Love is; when you hug someone and they feels like home…
No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.
A fusace Jadda ta shigo cikin gidan tana famar bambami, kamar wadda ta zauce. Hajjara na zaune a kan kujera tana taunar chewing gum, haɗi da latsa wayarta, wani ɗan iskan kallo ta bi Jaddan da shi, kafin ta ci gaba da kallon wayarta, daga gefen ta kuma Fahima ce zaune ta na wasa, yayin da Hammad ke zaune a kan dinning ya na cin abinci.
“Wallahi wannan yaron da aka aurawa Hafsat ya ɓatata, yo in ba haka ba ta ya za ayi na je na ce ta taho mu tafi, amma ta ce ba za ta zo ba?, wata ƙila ma shanyeta ya yi!…”
Haka ta dinga sambatu, har ta kai ɗakin da ke a mazaunin nata, ta riga ta yanke shawarar barin garin a yau, don babu abun da za ta zauna ta yi a Abuja, tun da wadda take zaune don itan ta ƙi yarda ta biyota, duk da wahalar da ta sha kafin ta samu adireshin gidan nata.
Kuma ta riga da ta yamie shawarar datse ko wace alaƙa dake tsakaninta da Mishal ɗin, tun da ita ba ta da mutunci, wai ita ‘yar daɗi miji, tun da ta zaɓi zama da shi ga fili ga me doki, sukuwa kawai ta rage, kuma Allah ya bata sa’a, amma ita da Mishal kam ko a lahira!.
No.181, Guzape, Abuja…
07:55 PM.
YUSHAL POV.(ALIYU & MISHAL)
“Ga shi”
Muryar Kuliya ta faɗi, a sanda yake miƙawa Mishal wani ɗan ƙaramin bowl dake ɗauke da yankakkakiyar albasa.
Rai a cunkune Mishal ta kai hannu ta karɓa, sannan ta juya kan stove, ta buɗe murfin tukunyar da take dafa jallof ɗin shinkafa, ta zuba albasar, sannan ta rufe murfin tukunyar. Ta ajiye bowl ɗin ta shiga wanke hannunta a sink.
Kuliya ya ci gaba da kallonta, ya na nazarin yanayinta, tun bayan da suka yi wannan faɗan da Jadda bata dawo dai-dai ba, kuma saboda ya san ta na cikin yanayin damuwar ne ya sa shi dawowa gida da wuri. Amma duk da haka sai ya isketa cikin damuwar.
Ko bayan da ta gama wankewa hannunta, sai ta ci gaba da tsayuwa a jikin sink ɗin, ta shiga karanta wasiƙar jakin da ba ta da ranar ƙarewa.
A hankali Kuliya ya isa bayanta, sannan ya saka hannaynesa ya kewaye waist ɗinta, ya janyota baya, tare da mannata da jikinsa. Mishal ta rintse idonta, saboda da wannan sanyin da ya fara shiga kowace ƙofa ta gashi a cikin jikinta.
“Me yake damunki?”
Sai ta buɗe idonta, ta soma kallon garden ɗin gidan ta windown dake kusa da sink ɗin, amma bata ce masa komai ba.
A hankali Kuliya ya sunkuyo da kansa zuwa kafaɗarta, sannan ya manna mata peck a wuya, wanda ya sa ba shiri ta damƙe bakin sink ɗin.
“Me yake damunki?”
Ya tambaya wannan karon a cikin kunnuwanta, kuma murya ƙasa-ƙasa, wadda ta sa Mishal saurin juyawa a cikin hannayensa tana kallonsa. Hannayenta a kan kafaɗunsa, idonta a kan kyakkyawar fuskarsa. Peck ya mata a goshinta, hakan ya sa ta lumshe idonta.
“Me yake damunki?”
Ya kuma tambaya a karo na uku, yayin da goshinsa ke kare da nata, hancinsa a kan nata. Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta fara hawaye, da sauri ya zare hannayensa daga jikinta ya dawo da su kan fuskarta ya na share mata su.
“Ba ki yarda da ni ba ne ?”
Da sauri ta girgiza kanta.
“Na yarda da kai sosai, wata ƙila ma sama da yanda na yarda da kaina, ina cikin damuwa saboda rashin ganin Yayata, yau ma fa ba ta zo ba, jikina na bani cewar ta na cikin matsala”
Kuliya ya girgiza mata kai ya na cije laɓensa na ƙa. Tare da share mata wata ƙwallar dake bin fuskarta, ashe kenan hasashensa bai zama gaskiya ba, ba abun da suka yi da Jadda ba ne a ranta, damuwar Rabi ce a ran nata.
“Insha-Allah ta na cikin hali me kyau, ki kyautata mata zato, da yardar Allah zan nemo miki ita, wannan alƙawari na ne”
“Ka min alƙawari?”
Ta tambaya muryarta a raunane.
Kuliya ya gyaɗa mata kai ya na ci gaba da share mata hawayen, kwanciya ta yi a jikinsa tana sakin wani kukan, Kuliya ya gyara mata riƙo a cikin jikinsa.
“Ki na so mu yi faɗa?”
Ta girgiza kanta, hakan ya sa jikinsa motsawa, saboda kanta dake kwance a ƙirjinsa. Ya ɗaga kafaɗa yana faɗin.
“To ki dena kuka… Ke fa kina da ƙarfin zuciya, you are so strong Teddy Bear, so don’t cry!”
Sai ta gyaɗa masa kai. Sautin tafasar tukunya ne ya ankarar da su girkin da suke, don dukansu sun ma manta da girkin.
Hakan ya sa da sauri Mishal ta fice daga jikinsa ta koma jikin stove ɗin. Shi kuma ya koma ya zauna a kan kujera ya na kallonta.
Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja
RAJA POV.
Zaune yake a kan kujerar dake kallon gadon marasa lafiya na ɗakin da aka kwantar da Rabi’a. Bayansa jingine da jikin kujerar, yayin da ƙarfen da aka saƙala drip ɗin da aka saka masa yake aje a gefensa, hannunsa na dama juma saƙale da allurar dake aika drip ɗin zuwa cikin jikinsa, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Rabi’ar dake kwance akan gadon.
A ɗazun suma ya yi, har sai da aka ƙaramasa ruwa, kuma ya na farkawa ya fito daga ɗakin da aka kwantar da shi, ya dawo nan ya zauna. A hankali wata ƙwalla ta gangaro daga idonsa, bayan da ya tuna irin gararin rayuwar da take ciki, yanzu kuma ga wani baƙin tabo me matuƙar muni ta ƙara samu.
Amma alƙawari ya yi wa kansa, na babu abun da zai hana shi aurenta, ko da sama da ƙasa za su haɗe, ko da duniyar ce za ta tashi, ko da kuwa aurenta shi ne abu na ƙarshe da zai yi a duniyar nan, ba fyaɗ… Kasa ƙarasa kalmar ya yi a ransa, don haka kawai ya tsalleketa ya tafi tunaninsa na gaba; ko da cuta me karya garkuwar jiki ce tare da ita, ba zata hanashi aurenta ba, wani kalar so yake mata da ya wuce soyyaya kawai, sai dai soyyayar haɗuwar jini, kasancewarta ɗaya daga cikin ahalinsa shi ne ya ƙara ninka soyyayarta a ransa.
Ganin ruwan da aka saka masa ya ƙare yasa ya kai hannunsa ya cire allurar, sannan ya manne wurin da plaster, saboda kada jini ya zubo, miƙewa ya yi, duk da ya na jin jikinsa babu ƙwari, amma haka ya taka a daddafe har ya isa jikin gadon da Rabi’a ke kwance kamar gawa.
Zama ya yi a gefen gadon ya na kallon fuskarta, sannan ya kamo hannunta na dama, wanda ke saƙale da clip na wata na’ura dake jikinta, hannunsa ya saka cikin nata ya damƙe, dubansa ya dawo kan fuskarta. Wadda a yanzu ta sauya suffa daga tata ta da, sakamakon wani yanka dake gefen fuskarta na hagu.
Ɗinkin da ya ga an yiwa raunin ya sa ya fahimci girmansa, ga kuma yanda fuskarta ta ɗan tattare daga gefen hagun, saboda yankan da aka mata, amma duk da haka kammanin fuskarta ba su sauya ba.
Sai kuma gashin kanta da ya lura da kamar sun rage masa tsayi, duk da shi bai taɓa ganin gashinta ba, amma ya yana da yaƙinin cewa gashin kan nata ba haka yake ba, kuma ya fahimci kamar saboda raunukan dake kanta aka rage yawan gashin.
Idanuwanta a rufe, fatar bakinta ta yi fari sol, a kallo ɗaya idan ka mata sai ka ce maccacciya ce, shi kansa ba don Huzaifa ya tabbatar masa da tana raye ba da ba zai yarda da tana da ran ba.
Jikinta sanye yake da rigar asibitin, wadda take blue colour, sai farin bargon asibitin da aka rufa mata a rabin jikinta.
Ya tuna yanayin murmushinta, ya tuna sanyin maganarta, ya tuna nutsuwarta, ya tuna hankalinta, ya tuna yanda take kallonsa da idanuwanta masu kama da na Aliyu, ya tuna komai a kanta, hatta da ranar da ya fara ganinta sai da ya tuna.
Idonsa ya rintse a sanda hoton file ɗinta da ya buɗe a ɗazu ya dawo masa cikin tunani, wai mutum biyar ko sama da haka ne suka mata fyaɗe, sannan bayan haka ma harda raunikan a jikinta, ga kuma dukan kanta da aka yi, wanda shi ne maƙasudin shigarta doguwar suma. A hankali ya buɗe idanunsa nasa, wanda ya yi ja kamar sabon barkwano.
A dai-dai lokacin Rhoda da ya aika ta shigo ɗakin, juyawa ya yi ya kalleta, a sanda ta ke ƙarasowa ciki. Sai kuma ya ɗauke kansa ya na dawowa da dubansa kan Rabi’a. Ya ɗaga kafaɗarsa kafin yace.
“Me kika gano?”
Ya tambaya cikin wata murya me ɗaci, Rhoda ta haɗiye yawu sannan tace.
“Na yi magana da waɗanda suka tsince ta a lokacin, kuma su ne suka kawota wannan asibitin, amma su… sun ce a gefen hanya suka ganta, nannaɗe cikin bargo, ko… Ko… Tufafi… Ba… Babu a jikin… jikinta!…”
Raja ya rintse idonsa, jikinsa har karkarwa yake, ga kuma hannun Rabin da ya ƙara damƙewa cikin nasa, Allah ne kaɗai ya san yanda zuciyarsa ke tafarfasa, shi kansa ya na mamakin yanda yake iya riƙe kansa a wannan lokacin, amma shi ya riga da ya san kansa, ba ya iya ɗaukar ɓacin rai, ya kan jima ransa bai ɓaci ba, don ba komai ne ke ɓata masa rai ba, amma idam har ransa ya ɓaci to na kowa ma kan iya ɓaci.
“Bargo?”
Ya tambaya ya na ɗan juyowa da kansa ya kalleta.
“Eh bargo, kuma sun ce wata ƙila ma a kan bargon aka haike mata… Dan sun ga something like spam a … A jikin bargon!”
Yanzu kam miƙewa ya yi tsaye, kuma ba tare da ya damu ba ya nufi kan wata chest drawer, ya kai hannunsa ya yi fatali da kayan kai, ƙaran abubuwan da suka fashe sai da suka razana Rhoda. Da gudu ta yi kansa ta na riƙeshi.
“Zaid!, Zaid! Ka nutsu, ka nutsu ka ji”
Ta faɗi hawaye na mata zuba, yayin da take bubbuga kafaɗarsa.
Ƙofar ɗakin aka turo, wata nurse ta leƙo da kanta.
“Lafiya kuwa?”
Rhoda ta juya ta kalleta.
“Lafiya, mun gode, za ki iya tafiya”
Nurse ɗin ta taɓe baki ta na jan ƙofar, da ma wucewa ta zo yi ta ji ƙara, shi ya sa gulmarta ta motsa, har ta kaita ga leƙowa don ganin meke going.
“Ka nustu ka ji?”
Cewar Rhoda ta na shafa ƙirjin Raja, wanda yake huci kamar wani zakin da ya je farauta bai samo komai ba.
Hannunsa ta kama ta zaunar da shi a kan kujera, tana shafa kansa. Idonsa ƙir a kan Rabi, wani abu me ɗaci yana kai kawo daga maƙogwaronsa zuwa bakinsa, ga wani ɗaci da zafi da ransa ke masa, ji yake kamar wuta ce kr ci a ƙirjin nasa, kamar da aka tsire zuciyarsa a tukubar tsire.
“Ga shi… Karɓi ka sha”
Kansa ya ɗan ɗaga ya kalli Rhoda dake miƙa masa cup ɗauke da ruwa. Karɓa ya yi ya sha, a lokacin da ita kuma Rhodan take zama a kusa da shi, hannunta ta kai ta share hawayenta.
“Wannan ba shi ne mafita ba Zaid, kamata ya yi a ce ka yi tunanin mafita ba wai fusata ba, akwai ranar da za mu huce haushinmu a kan wanda suka aikatawa Ammata haka”
Ya juyo ya kalleta ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, mafita? Tabbasa ta na da gaskiya, haka ya kamata ace ya kasance, kamata ya yi ace ya nemo wata mafitar da za su iya kama masu lefin, dan a nan me lefin ba ɗaya ko biyu ba ne, mutum biyar ake zargi, wata ƙila ma sama da haka.
Hannunsa na dama ya dunƙule ya ɗora a kan bakinsa, sannan ya rufe idonsa dan samun nutsuwa, ta yanda zai yi tunani me kyau. Kusan shuɗewar mintuna goma, sannan ya buɗe idonsa.
“Shin kin tambayesu da bargon suka kawota nan?”
Rhoda ta ɗan kalleshi.
“Idan ba da bargon ba to da ne za su kawota nan ɗin?”
“Correct, makamar mu ta farko kenan, ki tambaya mana Huzaifa, shin har yanzu wannan bargon ya na nan?, In har ya na nan, to wannan bargon shi ne madafarmu, ta hanyarsa za mu iya kama masu lefin”
“Ok”
Raja ya juya ya ƙara meda idonsa kan Rabi’a.
“Wallahi!, Wallahi!, Wallahi! Rhoda idan har… Na kama me laifin nan, ba zan sassauta masa ba, sai na tabbatar da na gana masa azabar da tun da uwrsa ta kawo shi duniya ba’a taɓa masa ba, sai na tabbatar da ya yi wata ɗaya ba tare da ya ga hasken rana ba, sai na tabbatar da ya kwana a cikin fitsarinsa, sai na tabbatar da bai ƙara ko da kusantar macen da ba ta hallata gareshi ba, sai na ɗai-ɗaita rayuwarsa, wannan alƙawarina ne!”.
No.181, Guzape, Abuja…
MISHAL POV.
Tana zaune a bakin gadonta, yayin da take cire sliders ɗin ƙafarta, ƙafafun nata ta ɗauke daga ƙasa, ta ɗorasu a kan gado, tana jan bargo dan rufe ƙafafunta nata, aka turo ƙofar ɗakin.
Kallon ƙofar ta yi, a sanda Kuliya yake shigowa, ganinsa ya sa ta fasa kwanciya ta zauna, cike da mamaki take kallonsa.
“Me ya faru?”
Ta tambaya. Ba tare da ya amsata ba, ya zagaya ta ɗayan ɓangaren gadon ya zauna, ya na cire takalman ƙafarsa.
Mamakin dake kan fuskar Mishal a yanzu ya ma fi na ɗazu, ido waje take kallonsa.
“Wai… Wai me yake faru?…”
Ba ta ko ƙarasa faɗin kalaman ba, ya janyota jikinsa, tare da kwantar da ita. Idanuwanta suka ƙara girma wajen kallonsa. Wai me bawan Allahn nan yake nufi da ita ne?, me yake shirin yi haka?.
Sakata ya yi a tsakiyar hannayensa, ya kwantar da kanta a ƙirjinsa, ya matseta a jikinsa sosai, har wata ajiyar zuciya yake sauƙewa.
“Ab… Abu Aswad”
Kafaɗarsa ta dama ya ɗafa yana ƙara kewaye hannunsa dake jikinta. Alamun dai ya na jinta.
“Me ya faru?”
Ta tambaya ta na shaƙar ƙashin turarensa.
“Babu komai, kawai de ba zan iya ba ci ba tare da matata ba ne”
Muryarsa ta furta hakan a hankali cikin duhun daren. Shiru ya ƙara rasta ɗakin, jin yanda yake sauƙe ajiyar zuciya, ya sa Mishal saka hannayenta ta kewaye shi ita ma.
“Abu Aswad”
“Ummm Teddy Bear”
“I hate you”
Tana jin sautin murmushinsa a kanta.
“And i love you”
“I hate you ”
“I said i love you”
Kusan a tare suka yi dariya.
“Gobe akwai school, ki kwanta ki yi bacci”
Kwanciyarta ta gyara a jikinsa tana lumshewa idonta.
One hug fixes everything…