Nasir ne zaune a cikin office dinshi , yayin da abokin shi Umar ya kawo masa ziyara Wayar Umar ta fara ringin, ya kalli wayar dake bisa teburin aikin Nasir da yakan iya ganin me kiran Sannan ya kalli Nasir yana cewa . "Mutuniyar ka fa ke kira. Dan Allah ka bawa yarinyar fuska , wallahi tana san ka ." Nasir kawai yaja tsaki tare da jan bakinsa yayi shiru Hakan baisa Umar jin haushi ba , ya sake cewa dashi . "Yanzu dan Allah to sai yaushe ne za kai aure, dukkan abokanmu sun yi aure , amman kai ko a jikinka , bayan ga yarinyar nan. . .