You never have to pretend with me, just give me your raw truth, all your imperfections and fears, and i will show you how beautifully broken pieces fit together.
Badawa layout, Kano…
RAJA POV.
Kayan da ya san zai buƙata yake shiryawa a cikin jakarsa ta matafiya. Hannunsa na dama ne ya janyowa wata riga, tahowar rigar ya yi dai-dai da faɗowar wani hoto.
Kansa ya sunkuyar ƙasa, idonsa ya sauƙa a kan fuskokin da ke jikin hoton. Waɗanan lumsassun idanuwan nasa suka kafe hoton suna kallo.
Mutum uku ne a jikin hoton, na farko fuskarsa ce, waɗanan gray ƙwayar idanun nasa ce tasa ya gane hakan, sai kuma fuskar Aliyu, sannan ta Momma, wato mahaifiyarsu. A hankali ya aje rigar, sannan ya tsugunna ya ɗauki hoton, har wa yau bai manta ranar da aka ɗauki hoton ba.
_“Kai Aliyu tsaye daga nan….. Kai kuma Zaid ka tsaya a haka….”_
Wannan shi ne abinda ta faɗi a wancan lokacin. Dariyar da suka yi a wancan lokacin ta shuga amsa kuwwa a cikin kunnuwansa.
Ba shiri ya yi saurin cilla hoton cikin jakar da zai yi tafiyar. Zuwa yanzu hoton ya sauya a idonsa, daga cikin falon gidan da aka musu hoton, zuwa baƙin gidan da wuta ta gama cinyewa.
Wayarsa ce ta shiga ruri, hakan yasa dubansa ya kai kanta. ‘UCHECHI’ Shi ne sunan dake yawo a kan screen ɗin, duk yanda aka yi yasan zuwa gidan ta yi. Rhoda da su Zuzu suka hanata shigowa. Sai kawai ya fasa ɗaga kiran nata ya katse kiran, sannan ya aikawa Rhoda kira.
Daga can harabar gidan kuwa, Rhoda da su Alandi ne suka tare bakin gate, suna zagin Uchechi, tare da faɗa mata ba fa za su barta ta shiga cikin gidan ba.
“Ke ki bar nan!”
Cewar Rhoda tana zare mata ido, Uchechi da ta kai iya wuya, ganin ta kira wayar Raja ya katse mata tace.
“Ba zan tafi ba, sai kun bar ni na ga masoyina…”
“Shgiya ‘yar wahala kawai… Karya me bin maza… A haka za ki ƙare….”
Jagwado ya faɗi cikin muryarsa dake nuna cewa a buge yake.
“Duk abinda za ku faɗa ku, faɗa, ni dai ba zan tafi ba… har sai kun barni na ganshi…”
“Ai ko za ki riɓe a nan… ‘Yar akuya kawai…”
Alandi ya faɗi yana maka mata harara kamar wata mace. Me gadi na daga bayansu yana kallonsu, kusan kullum ita Uchechin sai ta zo gidan. Kuma da zarar su Rhodan suna nan basa barinta ta shiga.
“Rhoda! Let her in!”
Muryar Raja ta faɗi daga bayansu. Cike da takaici Rhoda ta juya ta kalleshi, Allah ya sani ta tsani yarinyar nan, bata santa ko kaɗan.bShi yasa bata san ta riƙa raɓar Rajan.
Kiran wayar Rhoda da ya yi ya ji a kashe ne yasa shi fitowa don ya musu magana kan su barta ta shigo, yasan in har be yi hakan ba za su barta ta shigo ɗin ba.
Uchechi ta yi murmushi cikin makawa Rhoda harara, ta raɓa su ta isa gaban Rajan har da ɗan gudunta. Rungume shi ta yi a kan idonsu, wai duk dam su ji haushi. Shagwaɓa ta shiga masa irin wadda ta saba har suka shige cikin gidan.
Rhoda ta saki wani hucin takaici, ji take kamar ta bi bayansu ta maƙure Uchechin, ta karta har lahira kowa ma ya huta.
“Kar ki damu Rho, muna zaune a nan zamu ji kansu, ke dai ki zuba musu ido kawai, in har ta zaƙe yanzu Raja zai saita mata hanya…”
Zuzu ya faɗi dan ya kwantarwa da Rhodan hankali. Amma sam hankalin nata bai kwanta ba. A duk sanda za ta ga yarinyar kusa da Raja wani irin baƙin ciki ne ke cika zuciyarta. Har addu’a take kan ubangijinta ya bata damar da za ta raba yarinyar nan da haukar dake kanta, don idan aka bata dama, tsaf za ta rabata da wannan rawar kan da take.
“Babe Please ka rabu da waɗanan gajojin, kullum idan zan zo sai sun hana ni ganinka”
Cewar Uchechin, yayin da suka shiga cikin gidan, har suka zauna a kan kujerar falo, sai wani mammane masa take. Shi kuma ya ci gaba da kallonta da waɗanan lumsassun idanuwansa nasa. Amma bai ce mata komai ba.
“Babe magana fa nake”
Ta faɗi tana ƙara maƙalƙale shi. Hannunsa na dama ya saka ya tallafo fuskarta.
“Gobe zan wuce Abuja”
Wannan innocent muryar tasa ta faɗi, yayin da yake kallon idanunta. Shi kansa ya sani abun da yake ba dai-dai ba ne, yasan cewa hatta da taɓa jikinta da yake haramun ne, tunda ba maharramarsa ba ce. Sai dai yana iyaka bakin ƙoƙarinsa ganin basu wuce hakan ba, bayan taɓe-taɓen juna basa ƙetare iyaka. Duk kuwa da yanda Uchechin ke nuna masa cewar hakanfa ba komai ba ne, sai dai shi yasan cewa hakan komai ne.
Dan kuwa ba zai taɓa yafewa kansa ba idan har ya aikata abinda take so ɗin, sai dai kuma yana san Uchechi, shi yasa ya kasa rabuwa da ita. Duk da yanda take nuna masa zalamarta a fili.
“Shi kenan, ni ma akwai abinda nake yanzu, idan na gama zan biyoka Abujan…”
“Sure?”
Ta gyaɗa masa kai.
Kafin ta ci gaba da tattaɓa sassan jikinsa, ganin kamar suna shirin yin nisa ne yasa shi saurin raba jikinsa da nata. Ya miƙe tsaye yana riƙe kansa. Da sauri Uchechi ta miƙe tana rungumarsa ta baya.
“Please Babe, yau kawai, just once….”
“Uchechi, get out!”
Ya faɗi a ruɗe.
“Babe…”
“I say get the hell out of here!…..”
Ya maimaita mata wannan karon cikin ɗaga murya, kamar ba shi ba, don abu ne mayuwaci ransa ya ɓaci.
Nan take Uchechi ta fara hawaye, ta rasa me za ta masa ya fara santa, a ganinta kamar santa ne ba ya yi, dole ne ta koma wurin yayarta Chisoma, dan su san ta yanda zasu ɓullowa lamarin. Jakarta kawai ta ɗauka sannan ta fita. Tana fita Raja ya koma da baya yana kwanciya a kan kujerar.
“Astangafurullah, Astangafurullah…”
Ya shiga faɗi a hankali. Ya rasa wannan wata iriyar masifa ce haka, daga can ƙasan ruhinsa ba ya san hakan, amma kuma wani abu a cikin kansa na faɗa masa cewar ya aikata.
“Rho, ki share mana…”
Cewar Zuzu, yana ci gaba da lallashin Rhoda da ta ƙuntume fuska. Ganin fitowar Uchechi da gudu daga cikin gidan yasa suka miƙe da sauri.
Dan suna cikin wata rumfa ne dake harabar gidan. Har wata ajiyar zuciya ta yi, tana bawa zuciyarta da kanta haƙuri.
“Geti losh!”
Cewar Alandi, a ƙoƙarinsa na ganin ya kwaciɓa turanci. Dariya ta kama Rjida, ta juyo ta kalleshi.
“Ba geti losh ba, get loss!”
Ya sosa kai ya na ɗaga hannu kamar me kai wa duka.
“Sai ni Wallahi!… Hhhhh hajiya Rhoda ai kece ba ki gaɗa dai-dai ba, ki bar gani na a hakan nan, masters gareni a fannin kai sara suka!”
Rhoda ta kwashe da dariya, ranta fes.
*****
No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja
KULIYA POV.
Zaune yake a ɗakin Anna, tun bayan da aka sauƙo a idi ya yi wa gidan dirar mikiya, a ganinsa nan ne kawai zai iya zuwa ba tare da ya yi tunanin aiki ba. Sai dai a yau gidan nata cike yake da mutane, wanda suke zuwa mata barka da sallah, shi kuma na ɗaya da ga cikin ɗabi’arsa, ba ya san zama a cikin mutane. Shi yasa ya dawo ɗakin nata ya zauna, yana karatun wasiƙar jaki. Ƙofar ɗakin aka turo haɗi da sallama.
Jin muryar da ba ta Annaa ba yasa bai ko kalli inda ƙofar take ba, ya ci gaba da kallon inda yake kalla wato jikin taga, har yarinyar da Annan ta aiko kawo masa abincin ta aje a kan side drawer.
“Me ki ka kawo ?”
Kamar daga sama yarinyar ta ji muryarsa ta furta, wannan masifaffiyar muryar tasa, me sa cikin mutum murɗawa lokaci guda. Kuma nan take ita ɗin ma jikinta ya shiga rawa, saboda tsabar abar tsoro.
“A… Anna, ce… ta… tace na kawo… maka abinci…”
“Fita da shi!”
“Amma ta…”
“Ki fita da shi na ce, bana buƙata!”
Cike da bala’i ya katseta, kuma har zuwa lokacin bai kalleta ba. Sum-sum ta ɗauki kayan abincin ta fita da su.
“Gaskiya Anti Karima ba zan iya ba, na gaji da masifar bawan Allahn nan, shi kullum kamar bai san mutane ba, shekara nawa na shafe a gidan nan?, amma ko sunana ma bana jin ya sani…”
Yarinyar ta faɗi rai a ɓace, yayin da ta iske yayarta a kitchen. Wadda take kitsa mata yanda za ta shawo kan Kuliya da ya daɗe a cikin ranta, tun sanda ta zo gidan Annan ta shafe shekaru kusan shida ta faɗa sansa, amma shi ko kallonta ma ba ta jin ya taɓa yi.
“Ke dai Wallahi an yi wawuya, yanzu kina ga na miji irin wannan, za ki na wani cewa kin gaji?… ta ya zabki gaji ?… Namiji irin Kuliya ko yankar naman jikinki yake haƙuri za ki yi ki ci gaba da binsa…”
Yanrinyar mai suna Siyama ta juyar da kanta gefe, har ga Allah ita ta gaji, tun shekaru uku baya take ta fama, amma ya kasa ganewa. Abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, ya kukan uwa mara amfani.
“Ke ba ki ga irin yanda yake hidima da Anna ba ?, to ita da take marainiyarsa kenan, ke kuma idan ki ka zama matarsa ai sai yanda ki ka yi da shi kansa ma ba dukiyarsa ba!”
Antin ta kuma faɗi, murya ƙasa-ƙasa.
“Ke dai kawai ki ci gaba da dagewa, na tabbatar da za ki same shi… Kuma batun rashin sabo za ku saba, ba ki ji sunan sa ba ne ?, Kuliya manta sabo, ko ya san sabon ma mantawa da shi yake. Bare kuma ke da kunnenki ki ka ji Anna ta ce bai taɓa yin budurwa ba!”
Kuliya dake zaune a ɗakin Anna yana kallo da kuma sauraren abun da suke ta cikin wayarsa, wani abu ne me kama da murmushi ya yi playing a cikin ransa. Amma ba za ka gane hakan ba idan ka kalli fuskarsa. Don tana nan cikin yanayinsa na shanu, babu fara’a bare annuri, fuska kamar kunun da ya so gardama. Wato shi za’a yi wa haka ?, bari su saka ido su gani, ko ƙoƙarin Siyaman zai yi aiki.
Unguwar Shuwarin, Maiduguri…
“Wallahi Kalisa nake faɗa miki… Kwata-kwata ba na samun kansa, amma tun da na yi amfani da maganin da Fati ta bani, sai na ga ya yi aiki, amma kuma bai jima ba ya wargaje… Ni na rasa yanda zan yi”
Muryar Hajjara ta faɗi cikin damuwa, yayin da take bayyanawa ƙawarta Kalisa sirrin cikinta. Zaune suke a ɗakin gidan Kalisan, don bayan an sauƙo daga idi ta silale ta bar gida ta iyo nan. Kalisa ta taɓe baki.
“Wallahi ni kuma na ga haukarki… wa ya faɗa miki cewar ana wani biya boka ko malam yanzu?… To ba’a haka, zagewa za ki yi ki nemi ‘yancinki da kanki, da masifa da komai zaki ƙwatawa kanki ‘yanci”
“Ki na ga idan na bi wannan hanyar zan samu kansa ?”
“Da gudu ma kuwa”
Hajjara ta yi murmushi.
“To yanzu miye abun yi?….”
Daga haka Kalisan ta shiga tsara mata duk abubuwan da za ta yi, da hanyoyin da zata bi dan samun kan mijinta da kuma mallake gidanta.
Ba tare da sanin cewa hanyoyin ba za su amfaneta da komai ba, sakamakon ɗaya bayan ɗaya hanyoyin za su ruguje, kuma rugujewar tasu za ta taho ne tare da ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta nan da ‘yan kwanaki masu zuwa. Ƙaddarar da za ta wargaza komai, ta kuma saita wasu abubuwa.
Dambuwa road, Maiduguri…
MISHAL POV.
Zaune take a tsakiyar ‘yan uwanta na gidan Antinta Nimra, hira suke suna cin abinci, dan bayan an sauƙo daga idi su kai tsaye gida suka dawo.
Kowa cikin kwalliyarsa mai kyau, wasu sanye da manyan kaya wasu kuma kayansu ne na al’ada a jikinsu. Mishal ɗin kuma sanye take da wata dark green cargo jumpsuit, daga ƙasanta ta saka farar shirt. Dan duk kayan sallahr da aka ɗinka mata cewa ta yi sun mata yawa.
Shi yasa ta aje su da zummar idan sun koma abuja za ta bawa yayarta Adawiyya. Kuma da ma ita ba wani san manyan kaya take ba, ta fi so tai ta saka ƙananan kaya. A plate ɗaya suke cin abincin tare da kwaise, Arman da Daala.
“Aki mu fita yawo mana idan anjima”
Cewar Kwaise wadda take ‘ya a wurin ƙanin Nimra tana kai loma, Arman ya gyaɗa kansa.
“To ina za muje ?” Mishal ta tambaya.
“Muje Gumalti, daga can sai mu wuce gidan zoo”
Kwaisen ta faɗa tana kallon Arman dake zare wani zare daga kan Narjis, ‘yar iqra ƙanwarsa dake zaune kan cinyarsa.
“Shikenan, yarinya sai ta tanadi kuɗin da za ta kashe, an jima za mu fita!…”
Arman ya faɗa da ɗan ƙarfi, dan sauran ‘yan uwan nasa su ji.
“Ni dai ba wani kuɗi da zan fitar, ina aljihunka”
Cewar Iqra.
“Alƙur’an ba ki isa ba, ga mijinki ai, sai ya biya miki”
Iqra ta juya ta kalli mijinta Adam da suke cin abinci tare.
“Rabu da shi Babe, sai mun kashe sama da abun da zai kashe”
Adam ɗin ya faɗi cikin sigar zolaya.
“Aki, za mu tsaya a hanya na sai fara ”
Cewar Ijaz, yayin da yake cusa abinci a bakinsa.
“Hello! Ban da ni za’a je?!”
Wannan muryar ta faɗi daga bakin ƙofar falon, gaban Mishal ya yi tsalle ya hau kan mountain ever rest sannan ya diro ƙasa. Kallon fuskarsa kawai babban tashin hankalinta ne a duniya, kasancewar a duk sanda za ta kalli fuskarsa ma sai wannan lokacin ya haska a cikin kanta. Bata da tsoro, amma shi tana tsoronsa, ba ma shi kaɗai ba, duk wani abu da ya dangance shi tsoro yake bata.
Ta zabura za ta miƙe tun kan ma ya ƙarasa shigowa cikin falon, Arman ya yi sauri ya riƙe hannunta yana mayar da ita ta zauna. Sannan ya juya ya kalli Yazid ɗin da ya shigo falon.
“Yazid fita!”
Arman ɗin ya furta a dake… Cikin kakkausan amonsa irin nasu na sojoji, babu alamun wasa ko kaɗan a fuskarsa, ya dake ya koma ainahinsa na soja. Sai da kowa ya jiyo ya kalli Arman ɗin, sannan kuma suka kalli Mishal da jikinta ke ɓari, sai ɓuya take a bayan Arman.
“Ai ba…..”
“Ka juya na ce!”
Arman ɗin ya faɗi ya na aje Narjis kusa da Mishal ɗin da numfashinta ya fara yin sama.
“Ok…”
Ya faɗa yana juyawa, babu wani alamun nadama ko kunya a tare da shi, dan ya ci bulis, duk da bai mata komai ba a lokacin, kuma a ganinsa ko da ya mata wani abun babu abinda zai faru, tun da shi na gida ne.
“Ki nustu Mishal, ya tafi, ba ya nan…”
Adam ke faɗi yana san kwantar da ciwon nata, kasancewarsa likita. Idanuwanta sun fara yin sama, ga yanda numfashinta ke fita wani iri.
Abubakar da Arman na gefenta suna mata fifita. A hankali-a hanakli hayyacinta ya dawo jikinta, sai sauƙe ajiyar zuciya take a kai-akai.
“Kin sha maganinki yau ?”
Arman ya tambaya. Kanta ta girgiza masa, shi kuma sai ya gyaɗa mata kai, tare da juyawa ya kalli Kwaise.
“Duba ɗakinta ki ɗauko min jakarta…”
Kwaise ta miƙe tana faɗin to. Hanin Mishal ɗin ta dawo hayyacinta yasa kowa ya koma ya zauna, Mushal ta cure gu ɗaya tana saka babban ɗan yatsanta na dama a baki, tare da fara shan hannun a sace. Dan bata san wani ya gani.
Ko Abubakkar da sha hanata shan hannun, amma ba ta iya denawa, duk da takan jima bata sha ɗin ba, amma duk sanda zai faɗo mata a rai sai ta sha.
“Wai ke Baby har yanzu baki san cewa kin girama ba?… Da ma har yanzu kina shan hannu ?”.
Da sauri ta cire hannun na ta ta na turo baki, tare da juyawa Arman ɗin kai. Arman ya yi dariya.
“Abubakar me yasa baka kaita an cire mata wannan braces ɗin ba ?” Cewar Arman ɗin ya na duban Abubakar.
Abubakar da ke magana da Adam a kan ciwon Mishal ya ɗago ya kalle shi.
“Sai mun koma za mu je a cire mata, dan na ga gap ɗin sun haɗe…”
“Na kwaise kuwa har yanzu ba su haɗe ba”
Cewar Ijaz.
“Ai ba’a wani jima da saka mata ba shi ya sa, na Mishal ɗin fa ya kai shekara biyar, kawaise kuwa ai ko shekara uku bai yi ba”
Arman ya ba shi amsa. Haka hirarrakinsu suka ci gaba da wanzuwa, har zuwa sanda Kwaise ta dawo riƙe da jakar maganin Mishal, Arman da kansa ya bata.
Sannan suka ci gaba da hirar, har zuwa yamma, kowa ya sake kwalliya suka fita zaga gari da yawon gidan ‘yan uwa.