Ita da ma dai Yusuf ɗin ne Ziyada ta ce tana so. Wallahi a guje za ta bashi aurenta. Ba tun yanzu ba take matuƙar yabawa da halayen yaron, yana da kaifin hankali da hangen nesa. A unguwarsu yaron ya samu kyakkyawar shaida, lamuransa na aiki da hankali har sun zarce shekarunsa.
Amma Khamis, inaaaa.. Baza ta cusa kanta a cikin lamarin da tun farko bata yi mishi hangen zai haifar da ɗa mai idanuwa ba. Lumshe idanu tayi a hankali tana tunanin ta inda za ta ɓullo ma Ziyada su warware al'amarin lafiya ba tare da tashin. . .