No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja...
“Nemo min lambar Nimra”
Cewar Jadda wadda ke danƙawa Hajjara wayarta, Hajjara ta karɓa tana yatsina fuska, don Allah ya san,i ita Wallahi ta gaji da zama da wannan masiffafiyar tsohuwar, duk ta bi ta isheta, Allah-Allah take ta koma Maiduguri.
Zaune suke a falo, daga can gefe kuma Mama Ladi ce ke bawa Daala abinci.
“Ga shi. Ta shiga”
Ta ƙarashe tana miƙawa Jadda wayar, Jadda ta karɓa tana tsara kalar masifar da zatawa Nimran.
“Falmata! Tun muna sheda juna da ke ki saka wanan ɗan yankan. . .