Cikin gigin barci ta yi gefe tana rike cikinta, shi kuma ya cigaba da akllonta tamkar mayunwacin zagi, zuciyarsa na zalbaba kamar ya fiddo ta ya jefa a kogin kankara, wai har shi ‘yar wannan abin za ta yiwa fyade? Yo fyade mana tunda bai ga dalilin da za ta fado masa daki ba ta jefar da zaninta da gangan, amma kam da sannu zai shayarta mamakin da zata manta kalar fuskarsa, yana cikin wannan tunanin ya ji kara kamar an kunna tukatukan da ya shekara goma baya aiki ya cika masa kunnne, ya dan matsa inda take ya ga. . .