Skip to content
Part 13 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, cike da kalubale da kuma nasarori, zuwa lokacin Asiya ta amince za ta rayu ta tare da zanen kaddararta, wanda ta tabbatarwa kanta ba za ta iya goge shi ba, shi ya sa ta koyi yadda za ta rayu da shi.

Ta mayar da hankalinta wajen gina rayuwarta, hade da kokarin ganin ta yi achieving din abin da ta sa gaba.

Duk yadda Asiya ta rika kokarin kare kanta daga daukar ciki, sai da Allah ya nuna mata komai a hannunsa yake, shi ke bayar a lokacin da ya so, ya kuma hana a lokacin da ya so.

Haidar na da shekara biyu da yan watanni Allah Ya ba ta ciki, cikin da ya jefa ahlin cikin fargaba.

Tsoronsu kar a kara samun irin Haider, duk da likita na has basu tabbaccin Sha Allah a wannan karon ba za a samu matsalar komai ba, amma kullum jininsu a kan kumba yake.

Asiya ta fi kowa shiga damuwa, ita kadai ta san yadda take ji game da Haider, bare ace ta kara aje wani yaron mai lalura kuma, shi ya sa tun farko taso cire cikin, Hassan ya hado ta da Hajja, da kyar Hajja ta lallabata ta bar shi, sai dai ta ce idan har ta haifi yaron da irin cutar Haidar ba za ta sake haihuwa ba. Ita kanta Hajja ta amince da hakan, saboda Hausawa sun ce da haihuwar yuyu, gara daya kwakkwara.

Yau Juma’a ba ta je aiki ba, saboda hutun da ta dauka, cikinta ya yi girma sosai, a ko wane lokaci za ta iya haihuwa.

Yau Juma’a da Jamila za ta wuce school ne ta kawo mata Haidar ya yi mata weekend, shi din dan gidan Adda da Hajjah ne. Yawo kawai ke kawo shi wurin Asiya ko idan ta je can ta gan shi.

Yanzu kam ya yi baki saboda ya tasar ma shekara uku, tuni ma aka sanyashi a makaranta.

A makaranta an fadawa malamansu matsalarshi, shi ya sa ake ba shi kulawa ta musamman, hade da lura da yadda yake mu’amala da yara.

Wannan abun shi kadai idan Asiya ta tuna sai ta ji wani irin daci, ace Haidar karamin yaro da bai san komai ba, amma an jefa rayuwarsa cikin hatsari, ta yadda wasa ma sai an iyakance mishi yadda zai yi shi.

Shi ya sa ta so cire cikinta Hajjah ta hana, amma ta za ta rika haifar yara da mummunar cuta, fatan Allah Ya sa wannan karon ta haifi lafiyayyen yaro ko yarinya, kullum wannan ce addu’arta.

“Momy me kike yi?” ta yi saurin mayar da hankalinta kan tambayar da ya yi mata karo na ba adadi

“Mele.” ta amshi lokaci daya kuma tana tsame naman da ke cikin kasko, saboda ta gaji da fada mishi nama take soya, idan akwai abin da ba ta iya jurewa, shi ne yawan tambayoyin Haidar.

“Mele kike yi?” ta daga kai alamar eh,.

“Zan ci to”

“To jira in gama.” ta daure a wannan karon ta amsa mishi.

“To” ya fada daidai yana fita kitchen din.

Fitar shi kuma ta yi daidai da shigowar Hassan.

Da gudu ya tare sa, sama ya daga shi kafin daga bisani ya yi kissing din kumatunshi yana tambayar shi “Ina Momy”

“Tana kitchen” Haidar ya ba shi amsa

“Yar budurwataaa, yar budurwataaa, yar budurwataaa Asiya sonki yay nisa a zuciya” Hassan ya shiga kitchen din da baitin wakar fuskarsa dauke da murmushi.

Asiya ma murmushin take yi, cike da nishadi lokaci daya kuma ta harde hannayenta tana sauraron yadda yake ci gaba da rera wakar.

“Ko cikin birni aka bincika za a sha fama…

Ka’idoji su duka kin cika tun da kin girma…

Ko a tarihi aka waiwaya sunanki na nan ma…

” Ta daban ce ke Asiya zan kula ki kamar marainiya. “

Yana kaiwa karshen baitin ta hada hannayenta du biyu alamar tafi, yayin da ta dora da na ta baitin wakar

“Kai ne farin cikina, kuma hasken idona, a zamanmu ni da kai jagorana ba ka batan rai”

Ya amshe da “an ce ruwan zuma ce soyayya, na ji na gamsu.

Sanyin da ke ciki ba shi da illa kamar ruwan randa.

Ra’ayin Fulani ne tallar nono wadansu kuma ganda.

Nau ra’ayin a soyayya ke ce na saka ki a rai.”

Cikin murmushi ta ce “komai na mallaka kai zan baiwa ba ni jin kyashi

In har na ganka ko ina jin yunwa sai in ji na ƙoshi.

Ka zan farin ciki bacin raina kai ke kau da shi.

Kai za ni lallaba in ma ka wasa irin na jarirai .”

Hassan ya hade hannayensa du biyun ya shiga tafawa Raf-Raf.
Haidar ma da bai san me ake nufi ba, ya shiga tafa hannuwansa kamar yadda ya Abbanshi die na yi.

Duk suka fashe da dariya cikin nishadi.

Idan akwai abin yake so bai wuce ya ga Asiya cikin farin ciki ba, sai ya ji kamar ranar sallahr shi.

Shi ya sa yake sadaukar da kanshi ganin ya nemo abin da duk zai faranta mata rai.

Cinyar kaza ta mika mishi, “ga tukuici.” cikin dariyar da ke nuna zallar farin cikin da take ciki ta yi maganar.

“Mele ne Dady? ” Haidar ya fada hade da kallon Hassan da ya lumshe ido yana yagar naman.

“Nama ne”

“Karya ne mele ne” Haidar ya kuma fada yana kallon Hassan.

Asiya da ta fahimci inda zancen ya dosa duk yadda ta so boye dariyarta ta kasa, dole ta dan dara kadan, kafin daga bisani ta kalli Haidar tare da fadin

“Zo Babana. Ba kyau ace wa babba yana karya ka ji, kar ka sake fadar haka.”

Kai ya daga alamar gamsuwa kafin ya ce “Ai mele ne ko?”

“Nama ne.” cikin dariya Asiya ta ba shi amsa.

“Me ye mele kuma wai?” Hassan ya tambaya yana kallon ta.

Dariya suka kuma yi gabadaya bayan Asiya ta ba Hassan labarin abin da ya faru tsakaninta da Haidar.

Hassan ya juya rike da hannun Haidar yana fadin “Bari mu je mu yi shirin masallaci.”

Cikin shadda fara tas dinkin jamfa iri daya suka fita shi da Haidar.

Sosai suka yi kyau, hakan ya sa Asiya ta rika kashe su da hotuna kafin su tafi masallacin.

Bayan tafiyarsu ne ta rika kallon hotunan da ta yi musu

A ko wane lokaci idan ta kallesu sai ta ji ina ma ace lafiya kalau suke basa dauke da wata cuta, lallai da sai farin ciki da nishadinsu ya wuce haka.

Ta dauki wannan a matsayin kaddararsu, tabbas Allah ne ya jarabcesu da hakan don ya gwada imaninsu, za ta ci gaba da yi mishi godiya a ko wane irin yanayi ko hali take ciki.

Suna cin mai kyau, suna shan mai kyau, Allah ya basu ilmi da take amfana da shi, ga muhalli ya hore masu, tana da Yan’uwan da basa son bacin ranta, suna ba ta duk wata gudunmuwa a rayuwa.

Bai kamata ta tayar da hankalinta don wannan cutar ba, cutar da ba ta hanata komai na rayuwar yau da kullum ba.

Wasu kuwa suna asibiti kwance sai an tayar sai an kwantar, wasu kuma basu da abin da zasu ci, wasu mahalli suka rasa, kowa da irin jarabawar da yake fuskanta a cikin duniya.

Hakan na daya daga cikin abin da ya sa ta daina daga hankalinta, kullum take godewa Allah, take kokarin mantawa da duk wata damuwa.

Kuma Alhamdulillahi, abin da za ta iya fada kenan, tana samun ci gaba a wajen aikinta, mijinta kasuwancinshi kara habaka yake yi, ga kuma wata baiwar cikin da Allah ya basu, wacce likita ya tabbatar mata sha Allah lafiyayyen yaro ko yarinya za ta haifa, ita ma addu’arta kenan kullum Allah ya sa a wannan karon ta haifi yaro ko yarinya lafiyayye.

Ta kai karshen tunaninta hade mikewa zuwa toilet don yin wanka.

Cikin doguwar rigar material ta shirya mara nauyi, wannan ya cikinta damar sakewa.

Ba wata kwalliya ta yi ba, turare kawai ta fesa, sannan ta jera abincin a kan dinning ta zauna jiran Hassan.

Kamar yadda likita ya ba su lokacin da yake ganin ya dace a yi mata CS, lokacin yana cika suka shirya duk abin da ake bukata zuwa asibitin, ba hankalin Asiya ne kawai a tashe ba, hankalin duk wani makusancinta a tashe yake, ga fargaba abin da ka iya zuwa ya dawo, duk da likitan na kwantar musu da hankali a kan sha Allah ba za a samu matsala ba.

Haka aka shigar da ita dakin tiyatar cike da zullumi.

Su Adda ma haka suka zauna cikin zullumi bakunansu dauke da addu’ar samun nasara aikin da za a yi.

Lokacin da aka fito da ita, gabadayansu suka nufi likitocin hade da tambayarsu fatan dai babu matsala.

Likitan ya tabbatar musu Asiya dai tana lafiya, yarinyar ma lafiya kalau take a zahiri, Sai dai zasu yi mata gwajin H.I. V zuwa gobe Idan Allah Ya kai rai.

Asiya ma lokacin da ta dawo hankalinta, abu na farko da ta bukata shi ne, mai ta haifa, sannan kuma me ye sakamakon gkwajin da aka yi wa Babyn.

Ba ita kadai ba, duk wani makusancinta abin da yake jira kenan.

Cikin sigar kwantar da hankali suka fada mata likitan ya ce sai zuwa gobe zasu ji komai.

Aunty Maimuna ce ta zauna da ita a asibitin, yayin da su Adda suka koma gida.

Wanshekare misalin karfe goma asibitin ya kuma cika, a lokacin tuni Aunty Maimuna ta taimakawa Asiya wajen gyare jikinta, Baby kuma an shirya ta Cikin overall light blue masu taushi, an nadeta cikin farin towel.

Bayan gaishe-gaishe suka shiga hirar yau da kullum.

Asiya dai jin su kawai take, saboda a lokacin da za a auna jininta ya hau ya fi dari bakwai.

Tana son Haidar sosai amma kamar tausayinsa ya fi sonshi yawa a zuciyarta, wannan yarinyar wata irin kaunarta take ji a jininta hade da tausayinta musamman Idan ya kasance tana dauke da cutar. Ita mace ta fi fuskantar kalubale a irin wannan gabar fiye da namiji.

Lokacin da Hassan ya turo kofar ya shigo, duk sai suka zuba mishi idanu, da alama kuma Sai lokacin ne suka tuna ashe fa cikin tsaka mai wuya suke, dukkansu babu wanda ya iya bude baki ya tambayi akwai matsala ko babu, sai shi da kansa ne ya ce

“Alhamdulillahi! Yarinyar ba ta da wata cuta.” ya fada fuskarsa dauke da zallar farin ciki, lokaci daya kuma ya zubawa kyakkyawar yarinyar tasu ido da ke kwance a kan gadon Baby.

“Alhamdulillahi!” duk suka fada cike da farin ciki.

Asiya kam har hawayen murna ta zubar.

Take dakin ya yamutse da hayaniyarsu.

“Amma fa likitan ya ce kar a, ba ta nono, kawai a ci gaba da ba ta madara.”
Ya katse hayaniyar tasu.

“Ba damuwa Allah ya raya mana ita cikin koshin lafiya” Aunty Maimuna ta fada cikin zallar farin ciki

“Amin.” duk suka fada

Bayan kwanaki uku aka sallami Asiya, ba ta yi wani taron suna ba, saboda ba ta da cikakkiyar lafiya, a masallaci aka radawa yarinya suna inda aka yi wa Aunty Zee takwara kamar yadda ta bukata.

Madarar jarirai masu kyau Hassan ya yo odarsu daga waje, kasancewar yanzu kasuwanci akwai sauki ko me kake son saye za ka iya saye daga ko wace kasa da wayar hannunka

Wata irin kulawa ta musamman Asiya ke ba Zee, kamar an fada mata da zarar ta kuskure a kulawa da ita za ta rasa ta.

Sai da ta yi wata uku sannan ta koma wajen aiki, kamar yadda ta rika rainon Haidar haka ta yi na Zee, za ta biya ta aje wa Adda ita, ita kuma ta wuce.
*******

Yau sunday misalin karfe 12 na rana ta iso gidan da zummar aje Zee, ita kuma ta wuce wurin aiki, kasancewar ranar Sunday ne gidan a cike yake da iyalan gidan kowa yana harkarsa.

Bayan ta yi shirin tafiya ne Haidar ya saka rigima sai ta tafi da shi.

Hajjah ce ta sanya baki dole ta tasa shi gaba suka tafi.

Ba ta taba zuwa da Haidar wurin aiki ba, shi ya sa yau da ya je kowa dokin ganinsa yake, idan wannan ya ja shi can wannan ya ja shi can.

Misalin shidda saura ta fito reception tana neman Haidar don tafiya gida.

Tana wurin a tsaye suna magana da Aliyu Shamaki sai ga Haidar din tare da Musa Dan’iya.

Ta mayar da hankalinta kansu fuskarta dauke da murmushi.

Haidar da ke tsalle ya karaso wajenta hade da rungume kafafunta.

“Yaron nan ya yi saurin girma, ga wayo, abin da ya fi burgeni da shi shi ne kansa na ja tamkar dai naki.” fadin musa Dan’iya lokacin da yake mikawa Aliyu hannu.

Murmushi Asiya ta kuma yi kafin ta ce “Kila don ba kwa ganinsa ne, amma ni kam kullum dai gani nake yadda yake haka yake.”

Aliyu da Musa suka yi dariya a tare

“Kina nufin yanzu tun da kika haifesa haka yake?” Aliyu ya yi tambayar cikin zolaya.

Ita ma dariya ta yi “Ban da wannan.”
Duk suka kuma yin dariya a tare.

“Don Allah ki rika kawo mana shi, yana debe mana kewa.” cewar Musa daidai lokacin da yake mikawa Haidar farar karamar ledar da ke hannunsa.

Sai da ya duka sannan ya karba hade da cewa “Thank you!”

“Ji ba kunya kuwa ya karbe”
Asiya ta fada rike da haba tana kallon Haidar.

Shi ma ita yake kallo bayan ya narke fuska kamar zai yi kuka.

“Sorry my friend, kar ka yi kuka ko, kyale momy.” fadin Musa hade da tattaba kafadar Haidar.

Godiya Asiya ta yi hade da kama hannun Haidar suka fice

A cikin Napep ya fito mata da kudin da ya samu.

Ido ta zaro tare da fadin “Duk waye ya ba ka wannan?”

“Duk mutane. Momy sai ki sayi mota ke ma irin ta Hajjah ki daina zuwa aiki a kasa.”

Murmushi ta yi yayin da wani dadi mara misultuwa ya darsu a can kasar zuciyarta,, kaunar yaron ta kara kama ta gami da tausayin sa.

Ko wane lokaci idan ta kalle shi ta tuna lalurarsa wacce sune sanadinta sai tausayinsa ya kamata, wani lokaci ma har hawaye take zubarwa.

A hankali ta manna shi a jikinta “Na gode Haidar,, ina rokon Allah ya ba ka lafiya ya yaye ma wannan cutar”

Da sauri ya dago kai “Momy ba ni da lafiya ne?”

“Eh.” ta fada hade da jijjiga kai.

“Me ya same ni?”

“Ba kana yin sallah ba kullum?”

“Eh.”

“To ka rika yin addu’ar Allah ya bamu lafiya. Muma bamu da ita ni da babanka. Amma Zee lafiyarta kalau.”

Kafin ya ba ta amsa keken ya tsaya, da kuma suka shiga gida wasanni da yaran gidan ke yi a filin wasa sai ya dauke masa hankali ya mantar da shi waccan hirar.

Yau kai tsaye bangarensu ta nufa, saboda tun a waje yara suka fada mata Addah ba ta nan, ta san Zee tana wurin Hajjah.

Hajjah goye da Zee tana zagaye falo da ita, da alama so take ta yi bacci.

Sallamar Asiyar kuma ya sa ta saurin dago kai hade da kokarin sakkowa.

“Hajjah yau Zeeta tana more bayanki kenan.” Asiya ta fada cikin zolaya daidai tana zama a kan kujera hade da zare mayafinta.

“Sai yau ne ta fara morewa? Yau rikici take ji, tun da kika tafi ta hanamu sakat, sai in kunna radio in kanga mata idan kina magana kuma sai ta yi shiru.” Hajjah ta yi maganar lokacin da take sauke Zee hade da mikawa Asiya ita.

Sosai Asiya ke dariya lokacin da take daga Zee tare da manna mata kiss a goshinta.

Wangale baki ta yi hakoranta sirara guda biyu suka bayyana.

“Ina Yarona? ” Hajja ta tambaya.

“Yana wajen Kawunansa da Antinayensa”

“Ga garin kununki can Jamila ta amso dazu.”

“Kai amma na ji dadi, har ta hada min garin, shekaranjiya fa na fada mata.”

“Ga shi nan ma an kawo. Babanki za a kara mishi girma next week dazu yake fada min.”

Asiya ta yi saurin zabura “Kai ma sha Allah, gaskiya na yi farin ciki, Allah ya tabbatar da alkairi. Amma shi ne ni bai fada min ba Hajja, ko dazu fa mun yi waya.”cike da shagwaba ta yi maganar.

“Kila ya manta. “cewar Hajjah tana dan murmushi

“Ke dai yake son ki fara sani Hajjah”

Ta fadada dariyarta hade da fadin “Bai yi laifi ba ai.”

Asiya ma ta yi dariya tare da fadin “To Allah ya sanya ailkairi.”

“Amin. “

“Bari in tashi Hajjah Ina da aiki a gida, ga kudin Haidar da ya samo a wurin yawonsa.”

“Duk wannan a can ya samo, lallai gobe ma sai a koma.”

Tare suka yi dariya, lokaci daya kuma Asiya ta dauki Zee da take ta wasa a kasa.

“A ba ni garin kunun”

Cikin minti daya Hajjah ta shiga kitchen ta fito rike da bokitin garin tana fadin “Tunkiya zan sayawa yaron nan da kudin nan”

“Uhhhh! Ka ji tunanin irin na tsaffi.” cikin dariya Asiya ta yi maganar.

Hajjah ma dariya ta yi tare da mika mata bokitin.

Sallama Asiya ta yi mata ta fice saboda tana son zuwa gida ta yi girki.

Misalin karfe tara saura na dare, zaune take a gefen gado jikinta sanye da kayan bacci masu ruwan hoda, riga ce mai ƙaramin hannu sakakke, sai wandonta da ya tsaya mata iya gwiwa.

Kokawar ba Zee magani take yi, amma fir taki sai ma kuka da take ta tsala wa. Duk ta gajiyarta da ita.

Tun da ya shigo yake jin sautin kukan nata, dalilin da ya sanya shi yin sauri kenan ya fado dakin.

amsarta ya yi bayan ya aje ledojin da ke hannunsa.

“Me kike mata ne wai haka?” Ya yi tambayar daidai yana jujjuya Zee din hade da kallonta.

“Paracetamol ne fa nake ba ta, jikin nata ne na ji da dan zafi, dazu ne ta yi rikici a wurin su Hajja, ina tunanin shi ne ya kawo zazzabin, kasan kuma sam ba ta son magani, idan za a ba ta sai an kwashi yan kallo” .

“Ke fa karfi kike gwada mata, ta ya ba za ta yi kuka ba?”

“Kai jama’a!” Asiya ta fada hade da rike haba.

“To karya na yi, kin bi duk kin danne yarinya. Ina maganin?”

“Ga shi.” ta mika masa.

A gefen gadon shi ma ya zauna, bayan ya umarci Asiya ta dubo mishi droper da ake ba Zee magani.

Sai da ta kara daurayewa sannan ta mika masa.

A nutse ya matsi daidai yadda ake bukata ya kuma matsa shi a bakin Zee.

Take kuwa ta canja fuska hade da kakarin amai, ruwan da ke gefe ya rika tabawa yana shafa mata a fuska har ta dawo cikin natsuwarta, amma hakan bai hana ta tsalewa da kuka ba.

Jijjigata ya shiga yi bayan ya mike tsaye har bacci ya dauketa, sannan ya kwantar da ita a hankali.

A lokacin tuni Asiya ta kawar da abin da ya shigo da shi, ta kawo mishi abinci.

Yana cin abincin lokaci daya kuma suna taba hira.

“kin san me?”

“A’a.” ta ba shi amsa daga kwanciyar rigingine da take.

“Kwanaki can bana taba fada miki akwai wani abokina da muka zauna daki daya lokacin service ba, kuma har muna shearing abu tare.”

“Eh.” Asiya ta fada hade da tashi zaune tana kallonsa.

“Shi ne ya kira ni dazu wai zai zo wani gari nan kusa damu, don haka zai biyo ta nan mu gaisa.”

“Tooo!” abin da Asiya ta fada kenan hade da kallon sa.

“Ya ce in samar mishi hotel mai kyau kafin ya iso.”

“Hotel kuma, duk dakunan gidan nan Rabin Raina.”

“To haka ya ce.” ya ba ta, amsa, hankalinsa a kan cin abincinsa.

“Zai yi matukar farin ciki ka sauke shi a nan, ba ni da wata matsala Idan har ka yarda da nagartarshi.” ta fada lokacin da take ta shi zaune.

“Ba shi da wata matsala mutum ne managarci, ga addinin, amma mutane su kan canja wani lokacin.”

“Haka ne kam, amma zamu sauke shi a nan for the first time”

“Yadda kike so.” ya yi maganar lokacin da yake goge hannunshi da tissue.

“Albishirinki! “
“goro” ta fada hankalinta kaf a kansa, ganin haka ya sa ya ce

“Guest what?”

Shiru ta danyi hade da juya idanunta alamun nazari sannan ta ce

“I don’t know. Ban gano komai ba.”

“Na cika kudin motar nan, za a kawo ta cikin satin nan”

“Kar fa ka sanya ni rawa Rabin Raina.”

Dariya ya yi sosai kafin ya ce “Ta shi ki taka, wallahi
da gaske nake yi.”

Kafin ya rufe baki ta diro daga bisa gadon ta fara taka rawa, yayin da shi kuma yake tuntsira dariya, farin ciki da son Asiyar ya cika mishi kalbinsa.

Yana daya daga cikin abin da ke kara masa soyayyar matar tasa a zuciyarsa yadda take sanya shi nishadi.

Hannunta ya riko yana fadin “Zauna haka nan mana kar ki gajiyar min da kanki.”

“Ba zan gaji ba, ni ma zan fara zama gaban mota ta ya zan gaji?” ta karasa maganar lokacin da take zama a gefen gado cikin dariya.

“Kuma sai kin fi ko wace mace kyau da gaban mota fa.”

“Allah ya soka daga ni sai kai ne sauran matan duniya basu ji ba.”

“Da sun ji fa?”

“Da sun yi ma zanga-zanga”

Dariya ya yi daidai lokacin da yake shigewa toilet don watsa ruwa.

Addu’a ta tofe Zee da ita hade da sake mata net.

Sannan ta kwashe kayan da ya ci abinci ta kai kitchen.

Boxer da vest ya sanya hade da shafa turare mai sanyin kamshi.

Ya san hancin matarsa, tana son kamshi sosai shi ya sa yake kiyayewa, baya taba rabuwa da turarruka masu kamshi.

Sai da ya kuma tofe Zee da addu’a sannan shi ma ya lumshe ido ya fara karanto ta shi.

A ko wane lokaci ya kasance da Asiya ya kan ji kamar a ranar aka daura masu aure, a kullum kara jin kaunarta yake yi, musamman idan ya kalli taurarinsa guda biyu Haidar da Zainab sai ya ji babu wani abu da zai yi mata ya saka mata.

Addu’arsa kullum Allah ya wadatasu da lafiya ya azurtasu ya rabasu da dukkan wani abun ki.

<< Labarin Asiya 12Labarin Asiya 14 >>

1 thought on “Labarin Asiya 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.