Skip to content
Part 20 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

LITTAFI NA HUDU

Sai da Babana ya dawo ne magana taso ta lalace, don kuwa cewa yayi ba zai karbi kayan Ahmad ba.

Shiru nayi a daki cikin wani yanayi, yayi ta fada dalilin da yasa Umma ta bari aka sauke. Itama dai bata ce komai ba, Yaya Auwalu ya kira yace ya nemo mota a mayar da kayan ba ya so. Ganin haka ne yasa Baba Ladi diddingisawa ta same shi ta ce wai wannan fadan da kake yi na meyene?

Na jin haushin yayi wa Mahaifiyarshi biyayya ya saki Maijidda iye? Ina tambayarka?”
Ya ce, “Subhanallahi Haj…” ta ce, “Kada ka ce min komai, idan ba haka ba to menene?
Na ce me yayi maka? Ai bai yi maka komai ba in baya ga hakan. Haba! Wane irin abu ne haka, ka sa a mayar mishi da kaya kayi abin kunya ka tonawa kanka asiri ya gane abinda yayi ya bata maka rai kai ka sani.” Wai! Shiru Babana yayi ya koma daki, ni kuma na dan ji dadi don kuwa har a yau bana jin haushin Ahmad.

Gagarumin biki muka yi, cikin wadata don kuwa abinci kala-kala aka yi, fate, shinkafa fara da miya, dafa duka, alala, tuwon semo da shinkafa da miyoyi daban-daban.

Ga kuma masa, kowa yana cin abinda yaga dama ne.

Ta bangarena kuwa kwalliya nayi bana wasa ba, don kuwa dinkunan da Ahmad ya aiko min da su na saka, sun kuma amshi jikina tsaf.
A gidan da Yaya Auwalu ya karba haya aka saka Amarya wanda yake daf da namu.

An kuma watse biki lafiya, kowa ya tafi in banda Baba Ladi wacce take zaune saboda asibitin da zata fara zuwa, saboda ciwon kafa da ke damunta.

Hakan yayi mun dadi ba kadan ba, don kuwa katifata na dauko na dawo da ita dakin Baba Ladi.

Wani lokaci sai mu kai karfe sha biyun dare muna hira tana bani labarin mijinta da ya rasu. Mahaifin Babana da irin gwagwarmayar da ta sha da kishiyoyinta da a yanzu suka zame mata ‘yan uwa.

A duk sanda ta bani labarin su sai na ce oh, amma dube ku Baba Ladi kamar ba ayi irin wannan zaman ba.

Sai tayi murmushi ta ce, eh to wanda ya hada ma ai ya raba tunda ina yake? Bana shekaru ashirin kenan dukkanmu kuma muna nan, ko wace ce zata fara bin shi a cikinmu? Sanin gaibu sai lillahi.

Na ce, amma fa ni sai nake gani kamar gara mun matsalar kishiya a kan ta uwar miji.
Baba Ladi ta waiwayo tana murmushi ta kalle ni ta ce, saboda matsalar uwar miji ce da ke ko? Amma in ban da haka ai matsala bata wuce kishiya ba. Sai dai idan kawaiba ka da fitinanniya.

Ba zan yi musu da Baba Ladi ba da na gaya mata cewa ita kishiya duk fitinarta ai ba za ta saka mijinka a gaba ta ba shi umarnin sakinka ya kuma sake ka din ba, kenan dai da bambanci.

Kwanci tashi babu wuya sai dai kawai idan Allah bai kaddara maka ganin gobe ba.
An wayi gari ne a yau na gama Iddah ta. A karo na Rarshe kuma da nayi nufin fuskantar gaskiya game da maganata da Ahmad ta kare.
A daren jiya kuma na kwana ne ina tunanin abin da ya kamata nayi shi ne, komawata Makaranta wanda nasan da wuyar gaske Babana ya bar ni.

Umma dai ina ta yi mata maganar cikin dabara nake 6ullo mata da kuma muhimmancin karatun ‘ya mace da kawayena irin su Sadiya Tanimu. Wacce a yanzu take aiki a babban asibiti, ta gama karatunta na aikin jinya.

Umma ta ce, eh hakan yana da kyau amma ai kuma naga bai kai darajar aure ba.
To gaskiya Umma ta fada, don kuwa ko ba komai ai gani da Abulkhairi da ke can tare da Babanshi.

Yanzu shekarunshi hudu ne har da watanni. Idan da na haihu a gidan Ahmad da yanzu abinda na haifa yayi wayo.

Tuna abinda ya faru da ni da cikina a lokacin yasa zuciyata tayi mun wani iri. Amma har yanzu Sadiya tana nan bata yi auren ba tukunna. Ganin yadda Ummata ki maganar makarantata yasa jikina yayi sanyi da yawa.

Anya Babana zai yarda kuwa? A wancan karon ma ga yadda muka yi da Babana to ballantana kuma yanzu. To amma duk da haka Makarantar ita ce mafita a gare ni, tunda dai karatu ba ya hana aure. Sai dai ta ya ya zan bullo mishi?

Muna zaune da Baba Ladi a tsakar gida hantsi muke sha, yayinda nake shafe mata kafarta da wani mai da aka bata a asibiti. Muna kuma ‘yar hirar mu mai dadi. Umma ce a kicin, kokarin damawa Baba Ladi kunun tsamiya take yi.

Saboda wai bakinta da baya mata dandano. Wayata tayi kara, na dauka. Ahmad ne sai dai jikina a sanyaye na dauka na shiga daki don kada Umma taji ta gane da shi nake magana.
Bata hana ni magana da shi ba sai da kuma a yanzu da na gama Iddah menene alakata da shi?

Wannan ita ce tambayar. Har ta gama kararta ina rike da ita a hannuna ban dauka ba. Ta sake fara wani sabon rurin kamar kada na dauka amma kuma sai na kasa.

Sallama na fara yi mishi tare da gaishe shi, sannan muka yi shiru kamar dai ba kudi ne ke tafiya ba. Shirun ne yayi yawa na ce ya kasuwa?

Ya ce, Lafiya Hauwa’u, na kira ki ne naji lafiyarki.” Na ce, To na gode. Na ajiye wayar ina jin haushin abinda yasa na dauka.
Shiryawa nayi da daddare na nufi gidan Yaya Auwalu, don nayi mishi magana kan Makarantata. Don nasan idan ya nunawa Babanmu yana da ra’ayi a kan karatuna babu mamaki nayi nasara ya sassauto.

Matarshi na samu Samahatu tana ta hidimna dashi tana kokarin hada mishi abincin dare. Sha’awarsu ta kama ni.

Yaya Auwalu yayi sa’ar mata nitsattsiyar yarinya, ga kunya da kirki. Cikin girmamawa ta gaishe ni ta juya tana hado wani abincin. Kasancewar kicin din ta falo yasa Yaya Auwalu ya ce idan Hauwa’u za ki hadowa abinci bar shi zamu ci a nan.

Ta ce, To don haka ta miko min cokali na saka a plate din Yaya Auwalu muna ci tare.

Sai da muka gama cin abinci sannan na ce Yaya wurinka nazo. Dukkan nutsuwarshi ya tattaro ya zuba mun ido ya ce lafiya dai ko?
Na ce, Lafiya kalau, ya ce, “To Alhamdulillahi muje waje?” Na ce, A’a zamu iya yin magana a nan babu komai ai. Duk da haka sai da Samahatu ta shiga daki har da ce matan da nayi tayi zamanta kawai.

Na dan yi mishi ‘yan bayanan da zan yi mishi kan bukatata ta komawa Makaranta, da kuma muhimmancin hakan a wurina idan an bar ni.
Karshe nayi mishi bayani mai gamsarwa kan hakan ba zai hana ni aure ba idan damar hakan ya samu.

Ya dan yi shiru ya ce, “To ai matsalar a wajen Baba ne da kyar zai yarda don ba ma zai kalli abin ta wannan bangaren ba. Kuma ni nasan yana da gaskiya don kuwa karatu tuntuni ba a yishi ba sai yanzu ne za a tsiri yi Hauwa’u zai yiwu?

Na ce zai yiwu Yaya, ai komai sa kai ne idan mutum yayi niyyar yi. Ya ce, To haka ne.
Muka fito da Yaya Auwalu yana rakoni gida muna ‘yar hirarmu. Kwata-kwata ban kula na ganshi ba, Abdussamad ne. sai da naji suna gaisawa Yaya Auwalu.

Na daga kai na hango shi tsaye kofar gidansu, hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi. Duk da dare ne bai hana ni gane cikar da yayi ba. Ban ce mishi komai ba gida kawai na shige ina tuna rabona da ganin Abdussamad tun kafin aurena da Alhaji Ahmad.

Kwanaki biyu ne bayan nan ya shigo dakinmu ya same mu muna hira da Baba Ladi, ya zauna. Mun jima muna hirar dashi sai da ya fara shirin tafiya ya ce, to ke idan aka ce an bar ki ki koma makarantar daga ina za ki faro?
Cikin sauri na kalle shi na ce, Yaya Baban ya bari ne? ya ce, eh ya yarda amma kin san ba ki da takardar Secondary school ko?

Na ce, eh. Ai niyyata na koma daga inda da ma na tsaya, wato SS 2. Ya dan yi shiru ya ce, To amma me yasa ba za ki yi extra moral classes ba sai ayi miki register ki rubuta WAEC da NEC0.

Yayi min register gaba daya har da kuma reciept na biyan extra moral classes. Na tsaya bayanin murnar da nayi ma batawa ne kawai. Haka nan shi kanshi Yaya Auwalu yayi ne don naji dadi.

Tunda ba wani kudi ne da shi ba, dawainiya tayi mishi yawa, a yanzu mafi akasarin hidimar gidanmu a kanshi take, ga kuma na gidanshi.

Ban san dalili ba sai kawai naji tamfar an yaye min dukkanin matsalata. Ban wani bata lokaci ba a washegarin ranar ne kawai na fara zuwa daukar karatuna don fara shirin zana jarrabawar shaidar gama Secondary school.
Kwanaki kadan da fara zuwana karatu na dawo da yamma ina shan furar da na samu Baba Ladi ta ajiyc mun. Sai kawai ga dan aika wai ana sallama da ni a waje. Mamaki ya matukar kama ni.

A sanina dai ban taba kula wani ba tun gama Iddah ta, na ce ma dan aiken waye ne?
Baba Ladi ta ce, mu ki ke tambaya ko shi da aka aiko? Yarinya tayi aure ta zauna a dakinta wani sanabe wai zata yi karatun da da can ba a yi ba.

Nayi lullubi na fito na bar Baba Ladi tanata sababinta. Hango wata dalleliyar mota nayi sai kashe ido take yi, sai dai tun. daga nesa mamaki ya kama ni, Ishak ne.

Na kama baki ina mamaki tare da murmushi a raina dai ina cewa to wane irin kudi wannan mutumin ya samu haka?

Na karasa inda yake na ce, To ya ba ka karaso ba ku gaisa da su Umma. Ya dan yi murmushi ya ce, Hajiya Hauwa’u kenan ai sai na samu fuska a wurinki tukunna kada nayi karanbani.
Komawa nayi na sanar da Umma zuwan Ishak, na jawo tabarma nayi mishi shimfida tare da ajiye mishi ruwa.

Suka gaisa da Baba Ladi da Umma, sannan ya koma motarshi ya zauna. Nima can na sake binshi. Na tambaye shi Yaya da yaran duka, Ya ce suna nan kalau.

Satin can ma ina Kaduna tare da su na ma sanar da su cewa zan zo, Yaya ta ce na gaishe ki sosai.

Na dan yi murmushi don kuwa raina yana son Yaya. Ya dan kalle ni ya ce, Jininku ya hadu da na Yaya.

Na ce, To ya harkoki da iyali?

Ya ce, “To harkoki kam mun gode Allah, amma iyali kam ai kema kin dai tambaya ne kawai don jin baki? Ban ja zancen ba a nan na bar shi don ba doguwar magana nake nema ba.

Bai wani jima ba ya sa hannu a aljihun mota ya dauko kudi masu auki ya miko min. Na kalli kudin na kalle shi na dan girgiza kai na ce a’a na gode.

Ya zuba min ido yana kallona ya ce ba za ki kar6a ba saboda me?

Na ce, saboda ba ni da bukatar su. Take yanayinshi ya canza alamar ranshi ya sosu, ya ce to amma ai ko ba ki da bukata da sai ki karba don na gane ina da mutunci a wurinki.
Ba na ba ki ki ki karba ba, tunda nima ban ce kina da bukatar su ba, kyauta ce nayi niyya.

Nasa hannu na karba tare da cewa, Na gode.
A tsakar gida na samu Umma da Baba Ladi suna ‘yar hirarsu da alama kuma kan zuwan da Ishak yayi ne.

Baba Ladi ta ce, To ina tabbatar muku dai wannan mutumi idan ko me yazo yake nema ta tattara a kuma daura mata aure da shi ta koma ta rike danta.

Tunda ma da alama a gidanshi nata arzikin yake, ba gashi shi wannan da ta aura ba ‘yan rabuwarsu bata haihu ba.

Sannan shi mutumin da yayi saki ya dawo yake neman a komai ai alama ne na zai gyara kuskurenshi na baya.

Ina jinsu ban ce musu komai ba haka nan ban ma nuna musu kudin ba, don kuwa nasan halin Umma.

Da daddare bayan mun idar da sallar Isha’i, hira muke yi da Baba Ladi ta kara sako mun zancen Ishak da zuwan da yayi.

Na ce, kai Baba Ladi kenan, kuma kawai daga mutum yazo ba ki san abinda ya kawo shi ba sai ki ce a bishi a sasanta. Saboda zamana ya ishe ki ba kya son ganina ko ya ya? Ta ce, a’a ba fa haka nake nufi ba, zato nake ko maganar komawarki ce ta kawo shi?

Na ce, To ba haka ba ne, ranar da yazo a kan maganar ko-men zan kawo shi wurinki.
Ni kaina nasan zamana a gida baya yiwa mahaifana dadi, to amma lalura idan ta samuu mutum hakuri yake yi da ita, ya jira lokacin da Ubangiji zai warware mishi ita.

Wannan yana daga cikin dalilin da yasa na dukufa wajen ganin na dage na samu nasara a kan karatuna.

Kyakkyawan shiga nake yi ta mutunci a duk lokacin da zan tafi Makaranta. Dogon hijabi nake sakawa, haka nan ko a Makaranta bana shiga harkar kowa.

Karatuna kuma nake yi bil hakki da gaskiya. Yau ma fitowa nayi zan tafi Makaranta cikin kyakkyawan shiga. Har na hauro saman layinmu, daga kan da zan yi sai muka hada ido da Abdussamad da ke tsaye kofar shagon askin unguwar.

Shima ni yake kallo, ban tsaya ko tunanin gaishe shi ba wucewa ta kawai nayi. Sai dai a raina tunani nake yi abinda ya dawo da shi cikin ranakun aiki.

Tunda a sanin da nayi yana zaune ne a Abuja inda yake aiki a Ma’aikatar Sufuri. Tun a wancan karon da yaro yayi mun rashin mutunci ya fita mun a ka, don haka a yanzu ma babu ruwana da sh1.

Sati guda cif da zuwan Ishak, sai kawai gashi ya dawo abinda a take ya fassara min abinda yake nufi. Ko da dai bai budi baki ya furta ba. Nima kuma ban ce mishi komai ba, baya ga fitan da nayi ya gama maganganunshi ya sauke min kayan masarufi iri-iri.

Na shiga gida bayan tafiyar shi. Tun daga shigana jikina yayi sanyi saboda yanayin kallon da Umma take yi mun. Daga nesa kadan na nemi wuri na zauna, amma na kasa sukuni.
Bata ce min komai ba, aikace-aikacenta take tayi. Bayan ta gama ta shiga daki ne naji ta kira ni. Har a lokacin fuskarta bata washe ba. Ta zuba min ido a durkushen da nake ta ce “Za ki koma gidan shi ne?

Tambayar tayi mun wani iri, cikin sauri na dago kaina na kalli Umma da itama ni take kallo.

Idan za ki koma gidan shi ne ki fada saboda na sanar da Babanku tun kafin ki karasa zubar ma mutane da mutunci.

Cikin sauri na ce, “Umma kiyi hakuri ba izinina yake nema yake zuwa ba, ganinshi kawai nake yi.

Ganin shi kawai ki ke yi shi mahaukaci ne? kina nufin idan da bai ga fuska a wurinki ba za ki ganshi?

Tunda ki ke abubuwan da ki ke yi a gidan nan ban taba ce miki komai ba, amma ki kwan da sanin cewa a wannan karon kada ki sake fitowa ki dawo gidannan ki zauna.

Hakan yana nufin sabon aure ne ko kuwa ko-me don abin ya ishe ni haka, sannan na baki kwanaki kadan mutumin nan ya daina zuwa gidan nan ko kuma na shaidawa Babanku don ya sani.”

Dawowa daki nayi na zauna ina sakar zuci. Ni kaina. nasan komawata gidan Ishak ba mai yiwuwa ba ne, idan ba dole ya zama mun ba.
Haka an a yanzu da na samu aka lallaba Babana ya hakura ya bar ni na komna Makaranta wani abu yazo yayi sanadin da damar ta subuce min ba zan so ba.
Hakan kuwa yana nufin da Babana ya ji labarin zuwan Ishak, to zai dauki mataki, ne kawai a kai.

Ilai ko ba a cika sati guda ba wannan karon sai gashi ya dawo, abinda ya tabbatar mun da maganar Umma da tace fuskata ya gani.
Na shiga dakin Umma tana kara gyaran gadonta na ce, “Umma Ishak ne yazo. Ta ce, To menene kuma nawa a ciki? Na ce, eh dama na zo ne na gaya miki.”

Ba ta ce mun komai ba, na juyo na kamo hanyar fita waje. Yana hango ni ya saki mumushi.

Al’amarin Ishak har mamaki yake bani, idan na tuna irin zaman da muka yi da shia matsayin mata da miji.

Uhum, wasu mazan ma dai sai a bar su, basa taba sanin darajar matarsu a lokacin da take zaune a gidansu har suyi tunanin ya kamata su mutuntata don ta ji dadi.

Har sai ta subuce musu kuma sai su zo suna ta faman kame-kame. Muna gama gaisawa na ce mishi amma dai ya kamata ka san wannan zuwan da ka ke yi ba shi da ka’ida.

Don kuwa idan har Babana ya ji labari ka san ba zai ji dadi ba.”

Ya dan yi murmushi har sautin murmushin nashi ya bayyana, ya ce, “Eh ai babu wata matsala, don kuwa Kawu ne zai zo jibi a kan maganar saboda a yi komai nan ba da dadewa ba.

Ba karamin bugun zuciyata maganar Ishak tayi ba. Na dago kaina cikin mamaki da niyyar nayi mishi magana. Sai kawai yaci gaba.

“Kada ki samu damuwar komai, don kuwa na dauka wannan auren da ki ka yi wata gada ce ta halal ta mun ke don ki sake zama matata. Ina so ki san har a yanzu ina sonki, na rantse miki kuma na kasa yin wani auren ne saboda kullum addu’ata bata wuce na ki dawo gidana mu ci gaba da zamanmu ba cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

Kuma kema nasan kina sona, natsala ce dai muka samu tare kuma da kaddara da tsautsayi.”

Takaicin Ishak ya kama ni, naji kamar na shake shi na gana mishi azaba ko na samu na huce,

Tun da ya fara magana shi nake kallo har yayi shiru sannan nace ba addu’arka ce ta karbu aurena da Ahmad ya mutu ba. Don kuwa ba sakina yayi bisa son rai da wulakanci ba, irin yadda kayi mun.

Sannan ban taba sanin cewa tunaninka zai baka ni din zan kashe aure don na dawo gidanka ba. Ina so ka san babu tsautsayin da zai sani yin hakan a yanzu. Nayi wani auren naji yadda ake ji.

Na shaki iskar ‘yanci da mutunci. Mijina ya kula dani ya bani lokacinsa bai taba fita ya bar ni ya dawo mun da tsakiyar dare ba.

Wani abu bai taba hada ni da shi ya zage ni ya zagi talaucin iyayena ba. Ban taba yi mishi wani kuskure ya wulakantani ya gana min azabar duka irin yadda ka rinka yi mun a gidanka ba.

Amma kai fa duk wadannan abubuwan a gidanka suka same ni. Kana ganin kenan zan sake dawowa gidanka da har ka ke karambanin turo magabatanka gidanmu?

Jikinshi a sanyaye ya ce, “Haba Hauwa’u, ina ce duk wadannan abubuwan sun faru ne bisa kuskure kuma sun riga sun wuce.

Na ce, “Eh na sani sun riga sun wuce, amma wucewar ba yana nufin zan sake tsoma kaina cikin fitina ba ne. Kayi hakuri amma ni har na fara shirye shiryen komawa Makaranta.”

Ya ce, “To amma Hauwa’u ai nayi miki alkawura da yawa a baya da nake burin ganin na cika miki su a ciki har da komawarki makaranta.

Na kuma yarda da kura-kuraina, na kuma yarda zan gyara.

Na ce, Eh babu damuwa idan ka gyara nan gaba, amma ni kam kayi hakuri.

Kaje kayi aurenka don kaima ka saukakewa kanka damuwa.”

Ishak bai yarda da abinda na gaya mishi ba, don kuwa sai da ya turo magabatanshi.
Ba karamin godiya nayi wa Allah ba da ya taimake ni na yiwa Umma bayanin komai a ranar da Ishak din yazo.

Babana kuma ya gaya mishi shi a yanzu ba zai tursasa mun auren kowa ba. Idan mun sasanta a tsakaninmu to shi kenan shi ba shi da matsala duk wanda aka yi. Ban kara tsayawa sauraron Ishak ba idan yazo, yazo har ya gaji. Kullum kuma yazo ya aiko a kira ni hakuri nake ba shi na ce mishi ba zan samu fita ba.
To ya dan kwana biyu yanzu bai zo ba.

Wani lokaci sai na ce ina ma da Ahmad ne ya dawo? Zan iya hakura na juya mishi baya haka kuwa duk da matsalar mahaifiyarshi da ‘ya’ yanshi? Zuciyata har yanzu shi take so.

Dan saukin abin ma shi ne, na hakura abin kuma ya rage damuna.

Na kara fuskantar al’amuran karatuna gadan-gadan har muka fara zana jarrabawa ban fuskanci wani tsanani mai yawa ba.

Sakamako ya fito nayi nasara sosai, don a yawan shekarun da nayi bana karatu ban yi zaton zan samu result mai kyau haka ba.

WAEC na samu credit biyar, sai NECO na samu shidda kuma a darussa masu muhimmanci.

Kasancewar na ubuta har da JAMB sai abin yazo mun kusan lokaci daya, don kuwa JAMB din ma babu laifi an bani (Education English).
Ranar murna a wajen Babana ba a cewa komai, to ballantana kuma Yaya Auwalu. Yana fama da asibitin matarshi saboda laulayin da take yi, amma ba ya gajiya da tawa dawainiyar.

Kullum kuma muka dan zauna zai gaya mun ban da yawan yin kawaye saboda yadda ake maganar ‘yanmatan Jami’a.

Watanni uku ne kawai bayan nan sai gashi har mun yi registration mun fara halattar aji don daukar darasi.

Da iyakacin karfina na dage nake karatuna saboda a yanzu shi ne abinda na tasa a gaba don ganin bukatata ta biya.

A cikin sati guda da fara zuwana kuwa tsakanina da kowa a ajin to gaisuwa ce ta mutunci.

Ban ma ba da fuska ba saboda irin suturun da nake amfani da su na mutunci wanda yasa ake zaton ina da aure.

Na yarda da gargadin da Yaya Auwalu yayi min, don kuwa a yan kwanakin fara zuwa Makaranta da nayi naga yadda wasu ‘yanmatan suke ballagazar da kawunansu. Wai su ga hadaddu wayayyu, kaga budurwa takai ta kawo amma tana yawo da ‘yar fingilalliyar riga da matsattsen siket har ana ganin shatan pant dinta.

Sannan babu gyale na mutunci ko hijabi, kuma wai yar Musulma abin abin bakin ciki. Yaya Auwalu dogayen hijabaí ya dunka mun masu kyau har guda shida kala daban- daban, ya ce gudunmawarshi kenan.

Ganin irin abinda ake yi na holewa ga wadansu ni kuwa ban yi wannan wayewar ba kuma bana fata sai akwai nake wucewa library idan an yi break ko kuma na shiga cafë idan ina da assignment din da zan yi.

A gida kuwa har Umma sai ta kara tattalina. A duk sanda na dawo zan zo na samu abincina kammale cikin food flask da dan abin sha.

Haka ma Baba Ladi duk da sanin da tayi ana ajiye mun abinci itama duk abinda taci sai ta ajiye mun nawa.

A yanzu bani da matsalar komai tafiyar da al’amurana kuma nake yi cikin jin dadi, duk wani nauyi ya sauka a Zuciyata.

Ban taba tuna Abulkhairi naji fargaba ko rashin dadi ba don nasan yana hannu mai kyau. Yaya mutuniyar kirki ce da ta san girma da mutuncin kowa, da ace haka kaninta yake, to da al’amarinshi yayi dadi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 19Mai Daki 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×