Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Labarinmu by Ammin Sameer

GARGADI 

Ban yarda wani ko wata su yi amfani da wani sashi daga cikin wanan littafi ba ba tare da izinina ba. Yin hakan kuskure ne mai girma.

NOTE   

Wanan labarin ƙirƙirare ne. Idan kun ga yayi kama da wani sashe na rayuwarku, to akan rashin sani ne.

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

In the name of Allah the Most Gracious the Most Merciful

Littafi Na Daya

Babi Na Daya

Wani baban daƙin taro ne wanda aka yi shi domin dalibai, domin duk sanda buƙatar taron ya tashi a yi shi a cikin makaranta. Private university ce, wacce wani shahararen ɗan kasuwa wanda ake ji da shi a faɗin duniya da kuma cikin ƙasar ta Nigeria, ya budewa yaron shi tun shekaru 4 da suka wuce, wanda wanan yaron sai a shekarar baya ne ya fara aiki a matsayin director a makarantar.

Dakin taron ya cika da dalibai wanda ya kasance za a yi quiz tsakanin makarantar gomnati da kuma private. Da ma su kan yi haka duk shekara, domin taimakon marasa ƙarfi wato dai duk shekara suna bada scholarship ga mutane uku kacal. Hakan ya sa suka gayaci manyan mutane, sanan kuma baban baƙo yakasan ce Dan Mai makarantar ne. Gaba ɗaya daliban sunƙosa Suga Wanda Zai lashe wanan gasa domin kuwa kowa yasan Dr. Shaheed ne wato director yashirya questions din sunsan Sai Mai tsananin Rabo ne Zai lashe wanan quiz din, daliban Suna zaune ne ata Baya yayin Da malaman Ke zaune a gaba, kowane malami Saida akayi mishi interview Mai tsauri Kamin yafara aeki a makarantar sabida haka indai kana son ingantacen karatu to kasaka Yaron ka a Makarantar.

Can saman dan dakalin kuwa wajen zaman wadanda za su karanto questions din da kuma daliban da zasu amsa, gurin yayi kyau sosai.

Professor Asma’u Sani ce zaune tana Tunani Allah yasa yaran data kawo zasuyi participating yanda yakamata, Domin kuwa Saida ta horasu kasan cewa itama tana Da nata makarantar amma kuma secondary ce sukuma su Aleya shekara daya Da Gama makaranta shine takeyi musu lesson, ganin yanda suke Da ƙokari yata Saka su amatsayin Yan private. Kamin ta sakosu, sanan tana zulimin ganin yaronta da Rabon ta dashi tun Yana Shekara Goma gashi yanzu shekarun Shi talatin, kozai karɓeta a matsayin uwa ohoo, cikin sauri tagoge hawayen Da suka gangaro ta miƙe ta fice takoma Dakin data ajiye yan matan, dazasu Yi participating quiz din, ganin sutayi su biyu, cikin damuwa tace “Ina Aleya? cikin damuwa hafsat tace “Bata ƙaraso ba inaga tana hanya Domin munyi magana Da ita tace zata zo”

Okay professor Asma’u tace tana mai komawa dakin taron.

A can waje kuwa motar director ce tashigo harabar makarantar sabida haka Sai kowa yakma kanshi masu tafiya hall natafiya masu lecture nashigawa classes din su, tuni mutane suka Fara cika wajen tayake sakamakon fitowa dayayi daga cikin mota ya dau wanka cikin suit brown colour da white long sleeve ya haɗe sosai gaisawa ya shiga yi da mutane cikin sauri domin shi baya son yawan magana, Amma kuma duk da haka saita suka tsayar dashi Kuma a kan hanyar wucewa hall din.

Aleya ce ta shigo cikin makarantar ta Saka light blue din Riga da Wando Na Pakistan ta yafa mayafin su hannuta riƙe Da littafai Da pencil, papers,and pen Wanda Bata Samu damar sasu acikin Jakarta Dake rataye a kafadar ta, jakar goyoce irinta gonjo Dinan wayarta Kawai tasake aciki. Sai surfa sauri takeyi tazo daidai inda Taron mutane Ke tsaye ta Duba taga Babu hanya saitashiga faɗin please give me way I want to pass Da haka aka Dunga matsa Mata tanazuwa inda director yake tace mishi “zata wuce” baima jitaba hakan yasa taraɓa zata wuce Sai Kawai ta bangaje Shi cikin sauri ya Dago Yana kalonta saidai cikin sauri tayi mishi weaving hannu alamar yayi hakuri, kalon long sleeve din nashi ganin harta Bata mishi Da lipstick dinta, tuni ta wuce Domin Bata Da Burin daya wuce taƙarasa ba’afara ba tana zuwa hall din tanufi inda professor Asma’u take ganin ta nufota yasata miƙewa ta ƙarasa tana faɗin “Aleya ya akayi kika makara ankusa farawa fa”

Cikin marainiyar murya Aleya tace “madam kinsan kuntafi kunbarni, Saida naje gidan ki Na ajiye Keke Na, sanan na Hau Mota ya kawo ni nan.”

Madam tace “okay muje Dakin dazaku shirya Sai kikuma ƙintsawa.”

Binta tayi tanuna Mata Ɗaƙin tadawo, tazauna. Bata jimaba saiga Shaheed yashigo, tuni kowaya Tashi itakuwa Tama ƙasa miƙewa, Bayan angama gaisawa dashine kowa yasamu ya zauna, Sai Madam Asma’u ta shiga leƙen Dan nata Wanda Shi kaɗai Allah ya Bata, a Ranta tana Mai tausayawa Kanta Da rayuwarta, batayi haune ba saitaji ana sanar Da zuwa masu quiz Hakan yasata saurin dagowa tana kalon su, sun shirya cikin Abaya brown kamar yanda ta tsara sunyi rolling din Dan kwalinta.

*****

Wani dan madaidaicin gida ne wanda ya kasance namasu ƙaramin ƙarfine. tundaga ƙofa nafar jiyo kamshi natashi, Hakan yasani ƙarasawa Da sauri ganin kanshin Meye wanna? kayan ƙwalam Da maƙula she ne ake soyawa, Momma Dake aikin suya tace “Bisma ki je kitaya Aleya shiryawa, kinga maneman ta zasuzo, Kuma kinsan auren haɗine, dole a buƙaci ganin ta” cikin ladabi Bisma tace “to” 

Bisma tanufi ɗakin su tana Shiga taga Babu kowa Hakan yasata Tunani Ko ta Na toilet Dan knocking din ƙofar tayi Jin shiru yasata ɓuɗewa wayam Babu kowa cikin Tashi hankali tajuyo takali Wani table Dake kusa Da window din Dakin Dake kalon gabas table ne tare Da kujera Na karatu saikuma litatafai Sai computer wato Dai laptop duk na Aleya ne tunda Bisma taga laptop din a rufe hankalin ta yayi masifar Tashi saita Kali Wani Dan ƙaramin Alo Dake mane a bangon kudu saitaga an rubuta “sorry sister Bisma”

Cikin Tashi hankali Bisma tafara ƙiran sunan ta Aleya!!! Aleya!! Aleya!! 

Shiru Babu ita Babu dalilinta kasa komawa kitchen din tayi wajen Momma Domin itadai batasan mezata ce Mata ba Zama tayi Kawai tafara Kuka Domin tasan kashinta ya bushe tunda Aleya tabar gidan nan cikin sauri ta dauko wayar ta tafara ƙiranta saidai Babu ƙiran data Daga hakan yasata hakura ta Koma suka cigaba Da aiki.

Baya sungama ne Bisma ta Koma Dakin ta Yi wanka ta shirya cikin atamfa doguwar Riga ta yafa mayafi Daga kai zuwa ƙirji Sai ta taje gashinta Bata daure ba ta bashi yafito ta ƙasan mayafin nata gashin nata iyakar Shi kafadar ta, tayi kyau.  

Tana fitowa palor din Taji Momma Na waya Da Babansu Yana faɗa Mata cewa Yana hanya su taɓatar cewa Aleya ta shirya don yasan halin rashin jinta dakuma kafiyar ta.

Momma tace “insha Allah bazatayi taurin kaiba aita canza”

Yace kekikasani Domin kuwa Dake ake haɗa baki take bujiremin Momma tace saika dawo takashe wayar Domin inda Sabo tasaba Da halin mijin nata, yacika zuciyya sanan Shi Duk abinda ya Aiyana tofa Babu fashi koyayi kobaiyiba Sai an aiwatar Kuma Dama iya ta kajo ceke zugashi Kuma take nuna mishi komai yayi daidai ne sabida shikadai ne ɗanta. 

Ita kuma Aleya irin yaran nan ne masu zuciyya Kamar Dai mahaifin ta Amma Kuma ita fa Duk inda gaskiya take tofa tana gurin Kuma ita bakinta Baya shiru Koda kuwa kasheta zakayi to saita fada Maka gaskiya Babu ruwanta Da tsufanka Ko ka haifeta.

Bisma ce ta ƙatse wa Momma Tunani dafaɗin “Momma Munshi uku Aleya tatafi quiz din nan, Da Madam Asma’u ta ce zasuje, Kuma saidana ce Mata kartaje, Amma ta saci hanya ta tafi”

Momma tadan daki goshin ta tana faɗin ya ubangiji ka shiryamin Aleya kakuma tsaremin ita Idan karatun nan Da take so Alkairi ne ya Allah ka Bata nidai nasan cewa kashin mu ya bushe Amma kicigaba Da ƙiranta kozata Daga Kamin su ƙaraso inaga zata dawo

*****

Guri yayi guri quiz yadau zafi Domin kuwa kowa yaga amsa tambayar Shi wato Dai an kamala amsa tambayoyi saura jiran sakamako yayin Daka ce sukoma gefe Domin Idan angama tantan cewa za’a ƙira wandan Da sukayi nasara Dama su shidda ne.

Komawa gefe sukayi Suna addu’a Allah yabasu nasara Bayan 20 minutes Sai Mai faɗin sakamako Dake tsaye agaban Wani Dan dogon table irin Na lecturer din nan yace” P.A.S team sune suka lashe wanan gasa zamuso mubawa sugabar tasu kautar girmamawa sanan zamubawa daya Daga cikin shaƙwaƙurar dalibar Taku”

Cikin tsananin farinciki Aleya takeyiwa Madam Asma’u inkiya ta Tashi ta ƙaraso, itakuwa Madam Asma’u takasa miƙewa Domin gaba daya Bata cikin yanayi yin haka Bata Gama tunanin ba Taji ance Dr. Shaheed ne zaibada kautar, Sai suka Fara faɗin “Muna gayatar Dr. Shaheed” 

Cikin Dan Jin haushi ya miƙe yana ɓata Rai Domin Yana Tashi yaji idon mutane a kanshi ƙarasawa yayi Saman dakalin aka bashi cup din Da Zai Bada.

Tasowa Madam Asma’u tayi ta haura Saman dakalin ta zo kusa dashi ya Kaleta nadan wasu Sakan Ni Domin ganita yakeyi kamar wanan muguwar matar Dad din Shi wace take Sashi yiwa kanshi alura Da dare sabida Baya iyabaci Ko kadan Sai yayiwa kanshi Alura Kuma Da hoton ta yake bacci.

Kawar Da kai yayi Yana ƙakalo murmushin dole yamiƙa Mata aka dauke su hoto saitaga ya matsa gefe sabida Jin Suna gogar kafaɗa Sai ta Matso yakuma matsawa , Bata ƙara takura Shi ba ta tsaya Sai Aka Kuma kawo mishi Wani kofin sanan aka ƙira “Aleya Saleem”

Cikin kin gasgata abinda Taji tace Anya Ni aka ƙira hafsat tace “kije mana kinsan Dai bajiranki za’a tsaya Yi ba ko?

Tafiya Aleya tayi ta ƙarasa tana ta murmushi Kamar ta sauce, Saida Shaheed ya Dan Kaleta Kamin ya taɓe baki itama yayi Mata murmushin dole akayi musu hoto Bayan ta karɓa ne tace “nagode yalabai”

Bai bi takanta ba yakoma ya zauna aka Bawa Madam Asma’u microphone akace tadanyi tsokaci. Cikin harshen Turan ci ta Fara Magana.

“Yarana yakamata ace kukasan ce masu yiwa iyaye uziri dakuma adalci, Ina nufi anturoku karatu ku dage domin ganin gun kai gaci yanda iyayen ku zasuyi algahari da ku karki kasance yara masu butulci ga iyayen ku”

Director kuwa wayar shi ya dauko yana dan yamutse fuska irin bada shidin nan akeyi ba.

Sai aka buƙaci Aleya tayi mana bayan ta ƙarɓi microphone din ne tace “zanfara da gaishe daku Nagaba Dani, sanan Sai dalibai Yan uwana saikuma wadan Da mukayi quiz din tare Basu Samu nasara ba Ina Mai Baku hakuri Amma fa Karki sare Domin nasan zaku iyayin fiyeda haka nan gaba, Sai Abu Na gaba dazan fada shine wanan nasarar Bata mubace ta uwar Dakin muce Kuma waje takasan ce Mai tausayi Da jinkan naƙasa Da ita mungode Madam Asma’u Allah ne kaɗai zaibiyaki”

Shaheed yadago yakali Aleya a karona farko a ranshi yace “wanan matar ce Mai tausayi gaskiya bansan cewa halinku daya ba Sai yanzu ta shafa muku muguta gaskiya Na tausaya muku”

Tashi akayi Daga Taron lokacin ƙarfe biyar da rabi Na Yama cikin sauri Aleya ta Koma Dakin dasuka sauka ta Mayayar Da kayanta ta dauko Jakarta wayarta ta dauko tana dan na screen din taga fourteen missed call Bata tsaya bin ƙiran ba ta riƙe wayar a hannu tayi ta zura sauran kayanta cikin Jakarta tafito suka shige wata doguwar Mota wace takasan ce ta makarantar, tareda Madam Asma’u suka wuce.

 Suna tafiya a hanya saiga ƙiran Bisma yashigo cikin sauri ta Daga, tana faɗin

“Yaruwa Muna hanya,Amma fa bamukusa ba Dan kinsan danisa”

Daga daya ɓangare Bisma tace “dangin su Suhail fasun zo Kuma Baba baisan baƙinan ba niyanzu Ina daki nayi pretending Kamar Ina tayaki shiryawa ne”

Aleya tace “insha Allah Kamin su gaji Zan dawo”

Kashe wayar Bisma tayi tana maiciga ba da Safa da Marwa adakin nasu.

Aleya kuwa Bayan Gama waya Da yaruwa ta ne Madam Asma’u tace “yadai Aleya? Ganin fuskarta dauke Da tsoro Duk Da kuwa Batada tsoro amma abinda take gudu shine dangin Suhail sutafi basu ganta ba.

Madam Asma’u harta buɗe baƙi zatakuma yin Magana suka Ji Mota ta tsaya cikin sauri tace MLM Yaya meke faruwa Sai yace “Taya CE tayi faci”

Fitowa sukayi kowa yanemi guri Domin Zama, Amma Banda Aleya Hakan ya Sa𝐧ya Madam Asma’u Kuma tambayar ta ko lpy.

Aleya tace “Baba Na Yana so ne yayimin aure Da Wani Dan masu ƙuɗi, sabida ance bazakayi komai ba Idan zaka auri Mai ƙuɗi, saidai ka kai yarka Kawai, shine fa yake son auramin Wani Suhail, yanzu iyayen shi sun zo tare da shi kuma baisan ni ba yau zai fara ganina.

Ammin Sameer (Miss SBS)

Titans of Talent (T.O.T)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.