sheshen hoton Kabir da Aisha sai dansu ras ras gabanta ya shiga bugun uku,uku da kyar ta iya shirya kanta dai dai lokacin Aisha ta kutso Kai ta Tara’s da Aazeem a gaban hoton.
“waye ne wannan din?
“uban yara nane.”
“Ashe kina da aure?
“a,a yanzu babu Aure a tsakaninmu.”
“Amman Mai yasa?
“Labarin nada tsaho.”
“Amman zanso Jin wannan labarin domin naga kunyi mutukar dacewa Kuma dagani auren soyayya kukayi bai dace ace kun rabuba alhalin har da yara.”
“ai ni ko a kiyama bazanso haduwa da Shiba inda ma ace nasan haka yake wallahi da ban aureshiba.
Kuka ya kwace mata.
“azzalumi ne ma cuci butulu ko dabba yafishi agurina sabida shi dabba yakan banbance Mai hidimta masa.”
“haba kawata yazaki dinga hada mijinki da dabba.”
acan karkashin zuciyarta take ayana cewa inma kare ne bata da matsala da hakan zata aure shi,ai ita irinsu take so sai dai adaya gefen tamtama take Mai yasa ya boye true colour dinsa ga mutane.
tayi murmushi amman wannan makirine tana son wannan salon ko ba komi Aisha ta kwarara mata gwiwa.
“kince Zaki kwan biyu mubari.kada na bata Miki lokaci gobe zan gaya miki .”
“shikenan Allan ya nuna mana ,ni bara na wuce zan shigo da wuri.
Lokacin da tasake komawa ma saukinta inda Kabir ya sauketa ko kadan Bata iya nuna mishi tasan wani Abu agama da Shiba ta saki jiki sosai fiye da jiya Dan ta naji aranta Allah yabata irin mutumin da take so har ta faraji aranta ko dai ta zauna dashi har karshen rayuwarta sai dai zuciyar ta taki aminta da haka din son adamu na nan kwance a zuciyar ta adamu shine ya dauko dukkan tsarin da take son namiji dashi ga kyau ga shi ingarma ba siriri bane ba Kuma kato bane can, duk lokacinda ta dora idanunta akanshi takanji tamkar tayi mishi fyade tana son kwantar da Kai a wannan faffadan kirjin nasa.
“Tawajena da alama kingaji ko.?
Ta dubeshi cikin salon kissa tayi far da manyan idanunta.
“Idan Ina tare da Kai bansan menene ake nufi da gjiiya ba .”
Ya janyota jikinshi cikin wani irin salo yake bida ita.
“tunda na dora idanuna akanki,komi ya kwance mini zanso mu wuce kano tare agama komi cikin kankanin lokaci ko.”
“ni din haka nakeso amman zan fara tuntubar dad dina kafin mukara sa ko.”
handset din sane ya dau ruri ya dauka yayi waje Yana amsa wa dai dai nan itama ta dauko nata wayar tashiga laluben layin abban su.
“rangida Zaki iya yin nesa dani daman.”
tana faman kyalkyale dariya.
“daddy nafa sameshi, daddy akwai labari ,sai dai kafinnan Ina son sanar da Kai nakusa shiga daga ciki. danshi ya matsu ma mutoho ayi komai daddy Yana Sona.”
“rangida kinsan kuwa mai kike cewa.”
“daddy munyi magana anjima yanzu nagaji bacci zanyi,ya Nurat da ammina?
Zai sake yin magana tayi saurin katse wayar.
***. ***. ***
“Jiya banga yaronnan ba kince Yana gidan babansa, zonan yarona .”
Ta dubi Aisha.
Ya sunansa?
“sunanshi Ahmad Didat.”
“Kice sunan babansa yaci kenan.”
Aisha ta dan yatsine fuska.
Sunan kanin abban sane wanda ya satar masa suna yake cutar dashi yake dodon gona wa mutane sabida tsabar zalunci.”
“ban fahimce kiba.”
daman ba lallene ki fahimtaba,Zaki fahimta ne kawai idan na baki labari.”
zanso jin wannan gwaramar.”
Zainab da halima sun tashi suna mutukar kaunar junansu sabida sun tashi marayu zainab ce babba ta yi aure yayinda rikon halima ya dawo hannunta ita halima hafiza ce ta alkur,ani Bata kumayi nisa a bokoba domin sunfi baiwa bangaren islama karfi halima yarinyace Yar baiwa Mai Kuma mutukar farin jini iliminta ya Sanya takan fita Musabaka Kuma ta ciwo gasa .
Wataran aka gayya cesu masabakar kasa da kasa duk wasu manya suka hallara nan ma halima ce ta zo ta daya tunda ta fara karatunta alhaji munir babban ma aikacin gwamnati ne haka ta bangaren kasuwanci ma ya shahara ya rike mukamin ministan kudi Kuma sune dattawan da ake jidasu masu Kuma fada aji a siyasar kasar nan ya kwadaita da ita cikin wa and sukayi mata kyautuka na bajinta hadda shi
bayan sun tashi a musabaka ashe yabi bayanta sai da yabi diddigin Nemo gidansu kusa. wata guda yana bibiyarshi ta haka wutar Sha,awarta ta dinga ruruwa a zuciyarsa a inda yakasa sarrafa kansa har sai da yasa aka daukota har gidan hutawarta
Ya dinga lallaminta da yi mata alkawarika kala kala ciki hadda na zai aureta idan ta amince dashi duk nacinsa bata amince ba hakanne yasashi you mata fyade ,sannan yasa aka maidata gida yayarta zainab bata iya fasa zancen ba sabida gudun surutun mutane shi kuwa Alhaji munir tunda ya aikata ya bar kasar baki daya ashe yatafi ya barsu da jangwam zainab tayita bikin kanwarta har ta Sami lafiya bacin tsangwamar da baban kabir keyi mata batada katabus
Sai bayan wata uku aka lura Ashe da ciki ajikin halima zainab tayi kuka kamar ranta zai fita baban kabir yasa su agaba ya dinga yi musu tijara zagin rana daban na yamma daban ga gore gore karshe ma yaji yayi wa gidan haka akayita yamudidi da halima har kawo lokacinda cikin ya Isa haihuwa ranar da ta haifi Didat aranar ta koma ga ubangiji tabar yayarta da jaririnta shi Kuma baban kabir yace kota Kai Dan gidan marayu ko ta bar gidan ta zabi daya ita kuwa ta zabi dan kanwarta akan danta da mijinta tattarawa tayi ta bar gidan inda ta kama haya ta ci gaba da kula da Didat
Yatashi da farin jini kowa sonsa yake ga kyau babansa shiya dinga daukar nauyinsa a boye har ya gama karatusa ya kama aikin gwamnatii Shima da Kuma kasuwanci
Umminsa ita ta dorashi kan duk wani tsani har yasan kansa tun kan yagama cika saurayi Allah ya daukaka shi abin kamar tsafi Yana son taimako Yana da tausayi yadda jama,a keson hadda sa masa girman Kaine yasa ya komayin komi nasa a boye Kullum kamar tunkudo masa arziki akeyi hakane yasa sunansa ya kewaye ko Ina batare da ansan waye Shiba yakanyi mu,amala da kowa batare da ansan Shiba takensa in an sanshi shine idan ba,a sanshiba ba shi bane
Didat ya auri wata shegiyar mata wadda shi kansa baya sonta sabida fitsarar ta da ita suke Shirye duk wata muguntar da zasu kullawa Didat Kuma har yanzu baisani ba.
Kabir yadade yana lallaba Didat akan ya amince da tayin da jama,a sukeyi masa akan ya fito takara
bayyi nasaraba ya komo yace dashi to Yana sha,awa Didat ya bada kudi kudi shi zai fito Didat yaki hakanne ya tinzirashi ya sace uwarsa yayi garkuwa da ita azuwan wasune sukayi ya Kuma nemi kudin fansa har milyan fari uku tsananin sonda Didat yaka umminsu ne yasashi badawa da wannan kudi Kabir yayi amfani ya fito takara da sunan Didat ga alama zai iya lashe kuri,a sabida Didat nada masoya Koda Bai bada komiba za,a dan dangwala masa
Aazeem ta jinjina kai cike da mamaki tare da takaicin yadda ta bada kanta ga Kabir.
“Anya kuwa wannan mutum ne.”
“wannan ko shedan dole ne ya sallama masa.”
“taya zan iya ganin Didat ?
“ni kaina bana ceba sai dai Ina da hotonsa.”
Tayi tattataki gaban wata Yar karamar akwatu ta zugeshi ta dauko wasu hotuna guda biyar ta komo ta mikawa Aazeem.
shingin kiris numfashinta ya dauke.
“Aisha taci gaba da fadin arayuwata ban taba ganin mutumin arziki irin Ahmad Didat ba,burinsa Kullin ya magancewa masu rauni matsalarsu,yakan dauki matsalar wani ya mai dashi tasa,har yanzu da bazarsa Kabir yake rawa,ya Kuma San waye Kabir amman bai taba kulawa ba__
yadda Aisha taga fuskar Aazeem ya saiya ne yasa ta dakatar da maganar tata.
“ya kawata kinsan shine?
“Ina ai Al,amarin ne ya yi matukar rudar dani abu sai kace a film,yanzu Ina shi Didat din bawan Allah.”
“Tunda ya raba shi da ummin su ban sake Jin duriyar Saba Kuma ita nabila ba shiri muke da itaba ballan tana in tumtubeta.”
“Aiko yakamata ki tuntubeta kodan kiyi mata jajen abinda ya faru.”
ido waje ta dubeta.
“wani,tab rufa min asiri da nabila matar da ko kallon mijinta kayi sai tayi kamar zata shakeka .”
“naga kedin matar wansace Kuma ke matar aure ce.”
“ai Bari kiji Koda ni tsohuwa ce yanzunnan taga Ina mu,amala dashi sai ta yagani.”
“tab lalle wannan bala,i ce.”
“ta wuce duk inda kike zatonta dan haka ma suka jone da Kabir din.
Aazeem jinta takeyi kamar ta hadiyi zuciya daman kokadan bataji Kabir yayi mata ba bai taba birge taba ashe akwai dalili,takara kurama hoton Didat ido tanajin wani irin sonsa na kara bin ko Ina na jikinta.
dolene duk inda Didat yake ta nemeshi zata koma gida ta sake sabon shiri tayi murmushi tanaji Ahmad ya gama zama nata Nurat ce ta fado mata kawai taji wani irin tsanar ta, yarinya sumsum da ita ashe muna fukace zata bata mamaki kallon sa bazata sake bari Nurat din tayiba yanzu zata fito ta nuna wa Nurat din tasan abinda take kullawa shi Kuma kabir bazata sake bata lokaci akan saba dole ta koma gida yau dinnan.
“Kinyi shuru kawata ko dai har yanzu jimaminne.”
Aazeem ta sauke ajiyar zuciya.
“gaba daya hankalina yayi gida Ina son komawa yau.”
KANO
kallo daya ammi tayi mata ta dauke kai daman Aazeem tana tsammanin haka daga gareta tunda ba sallama tayi mataba ballantana tasa rai da samon kyakkyawar tarba.
ta aje Jakarta ta zube akan doguwar kujera kusan mintina goma tana ahaka daga bisani ta dubi ammi.
“sannu da gida ammina.”
ta dubeta kawai cikin jinjina Kai.
“kece da sannu ai.”
Nurat ta fito daga daki da gudunta zata fada jikinta da sauri ta matsa.
“wai ke bakisan kin girma bane .”
Tafada cikin daure fuska,Nurat duk jikinta yayi sanyi ta koma gefe ta rakube
Aazeem ta dubeta shekeke.
“Ji yadda kika bi Kika lalace Wai ko har yanzu kina kan bakanki na kin zaruk di.”
Nurat batace komiba
“Tasake cewa to in bakya son sa ki gaya mini wa kikeso?
“Ke Nurat taso toho nan kinji.”
“au ammina ni din da nake bakuwa aini yakamata ki lallabaa ,amman dai yau baza muyi fada ba domin ina cikin farin ciki.”
ta mike tayi tattaki zuwa inda ammi take ta kwanto ajikinta.
“ammi na na kusa komawa yadda kikeso burina ya kusa cika gaf nake da nayi aure zan auri Didat kota halin kaka.
Kallonta suke daga ammi har Nurat.
“waye Kuma Didat.”
Aazeem ta gyara zamanta .
ta fara zayya nu musu halaiyarsa daga karshe ta shaida musu shine adamunta.
ba Nurat ba hatta ammi ta shiga rudu .
“ammi ai sai ma kin shiga cikin jama,a zaki tabbatar da yadda ake son Didat,dan haka ashirye nake nayi komeye akan duk mutumin da zai shiga tsaka nina dashi koma waye gaba daya burina akansa yake Ina mutukar sonsa .”
Tana magana tana kallon Nurat wadda gabanta keta faman dukan uku,uku. karshe tashi tayi tabar gun
Aazeem tabita da wata katuwar harara gami da Jan tsaki
Mtss.
***. ***. ***
“Yakamata mutsaya mu tattauna akan matsalar yaran mu.”
kokarin mikewa yakeyi .
“Bazan tsaya sauraron wannan shirmen nakiba.”
Ta jinjina kai cike da takaici.
Kayi hakuri naji amman maganar nada muhinmanci.”
Komawa yayi ya zauna Yana dubanta
“Kuma kintsaya kina kallona kiyi min magana nifa sauri nakeyi.”
Ta kwashe komi ta gaya masa hadi da alwashin da Aazeem taci.
“Shikenan faduwa tazo daidai da zama,Allah ya kawo Mana mafita wallahi Nurat na Raina nasani sarai basan zaruk takeyi ba yanzu inhar Didat din ya kawo kansa zamu maida akalarsa ga Nurat inyaso ita Aazeem sai ta auri zaruk daman can da ita ya dace,naga abokin tane tare suka taso tasu tazo daya.”
” Haba yallabai kada muyi karanta Mana ka mance haliccin da babansa yayi maka?
“Kinga bana son wani tsari na tabbata muddin na baiwa shi Didat yake ko adamu Nurat zai bani ninkin abinda baban zaruk din yabani
Gaba daya ta ji kamar ta rufeshi da duka.
“Jinakeyi girma ta Sanya ka tuba daga duk dabi,unka na baya, ashe dai Mai Hali baya taba sauyawa.”
daga hannu yayi ya tsinka mata Mari .
Ta dafe kunci hawaye na faman saraftu daga idanunta.
Wallahi sai dai idan babu Raina ai itama Aazeem “yace kada kaganta a haka ka zaci bana sonta Ina sonta fiye da komi.”
“Shikenan muzuba mugani aga Wanda zaici galaba.
Nurat wadda akunnenta duk wannan maganganun suka wakana,bushewa tayi da mamaki mamakinta na farko da ammi ta fifita Aazeem akanta yayinda ta daye gefen take mamakin yadda abban nasu ya goya mata baya
” To Mai ke Shirin faruwa.
Gaba daya gidan ya zamo babu dadi yayinda daga ammi har abban nasu ke zaman jiran zuwan Didat ita kuma Aazeem ta dunduma neman sa wurjanjan sabida tasami labari agun Aisha matar Kabir cewar Yana kano haka ammi bata fasa Shirin bikin Nurat ba yayinda abban nasu ya ce akara masa sati guda.
Tana kwance hawaye na bin ta gefen idanunta tanaji aranta tabbas akwai abinda su ammi ke boyewa ta fahimci ammi tafison Aazeem da adamu sai dai akwai wata akasa mai yasa haka,Mai yasa ammi ta zabi yayarta tayi rayuwa da Aazeem fiye da ita ashe abinda ta gaya mata kawai a iya bakin ta ya tsaya.
Atika Mai aikinsu ce ta shigo dakin a sukwane tana faman kwalawa Nurat Kira tunda ta tafi garinsu watan ta biyu kenan batanan tana can tana jinyar mahaifiyar ta dawo warta kenan babu wadda take dokin son gani irin Nurat da gudu Nurat ta mike ta fada jikin atika tana wani irin sheshsheka.