Skip to content
Part 33 of 34 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu H. Muhammad

“Baby na,kinci abinci kuwa?

” Bana jin yunwa.”

” bazai yuwuba.

hannu yasa cikin aljihu ya dauko handset dinsa Salim ya Kira ya sanar dashi Yana bukatar takeaway.

“da izinin Allah daddy Yana cikin rahamar ubangiji kada ki dinga daga hankalinkiki addu,a ce zata tabbatar da kaunar da kokeyi masa kinji.

Salim ne ya shigo da take away ya Mika masa parpesun kayan cikine kawai sai kayan fruit ya shiga bubbude mata da dagewa akan sai taci.

“yaya deedat bazan iya ciba nace da Kai nakoshi kaji.”

“No baby na kinga anjima yan uwanmu daga bangaren daddy na zasuzo nafison su ganki da kuzarinki kinji ki taimakeni nannade hannun rigarsa ya yi hannu ya tsoma dibo ya nufi bakinta dashi.

“Kayi hakuri to zanci da kaina.”

yayi murmushi.

“Amman dai kinga na bata hannuna sai kici wadda na dibo ko.”

babu yadda ta iya haka ya tallafo kanta kamar wata jaririya ya saka mata abaki ya sake Kai hannu zai sake dibowa sai tayi saurin tsoma nata hannun ta dibo ta Kai baki haka ta dinga diba tanaci gaba daya ya kafeta da idanunsa yana Mai sake godewa Allah daya bashi Nurat handset dinsa ne ya dauki ruri ya dubi fuskar wayar Kiran nabila ne ras gabansa ya buga gaba daya ya mance da babinta.

“Oh god.

Ya mike ya danyi waje tana Jin muryarsa sama sama.

“bana tinanin zan dawo nan kusa idan wani abin kike bukata zan turo miki.

Can sai taji shuru alamar ana magana ta daya bangarenne can sai taji ya sake cewa.

“nace dake ba zan dawo nan kusaba dole dawowata shizai tabbatar miki da cewar Ina son baby na,pls ki kyaleni haka zan nemeki anjima .

Ya katse wayar

da matarsa yake waya wadda umminsu ta bata labarinta dazu Kuma har ma tana da ciki wani kishine ya taso mata tacika tayi makil .

Lokacin daya shigo jitayi kamar ta rufeshi da duka.

“Mai yasa bazaka iya amsa waya agaba naba?

Kallon mamaki ya komayi mata yadda ta birkice saima ta bashi dariya ya san umminsa ta Bata labarin nabila.

” baza,a sakeba tunda bakya bukatar haka ko.

mikewa tayi .

“Ina zakije ai ban sallamekiba.

Idanunta taf kwallah.

“Nagaji kaina nayi mini ciwo kwanciya zanyi.”

bata tsaya jin amsar Saba tayi saurin barin dakin hankalinsa yayi mutukar tashi ya shiga kiranta a waya fir Taki dauka dole ya hakura.

bayan sallar la,asar babu abinda kakeji sai kugin motoci har dasu jiniya  gaba daya jama,a sun shafe layin babu masaka tsinke dangin Alhaji munir ne da abokansa har da gomna maici yanzu.l wannan rana deedat yaga gata babu Wanda ya nuna Yana kyamarsa sai albarka da suke samasa kamar zasu cinyeshi cikin gida ko hajiyoyi ne da mankyan mata Kai da ganinsu basai ka tambayaba sunci sun tada kai.

yanzune Kabir ya gane rashin wayonsa tabbas ancishi wasa Mai yasa za,a hada baki da umminsa aci amanarsa yasani karshensa gidan yari kawai kallonsa akeyi yasani umminsa ta sanar dasu shine yayi garkuwa da ita ya,yada makamansa tabbas kabir yanzu yafi karfinsa ta ko Ina dolene ya bar kasar zuwa inda baza,aji duriyar saba ,Shima dai zaruk haka take daga bangarensa sai dai bai karayaba bazai iya rayuwa babu Nurat ba duk yadda yadda,ayi sai ya gudu da ita .

Kabir ne ya Kira nabila ya shaida mata duk abinda ake ciki har labarin ganin mahaifin deedat da yadda umminsa taci amanars,a inda nabila taci alwashin sai ta kashe Nurat sai dai hakan ya zamo sanadiyar mutuwarta itama tini ta fara Shirin tohowa kano batare da sanin deedat ba.

deedat da bayason mu,amala da mata amman yau yasake da dangin abbansa kowa yana nuna masa kulawa Hira sukeyi sosai suna faman tsokanarsa da fadin yayima Nurat waye ya aureta sabida ita din karamace tilas ya Dan batarai kada afada agabanta kanta ya fashe.

Yar kanwar babansa Mai suna Salma ta matso kusa dashi tanayi masa rada.

“Yayana aina ka samo wannan balarabiyar gata so could bata da haya niya kyawunta Mai shiga rai Ina kaunar ta.”

yadinga murmushi ita dai Nurat gaba daya ta kasa sakewa sun sakata a tsakiya yan uwansa maza da samarin suka fara shigowa bayan mankyan sun gama tasu gaisuwar  mayafine ajikinta gaba daya idanunsu akanta deedat yadinga yi mata inkia data gyara gyalen oho batamasan yanayi ba abinka da yan boko sai yabata sukeyi yako cika kamar zai fashe ya tura mata da text bata dubaba hakane yasa shi yimata flashing nan ma ko ajikinta yayi kwafa.

Salma ya Kira awaya yace ta Bata wayar da Salma ta Kai mata wayar kin karba tayi sai Salma ta zaci kunkya takeji kawai ta kyaleta ta koma ta sanar dashi cewar bata karbaba kunkya takeji ya cije lebe.

“matar yayan mu kizo inji Yaya nazir ku gaisa yana haraba.

Aiko ta mike da gayya,shima tanason yaji abinda takeji gama dashi,

“Ke Wai Ina kike Shirin zuwa ne keda ake zuwa gunki gaisuwa kace masa anyafe inta zo gida yayi mata.”

haj Saratu wadda take kaka agunsa tace

“haba jikana ka barta taje Mana ai ba cinyeta za,ayi ba ke wuce ki tafi kinji.

Aiko da sauri ta wuce yadingajin kamar ya shako kakar tasa fakar idonsu yayi wuf ya wuce sauri yake kamar zai tashi sama kanta kaiga harabar yacimmata ya fincikota wani dan lungu gaba daya ta zube ajikinsa yana faman huci.

“waike maike damun kine,Mai ya hanaki daukar wayata Mai ya hanaki duba text dina gaya min?

“babu komi kayi hakuri na daina.”

takaici ya isheshi

“ke da anyi dan motsi sai kice ayi hakuri,to anki a hakura kigaya min duk Mai ya janyo haka nagani fushi kikeyi dani.

ta rausayar da kai sai ga kwallah sharshar.

“nace bazan sakeba kayi hakuri.

ya sake mannata ajikinsa sosai yana kokarin zuge mata zip idanunta suka firfito.

“Innalillahi,yayana Mai kakesonyi.

yakasa magana lalubo bakinta yake yi da karfi ta kwace daga hannunsa ta koma cikin gida,yabi bayanta kawai da murmushi.

Cincirindon mankyan motocin data ganine ya firgitata ta tsaya daga can nesa lambar Kabir ta laluba tare da gaya masa inda take.

Cikin motar sa Mai duhuwan glass suka shige yafara koro mata bayanin abinda ke faruwa bayan yagama gaya mata ya dora da fadin.

“deedat yayi min nisa ya gaji arziki gaba da baya Koda Bai nemi siyasa ba bazai tabayin talauci ba dan hakama na yada maka maina mutumin da nake takama zai taimaka min mahaifin sane Kuma ma duk da ya auri ummina babu abinda zan karu dashi dan yanzu haka tadaina kallona amatsayina da ko dama can tafi son deedat ballan tana yanzu data gane wacece ni.

“Ok naji yanzu kenan Kai ka saduda?

“To ai babu abinda zan iya dauka ajikinsa wahala kawai zansha gwarama na lallabashi ya mance komi hakan zaisa in shiga aljihun arzikinsa,yanzu gaya min ke meye shirinki?

Murmushi tayi.

Nina barwa kaina sani,kawai kayi mun jagora zan yi musu gaisuwa.

“bazai yuwuba,nida nake neman gindin zama bazakisa na dabama kaina wukaba ga gidan can.

Yayi mata nuni.

babu zato babu tsammani ya hangoto ko dar baijiba ya dauke kai kamar baigantaba ta shige ciki.

kallon shekeke takema mutane babu Wanda ya kulata ganin hakane yasa tilas ta sauke girman kan ta gaishesu sannan ta tambay tana son ganin matar deedat can dakin Nurat aka kaita .

Tana zaune Akan darduma da alkur,ani agabanta tana karatu,ko sallama batayi ba .

“Sannu da zuwa.

da kyar ta amsa sabida wani irin kishi daya tirniketa taja tsaki.

“Kece matar deedat ko?

Sunkuyi da Kai kawai tayi.

“Ashe kece Kika rike minshi anan ko.

Nanma bata yi magana ba.

“Amman dai yasanar da ke cewar Yana da mata har da ciki ko kuma–

Kukan wayar ta ce ta katseta ta duba wayar lambar deedat ne ta Kara a kunne

“Kisameni a bayan gidannan.

“Mai yayi ruwanka dani, ni gaisuwa nazo ba gun kaba dan haka kayi ta kanka .

Ta katse masa wayar.

tana duban Nurat kyawunta yafi komi daga mata hankali,wani abu ta tino sai tayi murmushi,gwarama ta saki ranta hakane zai saka yarinkyar ta saki jiki da ita har ta aiwatar da abinda tayi niyya.

Itama Nurat Kiran deedat ne ya shigo wayarta zataki dagawa kalamen daddin ta suka dinga dawo mata amman tanajin nauyin dagawa agaban nabila sai da wayar ta katse tayi saurin tura mishi text.

“Ko Zaki iya kaini gun ummin sa?

“Eh tashi muje tana bangaren baki.

umminsu ta Dan kadu da ganinta hadi da mamakin yadda ta gano gidan.

“Ikon Allah kece?

“Eh ummi nice daman nayi niyar zuwa anyi Miki Allah ya Sanya alkhairi amarya wato ke,sai Kuma na sakejin ance yaya deedat ya yi amarya shima ,amman tare akayi auren naku ko.

Nurat bazata iya jure Jin wannan fitsarar ba satar jiki tayi ta fita dakinta ta koma takasa zaune ta kasa tsaye deedat ne yashigo asukwane.

“Babu abinda tayi Miki ko?

ahankali ta daga Kai idanunta taf kwallah

“Oh god ke da anyi magana sai kisa kuka

,ya janyo ta jikinsa yana rarrashi gaba daya haushinsa takeji ankya zata jure hada miji da wata.

Ya Kai hannu yana dauke gashinta daya barbazo mata fuska har Yana kamashi da ribon itakam ta zamo kamar kurma

Nabila ta turo kofa adaidai lokacin,hakan baisa yafasa abinda yakeba itama Nurat din ko ajikinta asalima Kara shigewa tayi jikinsa, jakan ya tabbatar masa da cewar yasami  jaruma yaji dadin haka sosai da Yana Raina wayonta yanzu yatabbatar da wayonta ya danyi murmushi .

batayi sallama ba dan haka sukayi biris da ita nabila jitakeyi kamar tayi hauka.

ta dan kada kai .

“banzo nan dan ka wulakantani ba.

“Waye ya janyoki yace sai kin shigo lalle nan dakin matata ne kamata yayi kiyi sallama idan an amsa sai ki shigo amman kawai kin wani kutso kai sabida haka wannan matsalarki ce.

“Kumama Ina son ki shaida min da izinin wa Kika kamo hanya Kika toho?

yasake daga murya har saida Nurat ta tsorata gaba daya kamar ba deedat dinta ba.

to kisani bada izinina Kika tohoba Kuma kada kiyi tunanin cewar zan shiga sabgarki daga yau har ranar da zaki koma.

Ya janyo hannun Nurat sukayi waje ta zube akasa tana faman kuka tare da cin alwashin kala,kala

***.              ***.               ***

babu alamar nadama atare da ita Sam mutuwar sa bata sanyata taji komiba,tinda aka tsareta bata da abinda take firtawa in banda bazata Bari akai gawar wannan mutumin gidan taba ai gidan tane kudin tane kudin ubanta ne,hankalinta bai tashiba sai da baban zaruk ya nemi kudaden da yake bin dad a inda ya kwace kamfaninsa da ya bashi da duk wasu kadarori har gidan da suke ciki ya koma na baban zaruk shauran ma sai yafewa akayi , kuka takeyi sosai idan ta tuna bata da komi,takara tsanar sa sosai”

“bazai ga da kyauba sai Allah ya tsine masa

gaba da muryarta ta karade police station din deedat ne ya shi  tare da wani dan sanda tafara tisge tisge tana zagisa kawai murmushi yakeyi cike da tausayinta.

“Kiyi hakuri Aazeem nasan abinda kikeji nazo ne muyi magana.

“Katafi banason ganinka bana son ganin kowa banason kowa a rayuwata na tsane ku,ni nasani bani da sauran gata kowa baya Sona.

Ya sassauta murya.

Kowa yana sonki ,muna kaunarki ammi na mutukar kaunarki haka kanwarki Nurat.

“Karya kakeyi ,sabida babanta ya zalunce ni ya danfareni ya rabani da komi yanzu niba komi bace Ina son na mutu sai na mutu.

Hannu yasaka cikin aljihu ya dauko wayarsa ya kunna muryar daddy nasu ta nutsu sosai kaf tagama ji jikinta yayi sanyi ta sake rushewa da wani irin kuka.

“Kana nufin karya yakeyi ma ammina,to ni waca irice ne

Ta zabura kamar mahau kaciya.

Ammina tanayi min fada tana dorani akan tarbiya dad Yana rushewa,bazan mantaba Tasha wahala ahannunsa sabida ni ashe makircin sane gashi yanzu narasata na rasa kadarorina.

ya matso kusa da ita ya zauna.

“Kina sha,awar ki gyara kurakurenki,za ki iya  zama da ammi da Kuma Nurat.?

ahankali ta kada kai .

“Amman ya zanyi bani da komi,bani da kudi tayaya zan iya rayuwa ahaka,bazan iyaba.

Takaddu ya Mika mata ta bude .

Gidan da baban zaruk ya karba deedat ya siya mata ya mallaka mata kamfanin baban nata ya ya Kuma bata zunzurutun kudi milyan arba,in tare da sama mata ma aikata a kamfanin daya bata.

dubansa tayi tana murmushi ta durkusa tana godiya.

“Bakya bukatar haka kefa yayar muce kawai dai burina ki fito da mijin aure.

tare suka baro gun dashi

Kai tsaye dakin Nurat ta fara nufa adokance cike da wani sabon kaunar ta dai dai lokacin Nurat na bacci nabila tsaye akanta tana kokarin bude wata Yar karamar kwalba sabida shagala da tayi har Aazeem ta turo kofa ta shigo batajiba ganin abinda ke faruwa yasa ta dauko waya daga ta soma dauka wani irin hayaki ta hanga Yana fitowa daga cikin kwalbar jingina wayar tayi ajikin drowa ta yo kan nabila suka shiga kiciniyar kokawa,Allah ya baiwa Aazeem sa,a ta kwace kwalbar ta watsa mata abin cikin kwalbar a fuska kan wani lokaci tini fuskar nabila ta kwakkwabe wata uwar Kara Aazeem ta saka hakan ya janyo hankalin jama,ar gidan dai dai lokacin deedat ya shigo gidan har dashi aka kutsa dakin har yanzu Nurat bata farkaba ,Kai tsaye dakin Nurat ta fara nufa adokance cike da wani sabon kaunar ta dai dai lokacin Nurat na bacci nabila tsaye akanta tana kokarin bude wata Yar karamar kwalba sabida shagala da tayi har Aazeem ta turo kofa ta shigo batajiba ganin abinda ke faruwa yasa ta dauko waya daga ta soma dauka wani irin hayaki ta hanga Yana fitowa daga cikin kwalbar jingina wayar tayi ajikin drowa ta yo kan nabila suka shiga kiciniyar kokawa,Allah ya baiwa Aazeem sa,a ta kwace kwalbar ta watsa mata abin cikin kwalbar a fuska kan wani lokaci tini fuskar nabila ta kwakkwabe wata uwar Kara Aazeem ta saka hakan ya janyo hankalin jama,ar gidan dai dai lokacin deedat ya shigo gidan har dashi aka kutsa dakin har yanzu Nurat bata farka ba.

Salatin jama,a ne ya farkar da ita idanunta akan nabila wadda bazata iya tantancewa da wacece itaba,da gudu cikin firgici ta mike zata kwasa da gudu da sauri deedat ya riketa ajikinsa ,itakam Aazeem sai yanzu ta tabbatar da cewar wannan din shi ake Kira da asid jikinta ya hau bari yau ga Aazeem na ihun kuka su Salim tini sun saka nabila a mota zuwa asibiti.

Cikin kuka take gaya musu yadda abin ya faru. ba kowa ne ya gamsuba tini yansanda sunyima gidan dirar mikiya suka tisa keyarta zuwa police station .

Aranar iyayen nabila suka karaso kano sunci kuka kamar ransu zai fita nabila kwance an nade fuskarta da bandeji kaf sun juye laifin akan  Nurat da deedat .

“Wallahi dad ko shine karuna sabida kudi sai inda karfina ya kare,daman wannan abin shiryashi akayi duk da anci amanar ta an yi mata kishiya amunafurce haka bai isaba sai an nakasata,wallahi sai na rama,bazamu yaddaba.

“Gaskiya ka fada nazifi wannan a zaune take.

Deedat ne ya shigo dakin tare da Nurat ,gai dasu yayi babu Wanda ya tanka masa sai mahaifin nabila ne yayi karfin halin amsawa har yana tambayar ba,asi ya zaiyya ne masa iya abinda ya sani a cikin maganar suka fahimci Nurat ce amaryar tasa.

“Munafuka kukanme kikeyi bacin kunriga kun cutar Mana da yarinya.

Nazifi ne yayi kanta wani irin fincika yayi mata zai fara duka,wani irin shaka deedat ya kai masa har sai da yaji kamar zai bar duniyar kan wani lokaci dakin ya cika da mutane aka ja nazifi waje Nurat ta kamkame deedat tana gursheken kuka gaba daya ta gama tsorata.

a police station Aazeem ce keta faman kuka tana faman rantse rantse .

“gwarama ki adana kalamenki koni mahaifiyar ki bazan amince dake ba ballantana yansanda.

“Ammina na tuba nasani na bata Miki dayawa,amman Kuma kinsani karya ba al,adata bace na kan bayyana gaskiyata ko da me zai faru.

Ammi ta dinga share kwallah tana sheshsheka tausayinta ya sake kama Aazeem.

shin yaushene zata haifawa amminta farin ciki bata taba hutawa agun mijintaba haka agurintama bata hutaba wani kaunarta ya dinga tsarga mata wayarta ta tuna take ta godema Allah  ta shiga yiwa yansanda bayani ammi ce ta koma gida dan dauko handset din.

<< Kyautar Zuciya 32Kyautar Zuciya 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×