Skip to content
Part 3 of 9 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

Idonta ya sauƙa a kan Daala dake ta zubar yawu, ita ma yarinyar Hajjaran take kallo. Tawarta ɗaya kenan a duniya, wannan yariyar da Allah yasa ta haifota a nakashe, kuma nakasar yariyar yasa ta gujeta, babu wani abu dake shiga tsakaninta da yariyar irin na uwa da ‘yarta, Mishal da Naani ɗin da Abubakar ya ɗauko su ne ke kula da yarinyar har wa yau.

Mishal na fita daga falon gidan BQ ta wuce, dan bata da wurin zama a gidan da ya wuce BQ ɗin, in baka sameta a BQ ba zaka sameta tare da Daala suna wasa, dan Allah ya ɗora mata ƙauna da tausayin yarinyar.

Ganin yanda Hajjara ke bagarar da lamarin yarinyar saboda nakasar dake tare da ita, ita kuma Allah ya hallici zuciyarta da wani irin tausayi, kuma tausayin ne ke sakawa bata da aminan hira a gidan sai masu aikin gidan.

A bakin ƙofar BQ ɗin ta tsaya, tana ƙare musu kallo. Mutum biyar ne zaune a kan bujukura. Ladi, wadda ita ce ke kula da Daala sai mijinta Malam Audu, wanda ke musu gadi, sannan Khalifa, ɗan Mama Ladin na farko, wanda shi ne yake musu sharar garden da ta compound da ma aike idan ya taso, sai Shatu ‘yar Mama Ladin ta biyu, sai autar Mama Ladin wato Ummul.

A taƙaice de duka ahalin Mama Ladin ne, waɗan da suka kasance ahalinta ita ma, dan bata da wurin zuwa da ya wucenasu, Shatu kuma ita ce wadda zata iya kira da ƙawarta, Mama Ladi ta zame mata uwa.

“Ah-ah, Hafsatu, ƙaraso mana”

Sai ta yi murmushi har ƙarafunan braces dake saman haƙwaranta na bayyana, tana ci gaba da kallonsu, su ma sai hadaniyar haɗa kayan shan ruwansu suke, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka ci gaba da takawa har zuwa kan bujukurar. Guri ta samu kusa da Shatu ta zauna.

“Yau kin yi azumi ?”

Mama Ladi ta tambaya, yayin da take juye tiyara a cikin wata doguwar roba, Mishal ta girgiza kanta.

“Ban yi ba”

“Haba uwata, sau nawa zan faɗa miki cewar kin isa azumi ?, bai kamata ace ki na shan azumu ba gaira ba dalili ba”

Cewar Malam Audu yana aje radion hannunsa.

“Rabu da ita Baba, ai kullum gaya muku nake cewar yarinyar nan raguwace, amma bakwa yarda” Cewar Khalifa.

Mishal ta turo baki gaba tana sosa kanta.

“Allah ni ba raguwa ba ce, a class ɗin Kungu fu ɗinmu fa kullum ni nake zuwa a farko, kuma watan da ya auce ma saida na karya wani malamin mu….”

Hannunta ta kai ta rufe bakinta, sakamakon suɓul da bakan da ta tuna cewar ta yi, dan tasan yanzu Mama Ladi za ta shiga mata faɗa.

“Kema kin san cewa ba dai-dai kika yi ba kenan, shi yasa kika rufe baki” Cewar Mama Ladin tana miƙawa Baba pure water.

Sai kuma ta sauƙe hannun nata.

“To ai shi ne ya min tsawa, kuma ya dake ni….”

“Ai haƙuri ake uwata, idan kika yi haƙuri sai labari, dan wata ƙila ma kina gama makarantar auren ki za ki yi”

Ido waje take duban Baba.

“Aure fa Baba ?, a’a ni ba wani aure da zan yi yanzu, nawa ma nake da har zan wani yi aure?”

Abinda bata sani ba shi ne, waɗanan kalaman nata zasu mai-maita kansa a cikin kanta kwanaki kaɗan masu zuwa, dan bata da masaniyar ƙaddarar da Allah ya hukunta za ta faru a ‘yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura, ta kuma zama silar ɓacin wasu.

A wurinsu ta zauna ta sha ruwa, har sanda su Baba suka fita Sallah, Sai da Mama Ladi ta mata jan ido a kan ta tashi ta je ta yi sallah, dan Allah ya sani, zuciya ɗaya take zaune da yarinyar, ganin ta ɗauketa kamar uwa, shi yasa ita ma ta ɗauketa kamar ‘ya.

Saboda rayuwar yarinyar tana buƙatar kulawar uwa, gashi ita kuma bata taso ta samu hakan ba.

Ko da ta koma cikin gidan ɗakinta ta wuce. Wani haɗɗaɗe kuma ƙawattacen ɗaki wanda aka cika shi da kayan buƙata irin na matasa dai-dai shekarunta. Komai na cikin ɗakin peach color ne, sannan ga tarin teddies a ko wata kusurwa ta ɗakin.

Lokarta ta buɗe, da ƙyar ta samu hijabin da ta saka, dan ba saka hijabai take ba, hatta da kayanta yawancinsu ƙananu ne, bata sakka kayan hausawa sam, a cewarta takura mata suke.

Bayan ta yi sallar ta fita falo, a lokacin Daala ce kaɗai, zaune kan kujrarta tana ta gwalantunta, bakinta sai zubar da yawu yake.

Zama ta yi kusa da ita, ta kunna musu tashar mbc 3, sannan ta shiga bata labarin da ita kanta tasan cewa Daalan ba fahimta take ba.

Hammad ne ya shigo falon ta ƙofar ɗakinsa,byana shigowa ya ɗauki remote control ya sauya tasha. A fusace Mishal ta yi kansa.

“Shge ubn baƙin hali, dan me zaka sauya mana tasha?, dan ka ga ban maka magana a kan munafurcin da ka min ɗazu ba ko?”

Ta ƙarashe tana ƙwace remote control ɗin tare da maida mbc 3n da suke kalla.

“Bar falon nan kafin na karya maka wuya”

Da gudu ya yi sama. Kuma bai tsaya ko ina ba sai a ɗakin Hajjara, wadda ke kwantar da Fahima a kan gado, sakamakon baccin da ta yi. Ƙarya da ƙarerayi ya sameta ya zayyana mata.

Kafin ita kuma ta bazamo ta sauƙo ƙasan ta samu Mishal ɗin tare da balbaleta da masifa, cikin ƙaraji da ɗaga murya take faɗan.

“Wai ke yarinyar nan me kike nufi ?, so kike mu fice mu bar miki gidan ko me ?, to wallahi baki isa ba, shi har gwara shi, tun da nan gidan ubnsa ne, ke kuma fa ?, sakabu fa kike, to wallahi ki fita idon yarana!……”

Ba komai Mishal ke fahimta cikin kalaman nata ba, sakamakon ciwonta da ya shiga ƙoƙarin tashi, dishi-dishi take ganin komai, numfashinta ya shiga ƙoƙarin ɗaukewa daga ƙirjinta, waccan ranar ta soma dawowa cikin kanfa.

_“Yau daga ni sai ke, kuma babu me ƙwatarki a hannu na!….”_

Abinda ya biyo bayan kalaman nasa sune ya zama silar shigarta cikin halin da take a yau.

Numfashinta ya ci gaba da yin sama, da ƙyar take iya janyo shi. Zuwa lokacin Hajjara ta tuna da ciwon nata, sai ta tsaya a gefe tana kallonta kawai, a ranta addu’a take, kan Allah yasa idan nunfashin nata ya yi sama kada ya dawo.

Mishal ta kai ƙasa tana dafe da wuyanta, sai neman iskar da za ta shaƙa ta ke, duk da sanyin acn dake falon sai gumi take, tuni idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, har hawaye ya fara sulalowa ta gefnsu, sai jan nunfashi take kamar me asthma.

Fatan Hajjara bai karɓu ba, dan a dai-dai lokacin da ta faɗi ƙasa gaba ɗaya, a lokacin ne ƙofar falon ta iyo ciki, alamun wani ne zai shigo, kuma bai fi tazarar sakan ɗaya ba, siffar Abubakar ta bayyana a cikin falon.

RABI POV.

Zaune take daga gefe a kan dakalin ƙofar ɗakinsu, yayin da Habiba da sauran yaranta ke zaune a kan tabarma suna kiciniyar shan ruwa.

Ba yau aka saba haka ba, kusan kullum hakan ake, a duk sanda za su taru irin haka, to ita za ka ganta daga can gefe tana kallonsu.

Amma yau ɗin ba kallonsu take ba, tunanine fal kanta, tunani take kan abinda ya faru ɗazu a makarantar da take aiki, abinda ya faru ɗazu tsakanin Malamar nan da yarinyar da ta kira kanta da Mishal.

Yanda yarinyar ta haƙiƙance kan ba za ta kwashe sharar ba, ita da ta mata magana, sai ta ganta a matsayin me sauƙin kai, ashe ba haka ba ne.

Dan da ƙyar ta samu ta tausheta, sannan ta haƙura ta tafi, kafin ita Rabin ta dawo kan malamar ta bata haƙuri, kana ta ci gaba da sharar da ta fara.

“Ni ban ga Abba ba”

Cewar Saratu, kuma maganar tata ce ta dawo da Rabi zahiri.

Habiba ta yi tsaki tana taɓe baki.

“Yana can yawon gantalinsa mana”

“Gaskiya Umma bakya kyautawa Wallahi, kullum ina faɗa miki cewar abinda kike bai dace ba….”

Cewar Saratu, kuma tun kafin ta ƙarashe Mama ta tari numfashinta.

“Eh, me ua, an taɓo mata ƙahon zuciyarta, yau ni Allah na tuba har na kalli wannan abun na ce shine ubna?!….”

“Mama ya isheki haka…. Da kike rena shi a yanda yake, gwara shi sau dubu da iyayen wasu, kuma ubn mutun ko a bola yake kwana indai har shi ne ya haifi mutum ro ubnsa ne, ko miji bai isa ya amsa sunan uba ba…. Kuma ki sani cewar; da uba ake ado…..”

Kuma Saratun na kaiwa nan ta miƙe daga kan tabarmar ta faɗa ɗakinsu har tana ƙoƙadin bangaje Rabi.

“Aikin banza…. Umma mi ye na faɗa ba dai-dai ba ?”

Mama ta tambaya tana tauna doyar bakinta, dan bisa ga dukkan alamu ma ba ta yi azumin ba yau”

“Wallahi baki da laifi, me ake da Ɗan Lami a rayuwa?!, ita ma in ta gaji da abinda ake masa ne a gidan nan,ta yi zuciya ta nemi mijin aure….”

Ita dai Rabi sai ido, dan bata isa ko tari ta yi ba, bata da wani kataɓus a gidan, yau wanda ya kawota ya aje ma bashi da iko da gidan bare ita karan kaɗa miya.

“Umma babu ruwan sanyi fa…”

Habiba ta kalli Fatima, sannan ta kalli ruwan dake aje a can baranda.

“Yanzu ke dan baƙin hali kinsan babu ruwan sanyi a gidan shi ne kika yi shiru, yanzu da an kira sallah fa?”

Ta kawar da kanta.

Habiba ta yi ƙwafa tana cince ƙullin dake gefen zaninta, ta fito da nera ɗari biyu, sannan ta cillawa Rabi.

“Karfa, uwr ‘yan baƙin hali, tashi ki je ki siyo mana ruwan sanyi leda ɗaya, kuma idan kin so ki zauna a can kin ji ?”

Rabi ba tace komai ba, ta miƙe tsaye, sannan ta shiga ɗakinsu ta ɗauki hijabinta, ta fita.

Mama ta bi bayanta da harara.

“Wallahi na tsani yarinyar nan, dan Allah Umma ki koreta ta koma inda ta fito”

Habiba ta yi dariya.

“Baki da hankali Mama, ai idan na barta haka ban amsa sunan Habiba ba, so nake sai ta tagayyara tukunna, ba na so ta koma wurin dangin uwarta ta ji daɗi, dan kinsan ai ‘yan uwan uwar tata suna da kuɗi, so nake sai ta gama lalacewa, so samu ma ta haɗa da cikin shee, sannan zan sa Ɗan Lami ya koreta daga gidanan, tunda dama ni ce na saka shi ya kawota!”

Mama ta tintsire da dariya, Fatima na na tayata.

Rabi na fita kai tsaye bakin titi ta nufa, a hanya ta tsaya tana kallon wasu yara dake buga wasan ƙwallo.

Ba yau ta saba ganinsu suna ƙwallon ba, kusan kullum a lokaci irin wannan suna buga ƙwallo, a wasu lokutan ma ba su ne suke yi ba, manya ne ke yi a filin, kasancewar ana azumi shi yasa manyan basa bugawa.

Tsaiwarta ta gyara tana ci gaba da kallonsu, ƙwallo na ɗaya daga cikin burukanta na duniya, ƙwallo mafarkin rayuwarta ce, a da bata da wani fata sai na ta zama shahararriyar ‘yar ƙwallo.

Sanda Ummanta na raye burin nata ya ɗauko hanyar cika, dan akwai wata football academy da Umman nata ta sakata, kuma kullum tana zuwa yin training, sai dai bayan rasuwar Umman tata komai ya sauya.

Komai ya ruguje, ciki kuwa harda burinta na zama ‘yar wasan ball, dan a nan gidan makaranta ma ba’a barta ta je ba, ta ina za’a barta ta wani samu damar tarining.

A gidan kakaninta kuwa cewa suke ai ƙwallo ba wasan mata ba ce, dan haka ita ƙwallo ba ta dace da ita ba, ko a sanda Umman na raye babu yanda ba’a kai ruwa rana ba a kan wannan ball ɗin.

Ganin tsaiwar ba zata kaita ba hasa ta kwashi ƙafafunta ta yi gaba.

FHA 2 lugbe, abuja

11:00am

Wasu baƙaƙen motoci ne har guda biyu suka yi parking a gaban wani gida cikin layin. Yanayin gudun motocin ne kaɗai zai tabbatar maka da ba lafiya ba.

Ƙofar gaba ta ɗaya daga cikin motocin ta buɗe, wani matashi ya fito a fusace, yanayin yanda yake fitar da iska daga hancinsa ne kaɗai zai tabbatar maka da cewar a fusace yake.

Sauran ƙofofin suka buɗe, sannan ɗaya bayan ɗaya mutanen ciki suka firfito, yanayin shigarsu ne kaɗai zai shaida maka matsayinsu.

Duka sanye suke da baƙaƙen kaya, sannan a jikin kowannensu akwai bullet proof jacket, wadda a jikinta aka rubuta DSS. Na farkon da ya fito ne kaɗai babu bullet proof jacket ɗin a jikinsa.

Kuma shi ne a kan gaba wajen shiga cikin gidan, a harabar gidan suka tsaya. Matashin sai safa a marwa yake, kamar wanda aka ɗorawa maganar duniya. Ɗaya daga cikin ma’aikatan ne ya taho kusa da shi, hannunsa riƙe da bullet proof jacket, a tsorace yace.

“Sir baka saka wannan ba…”

Wani irin kallo da ya masa ne yasa bai ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa ba.

Hakan yasa jami’in ja da baya, ya matsa kusa da mace ɗayan dake cikinsu, dan kaf wurin maza ne, ita kaɗai ce mace.

“Ki masa magana”

Kanta ta gyaɗa, sannan ta sofare bingarta ƙirar pistol a aljihun wandonta na baya. Ta sa hannu ta karɓi rigar, ta matsa kusa da shi.

“KULIYA kana buƙatar wannan…”

Sai da ya fitar da wani huci na takaici, sannan ya miƙo hannunsa ya fisgi rigar ba tare da ya kalleta ba, rigar ya saka yana ta hura hanci. Sannan ya yi alama da kawo masa abun magana.

“Ta ko ina gidanan a kewaye yake da jami’an tsaro, zai fi muku da ku miƙa wuyan ku cikin ruwan sanyi, idan kuma ba haka ba!…”

Ya kai ƙarshen maganar yana haɗe haƙwaran sama da na ƙasa cikin fusata, sai da ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba.

“Idan ba ku miƙa kanku ba, sai na binne kowannenku da ransa, idan kuma kun musa, kada wanda ya fito a cikinku!…”

<< Labarinsu 2Labarinsu 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×