"Mai yasa kika taimakeni alhalin bakisan niba.?
matar tayi murmushi.
"gaba daya naga kin tsorata ne Kuma na lura da cewar ke din bakuwace."
"Aikuwa naji dadi na gode kwarai ."
Wannan kusan shine Karo na farko da ta tabayi wa wani dan adam godiya.
yanzu gaya min Ina zan kaiki ta gaya mata .
har kofar gidan su takaita sannan tayi mata umarnin da ta shiga batayi musuba.
"Sunana Aisha.
"ni sunana Aazeem nazo ne daga kano,kina da kirki."
Aisha tayi murmushi.
"aikin fini kirki.
Gaba daya suka yi dariya lokaci daya suka Saba tamkar sun dade da sanin. . .