Skip to content
Part 51 of 55 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

Haka ya kai ƙasa yana haki, kamar wanda aka koro, idonsa har lumshewa yake, kuma a cikin lumshewar idonsa ya hangi ƙofar closet. Kamar an cillo shi daga wata uwa duniya haka ya miƙe tsaye ya nufi ƙofar closet ɗin. Ya shiga cika ya na ta dube-dube. Har ya fara fawallawa Allah, yana tunanin cewa wata ƙila sun tafi da su ɗin. Kuma a dai-dai lokacin idonsa ya sauƙa a kan wani ɗigon jini, kamar ƙofar da aka buga da ƙarfi haka zuciyarsa ta buga. Ya dawo da dubansa kan lokar da yake tsaye a gabanta. Ya shiga bin jikinta da kallo a hankali, kafin ya samo wata makkuna a jiki. Hannunsa na rawa haka ya danna switch ɗin. Lokar ta zuge zuwa gefe, wata ƙofa ta bayyana a gabansa. Sai da ya haɗiyi yawu, na tsoron abun da zai iya tararwa a bayan ƙofar. Kafin ya kai hannunsa ya turata ciki.

Abu na farko da ya fara cin karo da shi shi ne; wannan yarinyar da tace yana kama da yayanta ce durƙushe a ƙasa tana kuka, gefen fuskarta ɓace da jini. Daga ɗayan ɓangaren kuma, Aliyunsa ne jingine da bango.

Shin kun san yanda mutum kan ji a sanda ya ga wani abunsa da ya cire rai da samunsa?. Ko kun san yanda ake ji a sanda ka samu abun da baka taɓa tsamaninsa ba?. To idan de har kun sani, wannan shi ne halin da Zaid Aliyu ya shiga.

There is no WiFi in forest, but you will find a better connection.

No.86, Garki 2, Abuja…

RABI’A POV.

A hankali ta shiga ƙi-ƙifta idonta, kafin ta buɗesu gaba ɗaya. Hannunta ta kai kan side drawer tana kunna wutar ɗakin, kafin dubanta ya dawo gefen inda take kwance, inda take kyautata zaton Zaid na kwance a wurin. Sai de me?, wayam haka ta ga wurin, sai wata takarda da aka yi rubutu a jiki, ajet a kan pillownsa. Ganin hakan ya sa hankalinta da ya fara tashi kwanciya.

Hannunta na dama ta miƙa tana ɗaukar takardar, a lokaci guda kuma tana hamma, dan baccin be isheta ba.

_Ba zan iya jira zuwa gobe ba, dan haka na tafi, zan turo Rhoda ta kaiki AS roma Academy, ki je, ki buga wasa me kyau, ba na son ki bani kunya, na san matata jarumace, dan haka ki nuna ƙwarewarki… Daga mijinki abun somki… Zaid (Raja)_.

Dariya ta ɗan yi tana aje takardar. Abun be bata mamaki ba, dan ta ga ƙoƙarinsa a jiyan da tace masa ya bari sai gobe kuma ya bari ɗin, ashe shi bai haƙura ba.

Sauƙa ta yi daga kan gadon tana hamma. Kamar jiya, yau ma bata jin daɗin jikinta. Ita ta rasa abun da yake damunta a kwanakin nan, sai ta yi ta amai, ga kasala, ga kuma rashin san cin abinci da ba ta yi.

Sallah ita ce abu na farko da ta fara yi, kafin ta shiga gyaran gidan, bayan ta gama gyara gidan, ta ɗora girki, tana gama girkin ta faɗa wanka. Bayan ta fito daga wanka ta saka wani baƙin leggings, da wata baƙar long sleeve high neck shirt, ta ɗora kimonohnta a kan kayan, sannan ta kawo wani baƙin baby hijjab ta saka. Ba ta yi kwalliya ba, dan da ma ita ba gwanar kwalliyar ba ce. Mai kawai ta shafa a jikinta, sannan ta ɗauki backpack ɗint ta saka kayan sport ɗinta a ciki.

Ta fito ta zauna a danning ta fara cin abinci, sai da ta kusan gamawa sannan Rhoda ta ƙaraso, ba ta yarda sun tafi ba, sai da ta zubawa Rhodan abinci ita ma, Rhodan na ci Rabin na bata labarin ɗan uwan Aliyun da suka gano. Ita kuma Rhodan na ba ta bayani a kan shari’ar da za su shiga gobe.

Da haka har suka gama, sannan Rhoda ta ɗaukesu zuwa can acadamy ɗin. Bayan da Rhodan ta kaita sai ta tafi, tare da faɗa mata cewar; idan sun gama, ta mata waya, ita kuma za ta zo ta ɗauketa.

Rabi ce zaune a kan kujerar jira, sanye take da wannan jerseyn da kum wandonta, wanda ta saka leggings da kuma long sleeve high neck shirt a ƙasansu, ƙafarta sanye da football shoes. Kanta kuma rufe da baby hijjab, yanayin shigar tata akwai gwanin ban sha’awa, dan kaf matan dake wurin babu me irin shigarta, ba za ta ce babu musulmai a cikinsu ba, amma babu bahaushiya ko bafulatana ɗaya a cikinsu, duka ‘ya’yan iyamurai ne. Shi ya sa ita ta fita da ban a cikinsu.

“Rabi’a Muhammad!”

Me tantancewar ya kira sunanta da ƙarfi, hakan ya sa ta amsa tana miƙewa. Inda ya nuna mata ta ƙarasa ta tsaya. Har zuwa yanzu ba ta da wani isasshen kuzari a jikinta, ga cikinta da take jin yana yamutsawa, kamar za ta yi amai. Amma kuma ba za ta bari hakan ya zama ƙalubale gareta wurin cimma burinta ba, ita ta sa kanta cewar za ta iya, kuma da yarda Allah za ta iya ɗin. Za ta yi abun da za ta bawa kowa mamaki, ciki kuwa harda ‘yan uwanta na haɗejia.

Ball aka sa musu a tsakiya ita da wata yarinya da ta karanta sunanta a bayan rigarta, wai ita ‘Chioma’. A yanayin girman jiki ta fi Rabi ƙiba, amma kuma Rabi ta ɗan fita tsayi, gata a ƙasa duf, ta ci doya da tuwon mama Iyabo ta ƙoshi.

A sa’ilin da aka hura usur, a lokacin suka fara gudanar da wasan. Tashin farko sai da Chioma ta ci Rabi’a har sau biyu. Kasancewar ita Rabin babu kuzari a jikinta. Bayan sun ci gaba da wasan, Rabi ta kaiwa Chioma wani yanka, wanda ya sa Chioman ta yi amfani da ƙarfinta ta hankaɗa Rabi gefe. Faɗuwa ta yi, hakan ya sa gwiwar hannunta kurjewa da grass carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin.

Tashi ta yi zaune tana kallon Chioma ɗin. Me ya sa ta yarda kan cewa Chiomar za ta iya kada ta?, ita ma fa macace kamarta, babu wani abu da ta fita da shi, dan kawai ba ta jin daɗin jikinta sai ta saki jiki Chioma ta na nasara a kanta?, ya isa haka! Menene ba ta gani ba a duniya, ta shiga halin da ya ɗara wannan ma, ta ga ƙalubale a rayuwa wanda ba ta taɓa sanin zasu afko mata ba ko da a mafarki kuwa. Dan Chioma tana ‘yar kudu ba shi ke nuna cewar ta fita ƙarfi ba, su ma matan arewa suna da tasu jajircewar, ya kamata ace ta nuna musu hakan.

Cike da ƙarfin hali da na gwiwa ta miƙe tsaya, sannan ta koma aka ci gaba da wasa, wannan karon a zafafe take wasan, hakan yasa ta riƙa cin Chioma har sai da lokacinsu ya ƙare. Couches ɗin dake wajen ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin har yanzu Rabi’an ba ta manta da wasu abubuwa da ta koya daga garesu ba.

“Ina taya ki murna mrs. Zaid!”

Cewar ɗaya daga cikin Coach ɗin nasu yana miƙa mata hannu alamun su gaisa, hannun nasa ta kalla, yayin da take dafe da guwar hannunta na dama wanda ke mata ciwo. Kanta ta girgiza masa tana faɗin.

“Sorry sir, but ni matar aureci”

Hakan ya sa Coach ɗin janye hannunsa a sanyaye.

Daga nan kuma sai aka turasu sashen fara ɗaukar darasi, tun a ranar aka fara musu training kuma ba su suka gama ba sai ƙarfe biyar na yamma.

Rhoda ce ke tuƙa motarta a kan titi, tana tafe tana biya waƙar Dalling Jesus dake tashi a motar.

“I love you so much darling Jesus… My darling Jesus… Darling Jesus…”

Wayarta ce ta yi ringing, hakan ya sa ta faka motar a gefen hanya, tana kashe waƙar. Ganin Zaid ne ke koranta ya sa ta kai hannu ta ɗau wayar tana ɗaga kiran.

“Kina ina ?”

Abun da muryarsa ta fara tambaya kenan bayan da ta ɗaga wayar, amon muryar tasa ya bata tsoro, dan sautin nasa na ɗauke da wani abu me kama da damuwa ko tsoro. Kamar me san tantance wani abu, ta shiga wulƙita idonta a kewayen wurin da take.

“Ƙarfe shida yanzu, na kai Ammatanka gida ne… Kai wai ina ma ka shiga ne?”

Ta ƙarashe tana jefa masa tambayar. Sai ta ji ya yi shiru, kafin yace.

“Ki koma gidan ki ɗaukota, sannan ki kawota Hymill hospital!”

Damm, gaban Rhoda ya buga.

“Zaid! Zaid!. Me yake faruwa?. Ka ga ɗan uwan naka?”

Ta tambaya a kiɗime.

“Ki je ki zo da Adawiyya… Ɗaki me lamba ashirin da shida”

Daga haka ya katse kiran ba tare da ya jira abun da za ta faɗi ba. A hankali Rhoda ta sauƙe wayar daga kunnenta, duk yadda aka yi ba lafiya ba. Dan haka ta tayar da motar da sauri ta juya kan motar zuwa gidan Zaid.

RABI’A POV.

Rhoda na aje ta a gidan ta shiga wanka. Kuma kafin ta bar banɗakin ma sai da ta yi amai, ta rasa abun da yake mata daɗi, ko mai ta ci ba ya zama a cikinta sai ya dawo. Haka ta ɗaura towel ta fito jiki ba ƙwari. Duk da yau tana cikin farin ciki sosai, domin a yanzu ta na ganin labarinta ya gama cika, tun da har Allah ya mallaka mata Zaid a matsayin miji, ya sa mahaifinta shiryuwa, ya ganar da Habiba da ‘yarta Mama tafarki madai-daici, sannan ya nuna mata auren Anti Saratu, ya kuma cika mata burinta na ci gaba da buga ƙwallo. Ita kuwa me za ta ce? Da ya rage ta dage kan ibadunta, don ta nunawa Allah jin daɗinta kan ni’imomin da ya mata.

Ta ƙarashe tunanin tana saka wata doguwar rigar atamfa. Wayarta ta dawo ta ɗauka, ta aikawa Zaid kira, dan ta na so ta ji daga gareshi, tana san ta ji wani hali yake ciki, shin ya haɗu da Aliyun?, ko ba su haɗu ba?. Sau huɗu tana shiga amma ba ya ɗagawa, hakan ya sata shiga mamaki, a gefe guda kuma sai tsoro ya fara shigarta.

Ta kama hanya da niyyar barin ɗakin aka turo ƙofar ɗakin da ƙarfu, Rhodan da ta tafi a ɗazu ce ta dawo, cikin wani irin birkitaccen yanayi da Rabin ta kasa gane masa.

Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja

07:00pm

MISHAL POV.

Zaune take kan wata kujera dake bakin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Aliyu bayan zuwansu asibiti a daren jiya. Abun da likitocin suka rara sanar musu shi ne, ya rasa jini da yawa, haka aka gwada na Zaid, sannan aka ɗiba ganin ya dace da nasa. Kuma tun safe ake ƙara masa jinin. Bai ƙare ba sai da azahar, amma har zuwa yanzu bai farfaɗo ba.

Ita kanta ba ta san in da kanta yake ba, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kawai tana nan ne, amma hankalinta ba ya tare da ita. Tun a ɗazu da safe da suka gama zirga-zirga. Zaid yace mata ta zauna,shi zai tsaya a kan komai. Kuma tun lokacin take zaune a nan ɗin. Babu yanda Zaid ɗin be yi da ita ba kan ta ci abinci, amma fur haka taƙi. Ko sallah ma ba ta jin ta yi. Gani take kamar Aliyu tafiya zai yi ya barta, kamar shi ma zai bi Abbanta, Mamanta da yayanta. Wata ƙila ita ba ta da sa’ar zama da kowa a rayuwa, haka Allah ya tsara tata rayuwar, ba tare da yin zama me ɗorewa da makusantanta ba, wata ƙila haka za ta ƙarar da rayuwarta cikin kaɗaici.

<< Labarinsu 50Labarinsu 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×