Someday, you will get everything you deserve, and it will be beautiful
Shekara ta 2000
Kano...
“Aliyu!, Aliyu! Wai kana ina ne ?!”
Zaid ke ƙwalawa Aliyu kira, bayan da ya dawo gidansu bai tarar da shi a inda ya barshi ba, sanye yake da wannan uniform ɗin islamiyyar da ya rage musu.
Babu datti a jikin kayan, kasancewar ya na ɗaukowa ruwa a tuƙa ya musu wanki, sai haske da yadin kayan ya fara, alamun ya na jin jiki.
Hannunsa na dama riƙe da ledar ƙosan da ya samu ya siyo, bayan ya je ya yi. . .