Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Lokaci Ne by Oum Mumtaz

Acaɓa ya tsaya a ƙofar wani gida matsakaici na masu karamin ƙarfi, Lawal mai kimanin shekaru talatin a duniya ya fito sanye da yadi a jikin sa mai sauqin kuɗi, ɗinkin tazarce kansa sanye da hula hannun sa riqe da baƙar laida, ya sallami ɗan acaɓa ya sanyo kansa cikin gidan su bakin sa ɗauke da sallama fuskar sa a haɗe babu alamun fara’a ko kaɗan.
Kaman yanda yayi tsammani kuwa cikin ransa zaune ya tarda matan yayan sa tare da matar sa Umaima suna hira hankalin su kwance kaman basu da wata matsala cikin rayuwar su. Sallamar tasa ce tasa su dakatawa da hirar tasu da suke yin ta su uku, Umaima dake bama yaron ta Amir Nono ta maida tare da miƙewa fuskar ta na fadaduwa da fara’a tace, “Sannu da zuwa Abban Ameer.”  Ta miƙa hannun ta na dama ta karbi ledar hannun sa inda shi kuma ya karɓi Amir tare da ansa mata Sannun da ta masa, ya sa kansa zuwa kewayen su ta mara masa baya,mata biyu dake zaune a wajen ganin bai kula su ba sai suka hada ido tare da tabe baki suna raka su da harara.
Zama yayi kan kujera cikin parlo yana cire hular dake kansa hadi da share zufar data kwanta masa a goshi kasancewar lokacin zafi ne, Umaima ta samu guri a gefen sa ta zauna hadi da miƙa masa ruwa na pure water mai ƙarancin sanyi tare da faɗin, “Kasha rana Abban Amir, sannu da zuwa, yaya kasuwar.” Fuska a haɗe ya furta, “Lafiya.”
Jin yanda ya ansa mata ne ya sa ta kalle sa a kaikaice, cikin zuciyar ta take raya ko waye kuma yau ya taɓo mata birkitaccen mijin nata da koman ƙanƙantar abu ke baƙanta masa rai?

“Abban Amir yau kuma wa ya tabomin kai ne naga ka shigo ba a yanda ka fita ba? Allah dai yasa lafiya.”

Tayi maganar tana karɓar Amir ɗin dake hannun sa mai kimanin wata takwas haɗi da kwantar dashi a shimfidar sa dake cikin parlo ganin yayi bacci. Tsaki yaja mai ƙaramin sauti cikin dakewar murya yace, “Ina ruwan ki da abinda ya dame ni? Dalla tashi ki kawo min abinci kamin ki sake bata min rai malama.”

Take taji ranta ya sosu da irin amsar da ya bata daga abin arziki, har sai shi da kansa ya karancin hakan akan fuskar ta, amma da yake namijin duniya ne sai fuskewa da yayi ya kara haɗe fuska, tashi tayi zuwa kitchen ɗinsu dake karamin tsakar gidan jikin ta a sanyaye, ta kawo masa abincin ba tare da ta sake furta masa kalma guda ba hadi da zuba masa, daga haka sai ta koma kan kujera 3 seater ta kame kanta shi kuma ya fara cin abincin sa a natse kaman ba shi ba.

Ansa kuwar da wayarta ta soma yi ne ya katse mata ɗan gajeren tunanin da ta tafi, ganin wacce ke ƙiran nata ne yasa ta ɗauka ba tare da tayi jinkiri ba da yar ɗokin ta sabida ba ta saba ganin kiran waya daga mahaifiyar ta ba sabida wasu dalilai tace, “Salamu Alaikum, Ammah ina wuni”

Daga dayan bangaren Salamatu da ta kasance mahaifiya a wajen Umaima da yaran ke kiran ta da Ammah ta ansa da, “Lafiya kalau Alhamdulillah, yakike da maigidan naki da kuma Amir dik Kuna lafiya?”

“Lafiya Lau dik muke ya su Amina?”

“To masha Allah! Kowa da Kowa lafiya lau. Nace kinji labarin gudummawar da aka yanka muku na auren yayar ku ai ko?”

Gaban Umaima sai da ya bada ƙaramin sauti jin maganar da mahaifiyarta tazo mata dashi. Dake wa tayi gudun kar Lawal ya fahimci inda zancen yasa gaba tace, “Eh Ammah, munyi waya da  Aunty Asma’u tin a ranar ta faɗamin.”

Muskutawa Ammah tayi ta gyara zaman ta tare da fadin, “To sai kisan dik yadda zakiyi ki samu ki tura musu a lambar account ɗin da suka tsaida za’a tura kudin, kar kuma na sake naji kinzo da wani uzirin baki dashi kina jina ko?”

Wani kwallon da ya tokare mata makoshi ta hadiye tana danne takaicin dake ta so mata don kar ta Lawal ya fahimci inda zancen ya dosa ta gajarce tace, “Ok insha Allah.”
Daga haka sukayi sallama ta katse ƙiran tana mai tunanin ta inda zata samu naira dubu goma Sha biyar tinda ita ba sana’ar fari ba ballantana na baki da zata bada contribution.
Sai da ya kammala cin abincin sa tsaf, kamin ya miƙe haɗi da cire rigar dake jikinsa tare da wandon ya rage daga shi sai boxes da vest ba tare da yace mata kala ba ya fice daga parlourn zuwa bandaki, wanka yayi sannan ya dauro alwala ya fito jikinsa nannade da towel insa dake shanye akan igiya yana goge jikinsa.

“Umaima shiga daki ki dauko min 3 quarter na baki, da rigar da nake hadawa da ita. “
Lawal yake fadama Umaima a Sanda yake zama akan kujera fuskarsa na washewa daga ɗacin ran da ya shigo gidan da shi.

Umaima da take kwance kan doguwar kujera ta 3 seater tayi rigingine tana kallon ceiling kaman mai son tan-tance wani abin, nan kuwa tunani ne shakare cikin kwakwalwarta sun mata rubdugu, bata san ma ya mata magana ba.
Jin bata ansa masa bane yasa shi kallo inda take, wanda nan take ya fahimci bata jisa ba.

Hakan yasa shi jin babu daɗi cikin ransa, sabida yana da yakinin cewa maganar da ya yaba mata ne yasa ta shiga zurfin tunani domin son gano laifin da ta masa daga dawowar sa gidan tinda dai da safe kamin ya fita lami lafiya suka rabu da juna. Nan kuwa bai san cewa ita Umaima banda damuwar sa, har da nata personal issue da ya zabge nasa damuwar wajen kaso saba’in da biyar cikin cikin dari ba, tunanin ta ya lula can tunanin rayuwarta ta baya ne da suka faru a mabanbantan lokuta.

Wanda hakan yasa ba taji dik kiran da yake mata ba, har sai da yazo inda take ya sanya hannun sa akan fuskar ta da ta daura hannun akan goshin ta, ta dawo hayyacin ta.

“Tunanin mai kike ne ina ta miki magana bakya jina?”

A hankali ta sauƙe karamin numfashi tana nemo ƙaramin murmushi da yafi kama da yaƙe ta yafa ma fuskarta, tace, “Babu komai mai ka gani?”

Zama a gefen ta yayi,hadi da riko hannun ta duka biyu yana mai kallon tsakiyar idanun ta yace,”Ya zaki ce min babu komai, bayan gashi nan fuskarki kaɗai bai nunamin babu koman ba?”

Yayi maganar cike da kulawa tare da damuwa cikin muryarsa, wanda hakan yasa Umaima kallon cikin idanun sa domin son gano cewa wai shin da gaske har cikin zuciyar Lawal yana sonta kuwa? Ya kuma damu da damuwar ta kaman yanda yake nuna mata a lokuta mabanbanta idan wani abun ya haɗo ta da shi?

“Umaima magana nake miki fa baki bani amsa ba kin tsaya kina kallona.”

A hankali tace, “Ba komai bane, dama kawai tunanin abinda na aikata a gareka ne da yasa na cancanci irin wayannan sabbin halaye na bakanta min rai akan dalilai marasa karfi daga gareka wanda a farkon auren mu ba haka na saba gani daga gareka ba. ”
Ta ƙare maganar muryarta na karyewa alamun daf take da fashewa da kuka, domin kuwa ita din na cikin jerin mata ne masu saurin kuka ballantana kuma ga abubuwa dake neman sanya ta cikin damuwa a yan shekarun ta da bata taɓa tsammani ba.
Yaji babu dadi ƙwarai,na ganin ya sanya Umaima zubar hawayen ta akan laifin da ba ita ta aikata masa ba. Matse hannayen ta dake cikin nasa yayi cikin son lallashin ta yace, “Kiyi haƙuri Umaima! Ya kamata ace zuwa yanzu kin gama karantar halayya ta, ta ko wacce fuska, domin kuwa ni ina cikin jerin maza masu saurin fushi da kuma sauƙowa,sannan kuma a lokuta da dama nasha fada miki idan kika ga na shigo gidannan ba a yanayin da na saba shigowa ba ki nisance ni har sai lokacin dani karan kaina na sauƙo na neme ki domin gujewa bacin ranki kema, tinda kinsan cewa idan raina ya ɓaci bana iya fahimtar ko wani irin abu har sai ni da kaina na sauko daga dokin zuciya, amma kiyi hakuri insha Allah zanyi kokari wajen na ganin na sauya halaye na. “
Dan ƙaramin murmushi tayi dik da bai kai cikin zuciyar ta ba tace, “To shikkenan komai ya wuce, nima kayi haƙuri akan rashin fahimtar ka da nayi.”

“Ni dama baki min komai ba, wani ne daman ya batamin rai a kasuwa, amma yanzu naji raina ya huce, kuma nasan ba komai bane ya kawo hakan sai don kasancewa na tare da hasken rayuwa ta Umaima.”

Ya ƙare maganar cike da soyayya a lokacin da ya janyo ta jikinsa, sai kuma labari yasha bamban.

Sai da suka sami natsuwa, Lawal ne ya fara wanka, sannan Umaima ma ta shiga, wanda Amir dake bacci ya farka da kuka sosai kasancewar sa yaro mai tsananin rigima, Lawal ya ɗauke sa yana lallashin sa amma kaman wanda ake kara zuga sa, a gaggauce Umaima ta fito jikin ta ɗaure da zani, karɓar sa tayi ta zauna kan kujera ta fara basa Nono, Lawal ya zauna a gefen ta yana dungure masa kai a hankali yace,  “Amman dai Baba baka yimin adalci, ai idan wannan wani ne ya dauke ka bani ba wani sai yayi tunanin mintsinin ka ake yi, wai kai ma yaro ƙaramin da kai kasan uwarka wato tana karɓar ka har da yin shiru amma ni babu yanda banyi da kai ba, sai sake kara volume din kuka kake tsabagen sharri uwarka tace ban dauke ka ba dan naga bata nan? “

Cikin dariya Umaima da zuciyar ta ke cike da kaunan ɗan nata mara misaltuwa tace, “Kai dai Abban Amir, mitan naka ya isa haka nan kar ka sakamin yaro a gaba dan Allah, kuma ma ai ba laifi yayi ba da gaskiyarsa babu yaron da zai farka kaman Amir bai nemi Maman sa ta basa Nono ba.”

Tashi Lawal yayi ya shiga dakin su yana jin dadin ganin Umaima ta sake sosai kaman yanda yake so yace, “Kudai kuka sani.”

Kaya ya saka ya fito ya tafi masallaci jin an kira sallar azahar Umaima ta bisa da addu’ar dawowa lafiya,sannan ta zaunar Amir wanda har rarrafe yake kokarin yi ta shiga daki ta saka kaya, sallaya ta shimfida, sai da ta idar da salla sannan ta zuba abincin ta taci, wanda yau basu samu damar ci tare ba kaman yanda suka saba.

Tunanin hanyar da zata samu kuɗin contribution ta fara wanda hakan yasa taji damuwar ta na dawowa sabo fil, tana tunanin ta yanda zata sama ma kanta mafita sabida tasan halin Ammah sarai, akan wannan contribution din da ba farilla ba sai ta iya yin dogon fushi da ita fiye da tunanin mai karatu, wanda ita Umaima damuwar ta shine inda ace cewa sukayi kowa ya bada abinda yaga zai iya dai-dai karfin sa bata da damuwa, amma wai su wani ce sai 15thousand ko tunanin masu ƙaramin karfi kamar ita da wasu daga cikinsu tinda ba dika aka taru aka zama masu arzikin ba basa yi, sai shegen iyayi irin na Aunty Halima za ta wani ce ga abinda zasu bada sabida ita tasan nata mijin mai arziki ne sannan kuma tana aikin gwamnati tana daukar albashin ta? Wayarta ta dauka ta kira lambar da tayi saving da ‘Maimuna’, sabida tunanin zata iya samun mafita a wajen ta kasancewar ita kaɗai ce yar uwarta a gidan su da take iya baje mata kolin matsalolin ta su hadu su samo mafita ba tare da ɗaya daga cikin ahalin gidan nasu ya samu labari ba.

“Salamu Alaikum.” Umaima ta furta a sanyaye jin an ɗauki wayar.
“Wai Alaikumussalam, Uwar Amir yakike ya yaro na?”
“Lafiya Lau Alhamdulillah ina Kamila?”
“Yanzu suka fita da Baban ta sunje rakiyar abokin sa.”
“Tou yayi kyau a gaida min ita da Baban ta idan sun dawo.”
“Insha Allah zasuji, ya shirye-shiryen Salla?”
“Alhamdulillah muna ta fama.” Wanda Umaiman ta fadi hakan ne ba wai don da gaske shirin take ba.
“Wai ya naji muryar ki tayi sanyi kaman baki da lafiya? Ƙalau kike kuwa?”  Maimuna ta tambayi Umaima cike da kulawa.

“Wallahi daman kiranki nayi akan sha’ananin auren Aunty Hamida, nasan kinji labarin gudummawar da suka ce kowa zai bada, kin kuma fi kowa sanin bani da wannan kudin, sannan kuma bani da dalilin samun su, shine na kiraki dan Allah ki bani shawarar yanda zanyi sabida na tabbata idan ban bada wannan kudin ba Ammah da sauran yan gida baza su barni nasha iska ba, sun dinga yabamin baƙar magana, kuma kinsan ni ba hakuri ne dani ba idan ba Ammah da Umma ba (Kishiyar Ammah) babu wacce zan ɗaga ma kafa sai na rama idan aka fadamin baƙa.” Ta ƙare maganar cike da damuwa.
“Hakane kam dole ki shi ga damuwa,sannan kuma kin tambayi shi Lawal ɗin yace miki bazai baki bane ko kuwa?” Maimuna ta tambayi Umaima.

“Ina tunanin kin riga da kinsan halin sa, ko nace masa ya bani bazai bani ba sai dai ma raina yazo ya ɓaci a banza shiyasa ban tinkare sa ba sabida gujewar matsala.”
“Hakane kema kince wani abu, amma kuma da ki gwanda tambayar tasa kar muje mu yanke masa hukunci babu hujja a hannu, idan kuma yace bazai bayar ba ne sai musan yanda zamuyi amma in Allah ya yarda zaki bada gudummawar nan, sai an baima masu zuba idon ganin yaya za’a ayi kunya.”

“To shikkenan in Allah ya yarda zan tambaye sa, sai munyi waya daga baya.” Daga haka suka yi sallama Umaima tana jin ɗan relief a zuciyarta kan wannan lamarin.

Oum Mumtaz

Fitattu Biyar

3 thoughts on “Lokaci Ne 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×