Skip to content
Part 22 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Ban ko tsaya jiran wani darasin ba, fitowa nayi daga makaranta na wuce gidan su Nasiba.

Babban gida ne sosai irin na masu kudin da, sai dai gini ne na bulo amma sashe-sashe. A yadda kuma Nasiba ta gaya mun to a gidan nasu kaf dinshi ita ce ‘yar autansu. Matan Babanta hudu ne don haka Yayu ne da ita maza da mata masu yawan gaske.
Wani yaro ne ya shigar dani har dakin Nasiba kamar yadda nayi zato kuwa bata jin dadi ne.

Bata yi zaton ganina ba sai dai taji jiki don gabadaya ta zube. Ta kokarta ta wartsake har ta karya saboda lokacin da naje bata ko karya ba.

Tayi wanka sannan ta kai ni wurin mahaifiyarta. Maman Nasiba Hajiya Tani. Dattijuwa ce sosai, don kuwa zata kai shekaru sittin da biyar zuwa saba’in amma kuma das da ita. Da karfinta babu wani alamar da zai nuna cewa shekaru sun hau mata ka.
Na durkusa ina gaisheta tana amsawa cikin fara’arta. Yayin da Nasiba take gabatar mata da ni. Ta tambaye ni karatu da iyayena na bata amsar komai lafiya.

Ban wani zauna ba na mike da nufin tafiya, Hajiyar Nasiba tayi mun alheri sosai, na fito bayan na jaddadawa Nasiba lallai tayi kokarin zuwa makaranta gobe saboda tsoratar da nayi da abinda Mallam Zakariyya ya yi mana. Ta kuma yarda don kuwa a washegari har sai da ta riga ni.
Karatu ya kankama sosai don kuwa muna cikin sati na uku ne a cikin wannan zangon.

Muna zaune a friends joint inda mafi akasarin lokaci idan anyi break sannan ba mu da abin yi a wurin muke zama. Hira muke yi cikin nishadi da wasu daga cikin ‘yanmatan makarantar mu. Kowa yana nashi korafin ne a kan yadda yan matan Jami’a suke bai wa Malamai kawunansu, wanda kuma hakan shi ne ke kara lalata mana al’amura. Yake rage mana mutunci suke kuma ganin mu a araha banza. Wani yaro ne ya iso wurin da alamar gajiya a tare da shi, watakila saboda sassarfar da yayi don isowa wurin da muke zaune. “Hauwa’u ki je in ji Mallam Zakariyya.” Abinda ya fada kenan, a lokacin da ya gama yaushe mu.

Gabadayanmu muka zuba mishi idanu saboda yadda abin yazo mana kwatsam. Take alamar tsoro ya bayyana a idona, sai dai kafin na samu damar tambayar shi har Nasiba ta riga ni, “Lafiya yake nemanta?” Abinda ta ce mishi kenan, sai dai a maimakon ya bata amsa dariya ya yi ya ce. “Ka ji Malama Nasiba, ana tambayar tsakanin malamin Jami’a ne da kuma dalibarsa?”. Juyawa yayi, ya yi tafiyarshi, bayan ya ce yana fa jiran ki don kada ya ce ban fada miki ba.”

Da ni da Nasiba muka mike don zuwa kiran malam Zakariyya, ni dai gabana sai faduwa yake yi na abinda yasa shi kirana. Don kuwa ni ban ma san ya sanni ba, haka nan ban tuna wani laifi da nayi mishi ba.

Har muka isa kofar ofishin nashi babu wanda ya tankawa wani a tsakaninmu. Na taba kofar a hankali naji an ce “shigo.” Na yi kyakkyawar sallamata bayan na karanta addu’o’in neman tsari. “Ina wuni Mallam?” Yana zaune a kan kujerar ofishin nashi yana duba wata zungureriyar takarda mai dauke da zanen map (Taswira). Sai da ya gama nadeta sannan ya samu daman amsa mun gaisuwar da na yi mishi, ya dago kanshi yana kallona tare da dan jujjuyawa a kan kujerar tashi.

“A gwajin farko da nayi muku na ranar da aka dawo daga hutu akwai karin takarda daya da ta hau kan adadin yawan daliban da ke ajin a wannan ranar. A iyakacin binciken da na yi sai na fahimci ke ce ki ka rubutawa kawarki saboda rashin tarbiyya da sanin ka idar neman ilimi. Don haka zan yi amfani da ke don ki zamewa sauran daliban ajinku darasi a kan ganganci irin wannan koda kuma a nan gaba wani zai yi kuskuren yi to ba zai zama a kaina ba. Don kuwa ni mutum ne mai bin komai nawa bisa tsari da bin ka’ida. Fita ki bani wuri.”
Na fito jikina a sanyaye na samu Nasiba a tsaye a waje tana jirana saboda kin shiga da ta yi. Ta ce, “Lafiya dai ko?” Na ce, “Lafiya kalau.” Ban yi niyyar gaya mata abinda ya faru ba don kada tayi tunanin ita ce sanadi. Duk kuwa da rokona da tayi tayi, har taji haushi ta kyale ni.

Babu irin tunanin da ban yi ba a kan matakin da malam Zakariyya yake nufin dauka a kaina. Shin zai sa ni na maimaita maddar ne ko kuwa ya ya? Maimaita madda irin wannan mai matukar muhimmanci ba karamin abu ba ne. Ya zama dole na je na ba shi hakuri.

Washegari sanin da nayi muna da shi da safe yasa na yi sammakon tafiya. Sai da ya gama da mu ya fita sannan na mike na bishi don nayi mishi magana.

Ina shiga ofis din nashi ya dago kai ya kalle ni fuskarshi a murtuke. “Yaya lafiya dai ko?” Na ce, “Eh lafiya Mallam.” Ya ce, “To na kira ki ne?” Ya yi tambayar cikin daga hannayenshi alamar jaddada tambayar tashi. Na ce, “A’a malam don Allah nazo ne don na baka hakuri bisa kuskuren…” kan na karasa sai kawai ya ce “fitar mun a office!”

Sum-sum na wuce na fita na dawo aji jikina kamar an bi gabobina an bubbuge su. Na samu Nasiba a ajin bata ce mun komai ba, nima ban ce mata ba, ita dai da alama fushi ta yi don kuwa taga lokacin da na bi bayan malam Zakariyya.

“Wai me ki ke nufi ne da wannan wulakancin da ki ke yi mun? Ina binki ina tambayar ki abu kina wani daddaure rai kina bata fuska?” Na kalleta na ce, “Ba fa daure rai nake yi ba.” Ta tabe baki ta ce, “Kya dai ji da shi, ni nasan malam Zakariyya ba zai kira ki don ya nemi lalacewa da ke ba. Don kowa ya shaide shi a makarantar nan. Ni nasan da abinda ya faru amma kiyi mun bayani kin ki, ai kuma sai kiyi ta yi.”

Haka na wuni sukuku babu laka a jikina. Da na dawo gida ma Umma sai da ta gane. Ita kam na yi mata bayanin komai. Ta ce, “To ai sai kiyi hakuri kawai ki roki Allah ya sassauta fushin nashi idan kuma ya saki kin maimaita ma ai shi kenan tunda ba karatun ba ne gabadaya za a fadi ko? Idan badi tazo da rai sai ki sake rubutawa ai,Shekara kwana ne ga mai rai. Allah kuma yasa hakan ya fiye miki alheri.” To na dan ji dadin bayanin Umma, wanda hakan ya yi matukar sani na dan wartsake.

Duk da sanin tsakanina da malam Zakariyya da na yi bai sa na daina halattar darasin shi ba. E, Haka nan na kara dagewa sosai da sosai ba ma akan darasin shi ba kawai har a kan saura.
Kamar yadda ya saba na bayar da test ba tare da anyi zato ba yau ma haka yayi, daidai gwargwado kuma na amsa tare da yin bayani filla-filla.

Kwanaki biyu bayan nan ya aiko da takardar yin gwajin, abin mamakin shi ne mutum biyu ne suka ci, sha takwas a ajin gaba gabadaya sun fadi, daga wani yaro namiji sai ni a mata. Nade takardar nayi na cusa a jakata saboda zagaye ni da aka yi don tabbatarwa yayin da wadanda abin ya basu haushi suka fara haba! Ai dama biri ya yi kama da mutum. Don kuwa ai yanzu bini-bini sai ka ganta a office din shi.

Nasiba ta kalle ni, bayan mun fito ta ce, “Ni me ke tsakaninki da Mallam Zakariyya ne? Wannan shi ne karo na uku da nake tambayarki, kuma ba zan sake ba daga wannan karon.” Na dan yi murmushi nayi mata bayanin duk abinda ya faru, har zuwa yau. Ta ce, Ikon Allah, to Allah dai yasa ba ya yi miki makin ba ne kawai.” Na ce, “Nima tsoron da nake ta ji kenan.”

Na yi iyakacin taka tsan-tsan kan al’amurana da sauran malamai gabadaya, ba ma malam Zakariyya shi kadai ba. Har aka yi jarrabawarmu ta wannan karon wacce da ni da Nasiba muke sa rai da kyakkyawan sakamakon.


Rayuwata tana tafiya mun yadda ya kamata. Na cire komai cikin raina. Ahmad, Ishak da dan shi, duka burina kullum na ga na kammala karatuna na karbi sakamakona cikin nasara na tafi Bautar Kasa sannan na zama malamar makaranta.

Burina kenan, to amma anya hakan zai yiwu kuwa? Har a yanzu ina da wajen shekaru biyu ne a gaba kafin na gama makaranta.

Amma ban taba sauraron wani da sunan ya zo zance wurina ba, don gudun samun matsala a wurin iyayena. To suma kuma har yanzu ba su ce mun komai ba.

A yanzu hutunmu ya kare mun shiga shekara ta uku ne. Zan iya cewa a ajinmu gaba daya babu Mace da ta fini fice da hazaka, don haka malamai gabadaya sun sanni don hazakata.

Wayewar garin yau Asabar ce, don haka duk kokarina na ganin na gama ayyukana ne da wuri na tafi gidan Yaya Auwalu wuni. Sai dai kan na kai ga gamawa Babana ya shigo gidan.
“Idan kin gama ayyukanki kizo ki same ni.” Na ce, “to.” Ba tare da wata fargaba ba na a kammala cikin sauri na samu Babana kamar yadda ya umurce ni.

Ina shiga dakin na kara nutsuwa saboda ganewar da nayi neman da yake yi mun mai muhimmanci ne.
Umma tana zaune a can gefe da alama kuma wata maganar suke yi. Na durkusa a gefe na ce, “Gani Baba. Ya ce, “Zama za ki yi da kyau.” Na gyara zaman da nayi ta hanyar zama a kan tabarmar da ke shimfide a tsakar dakin.

“Na kira ki ne saboda a ganin da nake miki a yanzu to ya kamata ace kina da cikakken hankalin da kuma tunanin irin na manya. Haka nan ko baya ga haka addini ya baki yanci na kanki, a duk lokacin da wata bukata ko hukunci da ya dangance ki kai tsaye. Kuma ko da nake uba wato Mahaifi a gareki, nayi miki alkawari zan yi iyakacin kokarina don ganin ban tauyeki na tilasta miki wani abu ba. Akwai wasu mutane da suka zo suka same ni kan na basu izini na neman aurenki, kamar kimanin watanni biyu kenan, ban yardar musu ba ne a wannan lokacin saboda kokarin da nayi na ganin nayi kyakkyawan bincike a kan shi mutumin. A iyakacin abinda naji na kuma gani a game dashi ban samu wani mugun abu ko mummunan abu ba. Mutum ne na gari abinda mutane suka fada kenan a game da shi.”

“To, a jiya da daddare sai ga wani aiken ya sake yi duk dai akan maganar ne na kuma yardar musu amma hakan ba yana nufin maganar aure ya tabbata ba ne, don ba zan tilasta miki ba, don kuwa a shekaru uku zuwa hudun da kika yi a gida banga wani laifi ko mugun abu da ki ka yi ba wanda zai sa na tilasta ki yin aure a wannan lokacin ba. Amma duk da haka ina so ki san shi aure hijabi ne a wurin ‘ya mace, shi ne ke kara mata martaba, kima da kuma mutunci.”

Shiru na yi cikin wani irin yanayi da zurfaffen tunani. Abin da ban taba zaton zai zo mun a yanzu ba kenan, wato maganar aure. hakan yana daga cikin manyan dalilan da suka hana ni sauraron kowa, menene zai biyo baya kenan a yanzu? Tunanina ya dawo a daidai lokacin da naji Babana yana cewa “zai zo a cikin kwanakin nan don ku daidaita.”

Na ce, “A’a Baba ba sai ya zo ba ma, idan ya yi maka shi kenan.”
Babana ya ji dadin maganar da nayi ba kadan ba, amma duk da haka sai ya ce “A’a ai zuwan na shi yana da kyau, don ku san juna.”

Na tashi na dawo dakina jikina a sanyaye. Sanya mun albarkar da Babana ya yi ta yi bai sa na wartsake ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 21Mai Daki 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×