T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.
ZAID POV.
Zaune yake a kan kujera ya na facing Rhoda, wadda ke daddana system ɗin dake kan cinyarta, hankalinsa rabi na kanta rabi kuma na ga wayar da yake ta jira, dan kuwa a jiya ya aikawa da office ɗinsu saƙon yana san magana da ogansu, ya san da cewa a yau ɗinnan za su kira, amma kuma ba zai iya jure zaman gidan suna cikin wannan halin shi da Adawiyya ba, ba zai iya zama a gidan ta na gudunsa ba, gwara ya ba ta space, ko ta samu damar sararawa a gidan, ina yado bayan ya koma sai ya amsa kiran.
“Dude!… Zo ka gani!”
Cewar Rhoda, mamaki mamaye da fuskarta, idonta kyar a kan system ɗin gabanta. Da sauri Raja ya miƙe ya dawo gefenta ya na kallon system ɗin.
A jiya suka samo putage na CCTV camera ɗin dake layin da aka cillar da Adawiyya bayan da aka haike mata, ba ƙaramar wahala suka sha ba kafin suka samu putage ɗin, sannan kuma suna da tabbacin putage din shi ne zai kaisu ga karshen binciken da suka fara.
A tare suka juyo suna kallon juna shi da Rhoda, bayan da vedion ya kai ƙarshe.
“Usman?!”
Rhoda ta tambaya tana dubansa. Nan take idon Raja ya kaɗa ya yi ja, babu abun da Rhoda ke iya hangowa sai wutar masifa da tashin hankalin dake ci a cikinsu.
“Ba zan barsu ba!…”
Ya faɗi ya na miƙewa, da sauri Rhoda ta kamo hannunsa tana maida shi inda ya miƙe. Kai ta shiga girgiza masa alamin a’a.
“Zuwa yanzu case ɗin ya zama biyu Zaid… Ka fara miƙa hujjojji game da Alhaji Bala tukunna, idan an bamu izinin kamu, sai mu haɗa mu kamasu su duka!”
Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga ya na cije leɓensa na ƙasa.
“Kin tabbatar da haka ya kamata a yi?”
Rhoda ta gyaɗa masa kai cike da tabbatarwa.
Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.
Habiba ce zaune a tsakar gida ta na dunduma jikinta da ruwan ɗumi, kwana uku kenan da aka sakota daga hannun ‘yan sanda, kuma dukan da ta ci a hannunsa ne har yanzu be bar jikinta ba, dan ta doku ba ƙarya. Ita ta yi ma mamaki da suka sakota da wuri haka, duk da shi Ɗan Lami ma ko kwana be yi a wurinsu ba.
Sallamar Saratu ta ji daga bakin ƙofa, hakan ya sa ta juya ta na kallonta.
“Sannu Umma… jikin ne?”
Habiba ta gyaɗa kai tana matsa ƙafarta.
“Amarsu kenan, daga ina kike ne?”
Habiban ta tambaya kamar ba ita ba, a sanda Saratun ta karɓi ƙyallen hannunta ta shiga dunduma mata jikin nata. Saratu ta yi murmushi.
“Gidan su Farida na je, zuwa gobe za mu fara rabon cingam”
Habiba ta gyaɗa kanta, zuwa yanzu ta fara shiga hankalinta, ta fara gane gaskiya da akasinta, a jiya Saratu ke faɗa mata cewar wai Rabi ta yi aure, kuma wannan me kamar tata ne ya aureta, sai kuma ganin nutsuwar da Ɗan Lami ya fara yi, ita ma ta sa ta shiga taitayinta, ta gane cewa Allah ɗaya ne, dan kuwa ga shi dai duk wannan abubuwan da ta yi ta yi, ba su hana Rabi auruwa ba, kuma duk wannan makirce-makircen da ta yi ta yi, ba su hana ikon Allah faruwa ba.
Wata sallamar suka ji cikin wata murya me kama da ta Mama, cikin sauri kuma a tare suka kalli ƙofar gidan. Sannan cikin daƙiƙa ɗaya suka miƙe a zabure. Kallonta suke suna san su gane wacece.
“Ni ce Umma, ni ce Mamanki!…”
Cikin kuka Mama take faɗin hakan, tare da sakin jakar hannunta, hannu na karkarwa Habiba ta nuna Maman dake tsaye a gabanta.
“Ma… mama… Mama!”
Tsaye take a gabansu, jikinta ɗauke da cikin da ya fara fitowa, ga wasu ƙuraje da suka bai-baye mata jiki, ta wani kalar rame ta ƙwanjare, ta yi baƙi ƙirin da ita.
Allah kenan, za ka yi ta saɓa masa ya na ara maka dama, rana ɗaya kuma idon ya tashi kamaka, sai ka gwammaci ba a hallici me kamarka a duniyar nan ba. Domin kuwa shi ya fi kowa iya kamu.
Don’t be afraid to lose people. Be afraid of losing yourself by trying to please anyone around you
No.86, Garki 2, Abuja…
RAJA POV.
A hankali ya turo ƙofar shiga falo, bakinsa ɗauke da sallama. Cak ya tsaya, sakamakon ganin Rabi tsaye a tsakiyar falon, hannayenta harɗe a ƙirjinta, ta kafe shi da wani irin kallon tuhuma, duk wata ƙwarin gwiwa da ya zo da ita dan ya mata wasu tambayoyi game da abun da ya faru da ita sai ya ji ya gushe, kallon da take masa yana ƙarasawa ya ji ya muzanta, don ita ba ta kallonsa a matsayinsa miji gareta ko yaya, kallo take masa a matsayin ɗan daba, kuma makashi.
Wani yawu ya haɗiya, sannan ba tare da yace mata komai ba ya ɗauke idonsa a kanta ya shiga ƙoƙarin nufar ɗakinsa. Sai de me?, tsulum ya ganta tsaye a gabansa, ta na ci gaba da kallonsa cike da tuhuma.
“Waye kai?”
Tambayar ta doka wata ƙatuwar ganga me amon gaske a cikin kan Zaid, ya kafeta da idonsa, amma ya kasa ce mata komai.
“Zaid! Waye kai?”
Yawu ya haɗiya ya na faɗin.
“I’m a goon!”
Kanta ta girgiza tana sauƙe hannayenta daga ƙirjinta.
“I mean real you… Waye kai!”
Ta kuma maimaita masa tambayar, hakan ya saka zuciyar Zaid cikin kokwanto, to me take nufi da waye shi?, ko de ta gano wani abu a kansa ne?, ina ba zata gano komai ba. Dan haka ya haɗiye yawu yana faɗin.
“I am a killer and drug trafficker. I’m goon”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa, sosai rungumar ta ba shi mamaki, idonsa ya lumshe sannan ya buɗe, kusan shuɗewar muntuna biyar, kafin ta sake shi tana kallon fuskarsa.
“Akwai wani rubutu da na taɓa karantawa. A rubutun an ce, idan har ka rungumi mutum na tsawon muntun biyar, to za ka fara yarda da duk abun da zai ce, amma har yanzu ni ban yarda da kai ba. I will ask you for the very last time… Who are you Zaid”
Raja ga haɗiye wani kakkauran miyau me ɗaci, sannan ya lumshe idonsa ya buɗesu a kanta, kana ya amsa mata da:
“Zaid Aliyu… Department of state service (DSS) officer!”
No.181, Guzape, Abuja…
MISHAL POV.
“Yaushe za mu je gidan Anna?”
Ta tambaya ta na saka kayan Kuliya da ta wanke yau da safe a cikin loka. Kuliya dake zaune a bakin gado yan danna waya ya kalleta.
“Me ya faru?”
Ya tambaya. Mishal ta girgiza kai ta na saka wata rigar cikin lokar.
“Kawai de ina kewarta ne?”
Sai ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na gyaɗa mata kai.
“Nanbda sati ɗaya ne fa Teddy Bear,saurin me kike?”
Ta juya ta na ci gaba da aikinta tare da faɗin.
“Na gaji da zuwa school ne… Kuma mun kusa mu fara exams”
Lokar ta rufe, sannan ta juyo ta iso gareshi.
“Next term za ku fara Neco da Waec right”
“Ummm!”
Ta amsa masa tana karɓar wayar hannunsa.
“Lokacin danna waya ya ƙare, let’s fall asleep”
Murmushi ya yi ya ja kamo hannunta, tare da zaunar da ita akan gadon. Wayarsa dake haannunta ya karɓa ya na ajeta kan side drawer. Kwantar da ita ya yi a kan gadon, ya juya ya kashe wutar ɗakin, sannan shi ma ya kwanta ya na karata da jikinsa.
“Abu Aswad?”
Mishal ta kira sunan bayan wani lokaci.
“Ummm!”
Muryar Kuliya ta amsa ƙasa-ƙasa, alamun kamar ma ya fara bacci.
“Yaya batun Anti Adawiyya?”
Tar Kuliya ya buɗe idonsa cikin duhun ɗakin. Jin ta ambato masa sunanta, bayan da ya gama bincike ya gano komai a kanta, ciki kuwa har da fyaɗen da aka mata, sai de kuma baya so ya faɗa mata komai, dan baya so hankalinta ya tashi, shi ya sa bar wa cikinsa maganar, ba tare da ya faɗa mata komai ba.
“Sharon tace zuwa gobe za a iya samo address ɗin gidansu, ki kwantar da hankalinki!”
Ya faɗa mata dan ta kwantar da hankalinta, wata ƙwalla ce ta taru a idon Mishal, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta silalo. Sai jin damshi Kuliya ya yi a gaban rigarsa, kasancewar kanta na kan ƙirjinsa ne. Iska ya furzar daga bakinsa ya na ƙara ƙanƙameta.
“Hafsat?”
“Na’am!”
Ta amsa a raunane.
“Ni fa da kaina na ce miki zan gano miki inda take, babu abun da zai sameta”
Hawayen ta goge da kanta tana gyaɗa kai.
“Umhumm!”
“I love you, maza ki yi baccin ki…..”
“I hate you”
Ta faɗi tana lumshe idonta.
No.86, Garki 2, Abuja…
10:20 PM.
RABI’A POV.
Tsaye take daga jikin dressing mirrorn ɗakinta, a hankali ta aje wayarta dake riƙe a hannunta, bayan da suka gama waya da Jidda. Juyowar da za ta yi ta ji an buɗe ƙofar ɗakin. Ba shiri zuciyarta ta doka tsallen albarka a ƙirjinta har sau biyu. Dan kuwa ko ba’a faɗa ba, ko ba ta kalla ba, ta san waye, hakan ya sa ba tare da ta ko kalli side ɗin ƙofar ba, ta juya ta ƙara fuskantar mirronrn.
Allah ya sani, sam bata son su haɗu, ba ta son wani abu ya haɗasu, ta na jin kunyarsa da kuma kunyar kanta da ta yi masa mummunar fahimta, tana ta zarginsa game da abun da sam bai aikata ba, me ya sa zuciyarta ta yarda da abun da idanuwanta suka gani?, me ya sa har take zaton shi zai iya aikata wannan mummunar ta’asar?, kaiconta da ta kasance mace me matuƙar san kai. Satinsu ɗaya da aure, amma fur ba ta yarda su haɗu ko da wasa, kullum za ta yi girki ta aje masa nasa amma ko da kaɗan ba ta bari ya ganta.
Ba za ta iya haɗa ido da shi ba, ta kalli tsabar idonsa tace shi makashi ne, tace za ma ta iya kaksheshi, duk da ba da gaske take ba, amma ai ta faɗa. Tunaninta ya katse a sanda ta ji tsayuwarsa a bayanta. Hakan ya sa ta ɗaga idonta ta kalli fuskarsa ta cikin mudubin dake gabanta.
Zaid ya ci gaba da kallonta da lumsassun idanuwansa, tun bayan ranar da ya bayyana mata gaskiyar kasancewarsa ma’aikacin DSS suka shiga wasan ‘yar ɓuya shi da ita, wata ƙila kunyarsa take ji, wata ƙila kuma ba ta yarda da abun da ya faɗa ba ne. Ko ma de me take tunani a kai, shi de be damu ba, damuwarsa ita ce rashin ganinta, nisantarsa da take ya fi sosa masa rai, shi be ƙi a kullum ya kasance da ita ba, ko da kuwa za su ci gaba da zaman doya damanja ne, dole ne ta sama musu mafita, dan shi kam gaskiya ya gaji da wannan tazarar da suke bawa juna.
“Ammatan Raja!”
Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, ko a da ma ya ake ƙarewa idan ta ji sunan?, bare yanzu da sunan ya samu ƙari a gaba, ‘Ammatan Raja!’ haka yake kiranta. Sai ta kasa amsawa, ta ci gaba da kallonsa ta cikin mirrorn.
Raja ya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya yi taku ɗaya… Biyu.. Wanda ya ƙara kusanta shi da ita, sannan ya ɗaga hannayensa tare da zurasu ta ƙugunta, suka kewayo zuwa cikinta, kafin ya jata baya zuwa jikinsa, ya sunkuyo da kansa zuwa wuyanta.
Ba shiri Rabi ta rintse idonta gam, wai me ya sa?, me ya sa duk yadda zai taɓa jikinta irin haka sai ta ji wani sauyi tare da ita,me ya sa?.
“Na yi lefi ne?… Ko har yanzu ni makashi ne a idonki?”
Ya tambaya muryar ta sa na fita a hankali, Rabi’a za ta iya cewa sai da kalaman suka gama shawagi a kan fatar wuyanta kafin suka isa zuwa ga kunnuwanta, a lokaci guda kuma sai ta ji jikinta ya ɗauki wani irin ɗumi, kamar wata wadda aka kara a jikin kyandir, ko wata ƙofa ta gashi a jikinta ta buɗe. Amma sai ta ture komai ta girgiza masa kai.
Zaid ya saka hannayensa ya na juyowa da ita, ta fuskanceshi, ya sunkuyar da kansa dan samun damar haɗa ido da ita amma fur ta ƙi barin hakan ta faru, don nata idanuwan kulle su ta yi gam.
“Idan de kika ci gaba da yin abun da kike ɗin nan zan ɗauka cewar har yanzu baki yarda da ni ba!”
Da sauri Rabi’a ta buɗe idonta, dan kuwa gwara ta sha kunya da ace ya ɗauka cewar bata yarda da shi ba ne, a yanzu tana jin wani irin girma da kamarsa na ƙara hauhawa a cikin ranta, wani irin kwarjini yake mata, wanda ba za ta iya kwantanta kalarsa ba.
“Trust me Diary… Wallahi gaskiya na faɗa…”
Da sauri Rabi ta ɗago da hannunta ta rufe masa baki tana girgiza masa kai.
“I trust you Raj. And I’m sorry”
Cikin hanzari Zaid ya kai hannunsa ya kamo nata dake kan bakinsa, ya riƙe hannun nata ya na kallon fuskarta da ta fara jiƙewa da hawaye.
“Babu buƙata Ammata, kuskuren fahimta ne”
Rabi ta ja hanci.
“Amma me ya sa to ni na kasa fahimtarka?. Ya kamata ace na fahimceka Raj… I’m sorry… I’m really really sorry…”
Saurin rungumeta Zaid ya yi, hakan ya bata damar sakin kukan dake cin ranta, ta masa kuskure, abun da ta masa sam be kamataba, ta aikata babban kuskure.
“Ka yi haƙuri please!”
Kansa ya ci gaba da girgiza mata yana ƙara ƙanƙameta a cikin jikinsa.
“Wallahi sam ba ki min kuskure ba. A ko da yaushe ni me miki uzuri ne ko da kin yi laifi, bare kuma ba ki aikata komai ba. Ba dan komai ya sa na ɓoye miki ba sai dan yanayin aiki, ina kan wani assignment ne yanzu haka”
Rabi ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tana sakin wani kukan, ba ƙaramin ɗaɗi wannan shauƙin yake da ba, me yafi wannan daɗi a duniya?. Ka kasance a tsakiyar hannun wanda ƙaunarsa ke daddatsa ruhinka a ko da yaushe, wanda shi ma taka ƙaunar ke kai kawo a cikin nasa ruhin. Me ya fishi daɗi?.
Ta jima a jikinsa tana kuka, kafin ya ɗago da ita yana share mata hawaye, a lokacin ta samu damar kallon fuskarsa, dan haka ta ɗaga nata hannayen ita ma, tare da kamo fuskarsa.
“Ban taɓa faɗa maka wannan ba, amma yau zan faɗa. I love you… I love you Raj…”
Da sauri Zaid ya kara fuskarsa kan tata yana sauƙe tagwayan numfashi. Rabi ta lumshe idonta hawaye wani na bin wani.
“You love me Adawiyya?”
Ya tambaya, dan ya kasa gaskata kunnuwansa, he can’t believe, wai yau shi Ammata take cewa tana so?, abun is unbelievable. Bakin Rabi tale cikin kuka, idonta a rufe ta gyaɗa masa kai, wanda hakan ya sa nasa kan ma motsawa tare da nata.
“I adore you, i love you…”
“Kwatankwacin yaya?”
“Like damn… Damn much Raj!”
“Alhamdullilah!”
Ya furta yana ɗora lips ɗinsa a kan nata.
“Adawiyya!”
Idonta ta buɗe jikinta na tsuma, saboda yanda ya yi maganar lips ɗinsa na goguwa a kan nata.
“Can i kiss yah?…”
Bai ko ƙarashe ba, ita ta saka hannyenta ta kama fuskarsa, tare da haɗe bakinta da nasa.
Zaid ya saka hannayensa ta bayanta yana ƙara matseta a jikinsa.