Don't be afraid of falling apart. Some of the must beautiful heart are built from tragedy.
Bayan sati uku...
No.181, Guzape, Abuja...
09:30pm
MISHAL POV.
Kwance take a falo, ta duƙunƙuna cikin blanket, idanuwanta sun yi ja saboda kukan da ta ci, ta kunna tv ta tsura mata ido amma ba kallon take ba.
Damuwa da ruɗani ne suka saka rayuwarta a gaba, yau kusan sati uku kenan, amma Antinta Adawiyya ba ta zuwa makaranta, tun ta na ganin abun kamar fashi ne, har fashin nata ya zo ya soma bata tsoro. . .