Skip to content
Part 18 of 22 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

Do something for her that no one has ever done, love her for who she is.

Shekara ta 2000.

“Malam Ila ina kwana”

Cewar Zaid yana tsugunnawa har ƙasa, a sanda ya shigo shagon Malam Ila, wanda ke saida kayan provision a ‘yar ƙaramar containerrsa.

Baki washe Malam Ila ya amsa masa, kafin Zaid ya miƙe ya zauna a kan bencin da Malam Ilan ke kai, suka kuma gaisawa, kafin Malam Ilan ya ba shi abincin da ya siya ya aje masa, kamar yanda suka saba kullum.

Don a kwanakin kullum idan ya zo sai ya ba shi abinci, karɓa ya yi sannan ya ci, suna ‘yar hira jifa-jifa. Kuma a cikin hirar ne Malam Ilan ya sosawa Zaid inda ke masa ƙai-ƙayi.

“Ya kamata ka je ka dubo ƙanin naka, ka ga fa yau kusan satinsa ɗaya a can!”

Aliyu ya aje kwanon hannunsa sannan yace.

“Ai wai kar su ga gaggawata ne shi yasa, amma ina kewarsa, don ba mu taɓa nisa da juna irin haka ba… Tazarar awa ɗaya ne tsakanina da shi a haihuwa, kuma bayan wannan tazarar ba mu sake samun wata tazara ba… A ko da yaushe muna tare”

Cike da tausayawa Malam Ila ya girgiza kansa.

“Ka ga abun da za ayi shi ne; zuwa gobe sai muje mu duba shi ko?”

Cike da zumuɗu Zaid ya ɗagaa kafaɗarsa.

“Allah ya kaimu goben, na gode Malam Ila, Allah ya saka maka da alkairi…”

Washegari da sassafe Zaid ya dira a ƙofar shagon Malam Ila, ko fitowa ma bai yi ba, haka ya zauna ya na jiran fitowar Malam ilan.

Sanye yake da wani farin yadi, wanda Malam Ila da kansa ya bashi, don yace ba ya san ganinsa da wannan uniform ɗin. Kana ganin kayan za ka san cewa ba nasa ba ne, saboda yanda kayan ya masa yawa.

Ya na zaune a wurin har Malam Ila ya fito, babu yanda be yi da Malam Ila kan su wuce gidan marayun katsaye ba. Amma Malam Ilan ya dage kan sai ya sai masa abinci ya ci tukunna. Hakan kuwa aka yi, sai da ya sai masa abincin ya ci ya yi taf, sannan suka kama hanyar gidan marayun.

“Bawan Allah, Lafiya kuwa na ga kamar gidan marayun nan a kulle, kuma na… Na ga kamar ma gobara aka yi!”

Cewar Malam Ila a kiɗime, hankalinsa ya yi wata mummunar tashi, bayan da suka iso gidan marayun, suka ga gate ɗinsa a kulle, kuma ko daga bakin gate din za ka gane cewa an yi gobara a wurin.

Mutumin da Malam Ila ya tambaya ya kalle su.

“Kwana huɗu kenan da wuta ta kama a gidan, kuma babu wanda ya fita da ransa daga gidan!…”

Iyaka abinda Zaid ya iya fahimta kenan a zancen nasa, bai san sanda ya yanke jiki ya faɗi ba.

Kwanansa uku a asibiti kafin ya farfaɗo, kuma da ya tashi farfaɗowar ma ba a hayyacinsa ya farka ba. Abubuwa ya riƙa yi kamar wanda ya samu taɓun ƙwaƙwalwa, sai zantuka yake barkatai, an kasa gane kansa.

Ganin abun ba na ƙare ba ne ya sa Malam Ila ɗauke shi daga asibitin, don ya ga abun ba na asibiti ba ne. Tashin farko gidansa ya kai shi, amma matarsa tace fafur ba za ta karɓi tsinttaciyar mage ba.

“Wa to kai ga ka juju ko?, Ubn yaye-yaye, to Wallahi ba za ta saɓu ba!, a ina zan saka wannan gardin ƙaton?, A gida ɗaki ɗayan?, Ga ka, ga ni, ga ‘ya’yana, to Wallahi Malam da sake!”

“Haba Gambo, be kamata kike faɗin haka ba, yaron nan na faɗa miki cewar maraya ne, idan ba ki manta ba; babarsa ce ta ba ni kuɗin da na miki yankan sunan Audu…”

“Wallahi ba ka isa ba, wato dan kawai uwarsa ta ba ka kuɗi ka sai mana ragon suna, sai na karɓi ɗanta ko ?, na rantse maka da Allah wannan yaron ba zai zauna min a gida ba!”

Duk da Zaid ba ya hayyacinsa sosai, amma yana iya tuna yanda matar kewa mijinta masifa da bala’i, ya na iya tuna yanda ta haƙiƙance kan ba zai zauna da ita ba.

Tun bayan da ya fuskanci cewa Aliyun da ya rage masa ya bar duniya, rayuwarsa ta shiga halin ƙaƙa na ka yi. Ya ji gaba ɗaya ya gaji da duniyar, babu abun da ya fi buƙata sama da mutuwar shi ma, ya ji cewar yana son ya mutu kamar Momma da Aliyu, tun da da ma su ne kaɗai gareshi, to ga shi ya rabu da su, to ina zai sa kansa?.

Ba dan Malam Ila ya so ba, sai dan babu yanda zai iya, ya ɗauki Zaid ya mayar da shi gidansu na da, amma kullum sai ya kawo masa abinci da ruwan rubutun da yake karɓo masa a gun wani malami mai almajirai da yasa a yi masa, don ya temaka masa wurin dangana da halin da ya shiga ciki.

Safe, rana, dare, ba ya taɓa tsallakewa, har takai ga Zaid ɗin ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya, amma yanayinsa da ɗabi’unsa duka sun sauya, ba ya son yawan magana, ba ya son fita, ba ya son shiga jama’a. Ya koma rayuwar ƙunci. Ƙarshe ma ya yanke shawarar barin gidan.

Rana tsaka Malam Ila ya shigo gidan kawo masa abinci amma ya nemeshi sama ko ƙasa babu alamarsa. Ya ɓata ɓat! Kamar almara.

Ranar da ya gudu cikin garin kano kawai ya bazama, ya kwana a titi, kafin da safe ya ci gaba da yawatawa. Har Allah ya kawo shi rumfar wata inyamura me ƙosai, sunanta Ebere, tana da marainiyar yarinyarta Rhoda, da mijinta ya mutu ya bar mata.

Ganinta da Zaid na farko Allah ya saka mata tausayinsa, hakan yasa ta kira shi.

“Menene sunan ka ?”

Ta tambaya cikin gurɓattaciyar hausarta.

“Zaid”

Zaid ya amsa mata kansa a ƙasa.

“Kai maraya ne ?”

Sai ya girgiza kansa yana ɗaga kafaɗarsa ta dama.

“Ni maraya ne, ba ni da kowa”

Maman Rhoda ta waiga ta kalli ‘yarta Rhoda dake zaune a raufar ta na wasa.

“Za ka zauna da mu?”

Zaid ya ɗago da kansa ya kalli matar, sannan ya kalli ‘yarta, a take ya ga sun rikiɗa a idonsa sun koma masa Momma da Aliyu.

Ba jayyaya ta amince mata, a ranar tare suka wuni a rumfar saida ƙosan nata, bayan dare ya yi ta ɗauke shi da Rhoda ‘yarta suka tafi gidanta.

Gidan ba wani babba ba ne, amma nata ne, kuma mallakinta, ɗaki ɗaya ta bashi tace masa ya yi zamansa, daga yau shi ma ɗanta ne, kuma ba ta hana shi yin addininsa ba, zai iya ci gaba.

Tun daga wannan ranar Zaid ya yi sabin ahali, ga su dai ba musulmai ba, amma sun nuna masa karamci da hallacin da ya kamata a ce ‘yan uwansa musulmai ne suka nuna masa.

Maman Rhoda ta mayar da shi kamar babban ɗanta, Rhoda kuma ta ɗauke shi a matsayin wa, sai suka koma kamar ‘yan biyu, duk da shi Zaid ɗin ya fita shekaru, amma hatta da kaya iri ɗaya suke.

Maman Rhoda ta saka Zaid a makaranatar su Rhoda, sannan ta biya masa kuɗin shekarun da zai yi har ya gama makaranatar kamar yadda ta yi wa Rhodan ita ma, don tace akwai mutuwa, ba ta son ta mutu ta barsu cikin wani hali.

Kullum da safe Maman Rhoda za ta haɗa kayan ƙosanta. Kuma tare da su Zaid ɗin take tafiya, idan suka je suka aje mata kayanta a rumfar da ta saba yi, sai su wuce makaranta idan a cikin sati ne. Bayan sun taso kuma kai tsaye can rumfar tata za su wuce, ba su suke dawowa ba sai rana, idan sun dawo da rana za su zauna su huta, idan suna da wani aikin yi su yi, idan kuma ba su da shi sai su hau aikin haɗa ƙosan yamma.

Yamma na yi za su ƙara komawa, ba sa dawowa sai wajajen sha ɗaya, wani lokacin ma Rhoda tun a can take fara bacci, sai dai Zaid ya goyota su dawo gida.

Zaid ya sake da su sosai, ya na rayuwa cikin farin ciki, dan Maman Rhoda ba ta rage shi da komai ba, ko azumi ne zai zo tana ta ya shi yin hidindumun azimin, kuma duk sallah sai ta masa sabon ɗinki.

Kamar yanda take tafiya da shi can Enugu garinsu idan Christmas ta zo, kuma hatta da ‘yan uwanta na can ba sa nuna masa ƙyama, sannan ko da sau ɗaya ba ta taɓa masa tayin shiga addininsu ba, shi ma kuma bai taɓa musu ba, dan ya ga kamar idan ya musu ma bazasu karɓa ba.

Rayuwarsa ta ci gaba da wanzuwa a haka, cikin farin ciki da samun nasarori, kafin giftawar wata ƙaddara, wadda ta tarwatsa komai na rayuwarsu shi da Rhoda, ta yi fata-fata da jin daɗinsu!, Ƙaddarar ta hargitsa komai!.

Present day…

RABI’A POV.

Da sassafe ta farka kamar kullum, sai da ta yi sallah, sannan ta gyara alkama, ta kai niƙa, ta ɗauko niƙan, sannan ta haɗawa Habiba kayan suyar funkasonta kamar yanda ta saba.

Kana ta share gidan tas, sannan ta shiga wanka, a lokacin da ta fito har masu siyan funkaso sun fara taruwa a gidan, don Habiban da kanta take soyawa, tun da yau akwai makaranta.

Ɗakinsu ta shiga, ta saka kayanta, ta ɗan shafa mai, sannan ta yi wa Anti Saratu sallama, ta fita.

Yau ta yi mamaki sosai ganin har kusan kwana uku kenan ba ta ganin Mishal a makarantar, ita kuma ba ta santa da wata ƙawa ba bare ta tambayeta, wannan baturiyar ma da ta saba ganinsu tare ba ta san inda za ta sameta ba.

Hakan yasa tunanika sukai mata yawa, ta shiga saƙe-saƙe kala-kala, har zuwa lokacin da aka tashi. Kuma kamar yanda zuciyarta ta raya mata, kamar yanda ta saba ganinsa.

Tana fita idanuwanta suka sauƙa a kansa, jingine jikin gate ɗin estate ɗinsu, sanye cikin wasu ash jogger set. Hannayensa sanye cikin aljihun hoodie ɗin kayan, sai dai saɓanin kullum, yau ba shi kaɗai ba ne, shi da wannan budurwar ne, wadda ya kira da ƙanwarsa, sanye take ita ma cikin irin kayan jikinsa, hatta da takalmansu iri ɗaya ne.

Kamar yanda suka saba a kwannakin hannu ta ɗaga masa, hakan yasa Rhoda ta juya ta kalleshi, sannan ta kalli Rabi’an.

Bisa ga mamakinta sai ta ga Rajan ya sha mur, ya na bin bayan Rabi’a wadda ta fara tafiya, sai kawai ta yi murmushi ita ma ta bi bayansu.

“Me ya same ki yau ?”

Raja ya tambaya, ganin yanayinta ba kamar yanda ya saba ganin ba, Rabi’a ta ɗago ta kalleshi, sannan ta kalli Rhoda dake biye da su, ganin hakan yasa Rhodan ta ɗauke kanta sama tana fito, sannan ta ƙara da.

“Ni fa ba na jin komai…”

Raja ya tsaya, sannan ya waiga ya kalleta.

“Da ma biyoni kika yi ?”

Ta girgiza kanta.

“A’a fa, ni saƙo zan je na karɓo a nan bakin titi”

Raja ya finciko hannunta yana kama kanta ya matse, hakan yasa ta saki ƙara. Duk abun da suke Rabi tsaye a gefe tana kallonsu.

Sai kuma ya dafa Rhodan, sannan ya yi wa Rabi alama da su ci gaba da tafiya. Tafiyar suka ci gaba da yi, Raja na dafe da kafaɗar Rhoda. Ya ɗaga kafaɗarsa sannan yace.

“Baki amsa ni ba Ammata”

Ko kafin ta ba shi amsar Rhoda ta yi wuf tace.

“Ammata?, What a wonderful name!”

Raja ya kama kunnenta ya murɗe, hakan yasa ta saka ƙarar azaba.

“Raja mana!”

Ta faɗi a shagwaɓe.

“Ammata manta da wannan yarinyar, neman magana take”

Sai faɗan nasu ya bawa Rabi dariya.

“Kwana biyu kenan wata ƙanwata ba ta zo ba shi yasani a damuwa!”

“Gidan ku ɗaya ?”

Rhoda ta tamabaya daga ɗayan ɓarin, Raja ya ranƙwashi kanta daga sama, kasancewar ya fita tsayi. Ta dafe wurin tana turo baki. Rabi’a kuwa sai murmushi take.

“Ki kwantar da hankalinki Ammata, lafiya ita ce ke ɓuya, da yardar Allah tana cikin ƙoshin lafiya”

“Kawai ki manta”

“Rhoda hoo!”

Raja ya faɗi yana ƙara dukan kanta, ta ƙwace kanta, sannan ta koma layin da gudu, tana faɗin:

“Kada ki dumu Ammata! She dey fine oo!”

Daga Rajan har Rabi’a sai da suka yi dariya. Tafiya sukaci gaba da yi suna ‘yar hira, har suka iso bakin titi, kamar kullum haka y tsaidamata ta hau, har suka ƙulewa ganinsa ya na ɗaga mata hannu. Kamar daga sama ya ji muryar Rhoda daga bayansa.

“Hooo!, Raja ya kwarewa soyyayar me kama da shi…”

Juyawa ya yi ya kalleta, tsaye take a bayansa, kenan dawowa ta yi?.

“Ki bari na zo na sameki a nan”

Ya yi maganar yana nufar inda take. Rhoda ta fita da gudu tana dariya, shi ma ya bi bayanta yana dariyar, har ya cimmata, kafin ya riƙe kumatunta yana ja.

“Ke ba kya jin magana ko?”

Rhoda ta dafe wurin da ya ja mata tana kumburo baki.

“Ayya mana Zaid, wannan ai mugunta ce ”

“Ni ne mugun?”

Ya faɗi yana ƙoƙarin ƙara kamata. Ta kuma saka gudu tana dariya.

“I’m sorryyyyy!”

Ta faɗi tana kama kunnuwanta, a sanda ya kuma cimmata, sai ya dafata kamar ƙawarsa, suka jera suna tafiya. Har suka koma gidansu.

No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja.

“Assalamu Alaikum… Karima!”

Muryar Anna ta faɗi, yayin da wayarta ke kare a kunneta, bayan da ta aikawa Karima yayar Siyama kira. Daga cikin wayar muryar Karima ta amsa da.

“Wa Alaikumu Salamu, Na’am Anna, ya kike, ya gidan ?”

“Lafiya ƙalau Karima, ya Siyama da yaran, da kuma me gidanki ?”

“Suna lafiya”

“To da ma so nake dan Allah ki kira mijin naki ki sanar masa da cewar ina son ganinki, idan xai iya miki lamuni”

Karima ta ɗan yi jim, kafin ta amsa da:

“Ba damuwa, Insha-Allah zai bari, amma Lafiya kike nemana Anna ?”

Anna ta ɗan shafo gefen fuskarta, sannan tace.

“Lafiya… Ban faɗa muku ba ne, An ɗaurawa Kuliya aure, kuma yau za mu je mu ɗauko amaryar, su Laraba ma duk na kirasu, dan haka kema sai ko taho…”

Tsabar razanar da Karima ta yi sai da ta miƙe tsaye, hannunta kan ƙirjinta wanda ya shiga bugu da sauri.

“Aure kuma Anna!, Kuliyan ?!, Shi da wa ?!”

Sai da Anna ta ɗan yi shiru, kafin ta amsa mata da.

“Wannan ba huruminki ba ne, matar Aliyu kuma idan kin zo za ki ga ko wacece!…”

Daga haka ta sauƙe wayar. Ɗazu da safe Kuliya ya zo yace mata kawun su Abubakar yace tun da jiya aka yi bakwai ya zo ya ɗauki matarsa yau. Kuma su yake so su je su ɗaukota. Shi yasa ya zo ya sanar da ita.

A lokacin kallonsa kawai ta ci gaba da yi, ganin yanda ya rame, ya yi wani irin baƙi, kamar wanda ya tashi daga jinya. Kafin ta daure ta tambayeshi shirin da ya yi domin bikin.

Ya shaida mata da; babu wani abun da ya tanada, kawai a je a ɗauko amaryar, koma miye daga baya sai a yi, ba ta ƙara cewa komai ba, dan wata ƙila a ganinsa hakan ya masa, a irin halin da yake ciki ba ta jin za ta iya tirsasashi kan wani abu da baya so ba.

Daga can gidan Anti Karima, Siyama dake kan danning ta nufota a razane, jin ta ambaci aure da kuma suna Kuliyanta.

“Anti Karima wai menene?”

Cike da baƙin ciki da ƙunar zuci Anti Karima ta kalleta tace.

“Wai Kuliya aka ɗaurawa aure!”

Wani irin duka gaban Siyama ya yi, har ta ji kamar an daki zuciyarta da ƙarfin da aka saka a wuta, kamar da Anti Karuma ta watsa mata barkwano, zuciyarta ta shiga mata ɗaci, wanda ya zagayo har zuwa bakinta.

Kuliyanta ?, Kuliya ya yi aure?, wai me Anti Karima ke faɗi ne?, anya ma kuwa tana cikin hayyacinta? Inna! Ba za ta saɓu ba, wannan zancen ƙarya ne, Kuliya na ta ne ita kaɗai, wata mace ba ta isa ta rabata da shi ba, babu wanda ya isa ya shiga tsakaminta da shi.

Ba ta san ta fara hawaye ba, sai da Anti Karima ta dafata.

“Kada ki damu Siyama, ko wace shgiya ya aura za mu raba shi da ita, Kuliya naki ne ke kaɗai, dan haka ke kaɗai za ki same shi”

Kamar wadda ta bada ajiyar hankalinta haka ta kalli Anti Karima, hawaye na mata zuba.

“Anti Karima Wallahi ina sansa… Na rantse miki da Allah ina san Kuliya, na shiga uku ni Siyama! Yanzu wai Aliyuna ne ya yi aure?, Wayyo Allahna, Anti Karima… Anti Karima Ina sansa, I love him Anti Karima… I can’t live without him, I can’t, i can’t…”

Gaba ɗaya ta fita hayyacinta, sambatu kawai take tana ƙarawa. Anti Karima ta rungumeta tana bubbuga bayanta.

“Ba za mu rabu a su ba, dole sai mun rabasu!…”.

Haka Siyama ta ƙarar da yinin ranar kamar mara lafiya, kuka kam ta yi har ta gode Allah.

Sai da yamma Anti Karima ta shirya dan zuwa gidan Anna, amma sai wayar Annan ta risketa kan ta yi zamanta ba sai ta zo ba, Kuliya yace zai je ya ɗauko matarsa da kansa.

Tun daga lokacin ta riga ta tabbatarwa da kanta ba zata bar wannan auren ya ɗaure ba, sai ta ga bayan wannan auren, ta ko ta halin ƙa-ƙa.

<< Labarinsu 17Labarinsu 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×