Watan Azumi ya kama, Musulmi gabadaya kowa ya bada himma wajen ganin ba a bar shi a baya ba. Matsalar dai kawai shi ne, a watanne kuma cikina ya shiga wata bakwai, don haka lallabawa nake yi har a yanzu saukin abin ma dai tun shigarmu wannan zangon karatun Mallam yasa ni dole nayi differing din shekarar gabadayanta.
A cewar shi badi na haihu dan yayi kwari sai na ci gaba, to ban musa ba don kuwa nima hakan ya fi mun sauki. Raba abincin muka yi mai girki ta yi abinci soye-soye yar uwarta kuma ta yi kunu da kosai.
Tunda shi ya ce idan bai sha kunu da kosai ba idan ya kai azumi baya jin dadi. Har da haduwar da muke yi gaba dayanmu a kicin Amina bata kula ni, idan na gaisheta ma ba ta amsa wa ban dai daina gaishetan ba tunda umarnin maigidan kenan. Habaici kuwa tunda dabi’arta ne bata daina ba. Ni kuwa tunda na rama sau daya abin ya zama gagarumi to na kyaleta magana ta kare, sai tayi tayi taji dadin da take ji idan tayi.
Duk da zaman Sahura a gidan aikin mu kawai take yi, ba ta shiga dakin Mallam, don haka mu ke sharewa. Kirana Umma ta yi akan Babana yana rashin lafiya, tunda naji haka kuma nasan abin ya baci. Don kuwa shi ba mai yawan ciwo ba ne, sai dai idan zai yi, ya kan yi mai zafi ne.
Cikin sauri na mike zan shiga falo saboda na sanar da malam kafin ya fita don ya sauke ni a gida. Amina na samu tana shara har ta kawo kusa da kofa bata yi alamar zata tsaya na wuce ba, don haka nayi nufin rabawa ta gefenta. Mikewar da zata yi sai kawai ta hankade ni da hannunta na bugi bango.
Ta nuno ni da tsintsiya “Kin san Allah? Ki kiyaye ni kada ki yi sanadin da zan saki zubar da jini a gidan nan. Kin sanni kuwa?” Daga bakin kofar uwar däkarshi ya tsaya ya ce, “Me ke faruwa ne?” “Ka dai mata kashedi kawai abinda zan iya fada maka kenan, idan kuma ba haka ba zan yi mata abinda da kai da ita ba za ku yi zato ba. Idan yaso duk abinda zai biyo baya babu damuwa.”
“Hauwa’u!” Na ce, “Na’am, zo nan. Wuce ta nayi na karasa inda yake tsaye ya ce, “wuce ki nemi wuri ki zauna ina zuwa.” Na ce, “to”.
Bai sake tambayata abinda ya faru ba, nima ban gaya mishi ba, bayanin da nayi mishi kawai na rashin lafiyar Babana ne. Ya ce, To na shirya muje. A hanya nasiha yake tayi mun kan hakuri a wata mai alfarma irin Ramadan, sannan kuma a irin halin da nake ciki bai kamata na rinka tanka mata muna fada ba. Zuciyata dai babu dadi kawai abinda na sani kenan.
Mun samu jikin Babana yayi sauki amma duk da haka Mallam yasa likita ya rinka zuwa duba shi. Duk da farkon azumi yayi aike sosai na kayan Abinci, yau ma ya bayar da kudi ma su auki, saboda magani da hidimar gida.
Tare muka dawo saboda aikin abincin buda baki. Ina tsaye a kicin din ina hada abinci tunda ni ke da girkin ranar ita kuma tana hada kunu maganganunta take yi da zage-zage.
Ban tanka mata ba don kuwa duk da dama ba ɗabi ata ba ce amsa mata a yanzu kuma tsoronta nake ji. Na gama na juye abinci a babban flask na hada salads a gefe na dauka zan fita, ita kuma zata shiga kicin din na kauce na bata wuri ta shige. Na isa falo na ajiye na tafi daki don dauro Alwala. Muna zaune bayan sallar magriba abinci nake ƙokarin zuba mishi na dauko ludayi a cikin kunu da nufin zubawa a kofi, sai kawai naji Amina ta ce “lalala ki ka fantsala mun?” Kan na san abinda zan ce mata sai kawai ta ɗauki kunun gaba dayanshi ta sheka mun. Da iyakacin karfina na yi ihu tare da salati.
Wuf nayi zan mike saboda firgitan da nayi da radadin kunun a jikina, santsi ya debe ni na sake zamewa na fadi warwas a kasa. Gudun da Mallam yayi wajen rike ni bai sa hakan ya taimake ni ba. Illahirin komai nawa sai da ya dauke ya sake dawowa saboda buguwar da nayi, Take ya dauko ruwan sanyin wurin ya sheka mun ya kama kici-kicin tube min rigar da ke jikinsa ta atamfa wacce Allah ya ufa asiri ta rage karfin kunan da nayi. “Sannu Hauwa’u.” Ya fada a lokacin da ya gama zame rigar a jikina.
A gefen hannuna na dama kunan ya tsaya kuma nan ma Allah ya takaita babu yawa. “Ki yi hakuri.” Abinda ya fara gaya mun kenan, sai dai kafin na ce wani abu ji nayi tamkar ina fitsari saboda irin wannan abin yasa take gabana ya fadi. Ba sai an tsaya yi mun bayani ba, jini ne. Kukan da nake yi zatonshi na kunan da nayi ne, don haka hakuri yake ta bani. Sai dai ban ce mishi komai ba sai da yaga ya dan fara gangarowa gefen tiles din da nake Zaune. Mikewa yayi yasa hannu ya ciccibe ni cikin sauri yayi waje.
Inda yake ajiye mota bakin shi kuwa fadin Innalillahi wa inna ilaihir raji’un yake yi.
Tun kafin mu karasa asibitin na fahimci wannan karon da bambanci, don kuwa ciwo ne mai tsanani ya kama ni. Ciwon ciki da bayana tamfar zai karye. Muna isa aka tabbatar mana haihuwa zan yi. Mallam ya kalli Likitan ya ce, haihuwa watan cikin bakwai ne fa? Ya ce, eh babu damuwa in dai da ranshi shi kenan za mu san yadda muka yi da shi. Cikin ikon Allah da taimakon likitoci na haifi da wata bakwai.
Yana fitowa kuwa ya fara zandara ihu alamar da ke nuna yazo cikin koshin lafiya. Nurse din da ke wurin ta nuno mun shi na kalle shi hawaye na bin kumatuna.
Ta dan yi murmushi ta ce, kada kankantarshi ta dame ki, muhimmin abu shi ne lafiyar shi kalau. A ka gama kintsa ni tare da canza mun daki. A lokacin ne kuma Mallam shima ya shigo. Ya kama hannuna ya rike yana dan matsawa.
“Kiyi hakuri Hauwa’u. Na daga ido na kalle shi take na hango fadawar da yayi ta farat daya Na dan yi murmushi don ganin hankalinshi ya dan kwanta. Na ce mishi, karfe nawa ne yanzu? Ya daga hannunshi da agogo ke daure ya ce, biyu da kwata, na ce har yanzu ba ka ci komai ba ko? Ya ce, na ci zan yi magana ya ce, rufe idonki ki yi barci ki huta.
Ban farka ba sai wajen bakwai na safiya. Samahatu da Baba Ladi na gani a zaune.
Na yi murmushi muka gaisa suna tambayata jiki, na ce da sauki. Ban dade da farkawa ba malam ya shigo da Baba Ladi sannan ya matso kusa dani yana tambayata abinda zan ci. Na ce, haba “yallabai ka bari su Samahatu za su bani”.
Ya dan yi murmushi yana kara kallon hannuna da kunan kenan ya dan tattashi, ya juya ya fita. Wata Nas ta dawo tare dashi da kayan dressing na zauna a bakin gadon ta daye kunan sannan tayi mun dressing.
A asibiti muka bar yaron saboda umurnin likita na a saka shi a kwalba (incubator) saboda ba shi da girma sosai ga kuma rashin kwari. Sai dai da gargadin kullum za a zo a tatsi nono wanda za a rinka ba shi safe da yamma.
Na dawo gida sai dai babu Amina a ciki abinda na lura kenan ban tambayi Mallam ita ba, shima kuma bai ce mun komai ba. Sai dai ya roki Umma da ta ba shi wacce zata zauna da ni mai dan shekaru, don haka Inna Hadiza ta zo. Jego mai matukar dadi nake yi don kuwa ta ko ina ji da ni a ke yi.
Ta bangarena da kuma bangaren Mallam, don kuwa ‘yan uwanshi sun zo, ƙannenshi da kuma ƙanwar mahaifinshi. A wurinsu kuma naji zancen sakin Amina.
A rayuwata babu abinda naki irin saki, ko ambaton shi aka yi a kusa da ni sai gabana ya fadi. Kamar yadda likita yayi umurni kullum muke zuwa baiwa yaro nono.
Idan naje kuma za su sani na gwada mishi don ya dan koyi tsotso. Sai dai basa bari ayi ta bashi sosai saboda rashin ƙarfin mukamukinshi. Sai na tatsa mai yawa a cikin wani abu a ajiye shi ne za a rinka ba shi har yamma idan mun koma.
Cikin yardar Ubangiji kuma yaron yana ɗan murmurewa a hankali yana kara girma kadan-kadan. Ranar da aka wayi gari kwana bakwai Mallam ya nada wa yaro suna Zakariyya.
Ni dai mamaki ya kamani. Na shiga dakin don kirana da yayi, na same shi ya tsala kwalliyarshi cikin shadda ‘yar asali, fara yana murza hular da zai saka yana ganin isa na ya ajiye ya jawo ni jikinshi. Ya ce, “wata alfarma zan roka a wurin ki” na ce ta me ce Yallaɓai? Ya ce, ga Mallam nan na baki kiyi hakuri ki canza mun suna.
Amma yadda ki ke gantsara mun Mallam din nan wani ai sai yayi zaton idan ya tashi ganina a zaure zai ganni a kan buzu.” Na ce, “To shi kenan me ka ke so na ce maka?” Ya ce, “ga sunaye nan da yawa ga Darling” na karkace na gallà mishi harara na ce, “eh ai dole na ce maka darling don shi yafi maka dadi.”
Ya kyalkyale da dariya saboda gane abinda nake nufi ya ce, “kai Hauwa’u kenan” na ce, “Habibi zan ce shi fa ya yi maka?” ya dan lumshe ido ya fadi sunan. Sannan ya ce, “masoyina kenan ko ba daidai ba ne da kalmar larabci” na ce, eh haka ne yayi mun”.
Har na juya na dawo na ce, “to amma ai sunan Mallam suna ne mai daraja wanda ake yiwa manyan mutane lakabi da shi kamar kai ai na kira ka da shi ne saboda girmanka da darajar da ka ke da shi a wajena”.
Ya ce, “haka ne Habibati” nayi murmushi na juya na dawo dakina Inda aka cika dankam akai shagalin sunan da ban san iya adadin kudin da mai gidan ya kashe ba duk kuwa da cewa yafi kowa sanin jaririn da ya kashewa wannan kudin yana can asibiti kwance cikin kwalbar Likita.”
Cikin ikon Allah sai yaro yayi murmurewar da su da kansu suka ba mu shi cikin sati biyu, sai dai tare da gargadi mai yawa. Na yadda za a kula dashi cikin dan kankanin lokaci sai na murje nayi kibar da ta baiwa kowa mamaki. To balle kuma jaririn da tamkar hura shi ake yi. Ya yi wayo babu mai ganin shi ya ce, bakwaini aka haife shi.
Taruwan da ayyukan gida suka yi mun bai hana ni kara kula da mijina ba tunda har yanzu kusan wata biyu Amina bata dawo ba don ya ce ya hakura.
Da taimakon Sahura sai komai ya zamo mun mai sauki, sannan shima da kanshi yasa a nemo mun mai taya ni reno.
A wannan lokacin ne nake ganin na taba yin Amarci a rayuwata saboda kula da tattali da tsantsar so da Habibi yake nuna mun.
Sai na gane shi aure dai sa a ne idan Allah yaga dama sai ya baka. Ba kuma yana nufin don kayi aure ka fito ka sake yi ka fito shi kenan kai ba ka da rabo ba.
Sai dai kowa yana da irin tashi kaddarar, ni tawa kaddarar ta zan yi wasu auren ne a baya kafin wannan. Ƙaunar da nake yi wa mijina kuma sai tasa na ko yi wata dabara ta rokon Allah a kullum nayi sallah shi ne ya karawa mijina so na da kaunata. Ya kwadaitar da shi zama da ni, ya bani ikon kyautata mishi na zamo mace ta kwarai saliha a gare shi, ya kuma sa na zamo mata a gare shi a Aljanna.
To kuma ya amsa don kuwa kullum kara sona yake yi. Ban bar yaran Amina sun yi maraicin uwa ba, don kuwa na tsaya tsayin daka wajen ganin na wadatar da su.
Sai dai abu daya da na kula kawai shi ne, shi Ɗa a kodayaushe uwarshi kawai yake bukata.
An wayi gari yau Asabar kasancewar Mallam a gida yake bai hana ni baiwa yaran kulawata ba, duk da hidimar shi da nake yi. Sai da suka tafi makaranta sannan na shiga ɗakin nashi.
Waya yake yi ban dai san da wanda yake yi ba, na ajiye mishi plate din dambun naman da na kawo mishi. Sannan na dauko ruwan juice din da nayi mishi da ya yi sanyi na ajiye. Shima ya ajiye wayar yana murmushi ya ce “Hajiya tana hanya.”
Na ce “Amma shi ne bata fada ba.” Ya ce, “Eh nima nayi waya da Karima ne take gaya mun tayi niyyar yi mana kwatsam ne z ata zo ganin yaro. “ Wuf nayi na mike ya ce “ina za ki?”.
Na ce “haba yallabai ai banga ta zama ba.”
Kafin isowar Hajiya har na kammala muhimman abubuwan da zan yi, tuwo nayi mata na alkama da kuma lafiyayyiyar miyar kuka nayi mata farfesun kayan ciki da ya ji kayan kamshi Na kuma yi mata kunun zaki.
Gabadayanmu muna zaune a gabanta har da yaran, yayin da take rike da (Daddy, Junior abinda yaran suke kiran shi kenan). Itama mamakin girman yaron take yi, ta dan faɗaɗa murmushinta ta ce, gashi kuma cikin yaran babu wanda yayi kama da shi haka.
Ta sanyawa yaran albarka gabaki dayansu.
Ta miko mun shi ta fara cin abincinta don haka da ni da yaran muka basu wuri.
An dade kafin yazo yayi kirana na shiga ɗakin na zauna a can gefe ta kalle ni ta ce, matso nan Hauwa’u, na dan kara matsawa gab da ita ta ce, bude hannun naki mu gani.
Na bude gefen hannuna da ke dauke da tabon kunan, don kuwa ya dade da warkewa. Ta ce, “Sannu kin ji, ki kuma kara hakuri. A yadda mijinki ya yabe ki kin samu kyakkyawar shaida amma kada hakan ya sanyaki ki rudu. Ki kalli wadannan yaran guda hudu ki yafewa uwarsu ki kuma san Ubangiji shi ne ya kare ki daga sharrinta ba wayo ko dabararki ba. Ki kuma san shi ne a kullum zai ci gaba da kare ki. Ballantana a ganin da nayi mata ta canza ta yi da na sani. Da sabuwar kishiya ai gara wacce ka san halinta.”
“Na umarci mijinki da yaje ya dawo da ita, don haka ku dukkanku ku kara hakuri akan wanda kuke yi a da.”
“Tunda zama ya hada ku tare kun haifi yara tare kuma dolenku suyi zumunci tunda ubansu daya.”
Na dawo dakina na zauna tare da yarda da abinda Hajiya ta ce. Ita kuma washegari da sassafe ta tafi.
Sati daya cif bayan nan ya shigo dakin cikin kwalliya ta manyan kaya sai kamshi yake yi ya matso kan kujerar da nake zaune a kai ina baiwa Daddy Junior nono.
Ya rike hannunshi yana wasa dashi. Zuwa can yace na dauka zamu fahimci juna da ke Hauwa’u, ina rokonki ki bani hadin kai da goyon bayan da nake nema daga gare ki tunda kin sa ko a da na hakura da zama da Amina to a yanzu zan bi maganar mahaifiyata, don haka bana son wata matsala daga gare ki. Ya mike ya tafi.
Wani irin abu na rinka ji mai daci a bakina saboda ɓacin rai wanda daga baya na gane kishi ne.
Haka na wuni wannan abun yana nukurkusata.
Nayi kuka har na gaji wato dai shi aure ba ka samun yadda kake so. Kamar ni da nayi aure na gamu da matsalar miji da uwar miji da Ya’yanshi, a yau kuma na gamu da na kishiya wanda nake ganin kamar yafí wahalarwa saboda shi a zuciya yake. Idan kayi sa’a ka samu saliha mai tsoron Allah sai abin yazo maka cikin sauki, idan kuwa ka gamu da muguwa mara imani to ba saki ba sai ta kashe ka. Ba komai ke sa hakan ba face dacin da zuciya ke yi a kanta.
Sai dai a yau na kudurci aniyar kara wata addu’a a kan wacce na saba yi a da, ita ce ta neman tsari da kishiya da sharrinta da kuma muguwar shawara. Zan kuma baiwa mijina goyon bayan da yake so, don kuwa na kuduri aniyar zan kyautata mishi iyakacin iyawata.
Tashi nayi na fara kokarin shirya musu abinci don nasan a yanzu kam suna gab da isowa. Sannan na shirya yaran gabadaya tare da sanar da su dawowan Mamansu.
Nima nayi kwalliya mai kayatarwa na gyara yaro. Muka yi shar. Ba su iso ba sai bayan Isha’i.
Har daki na same ta nayi mata sannu ta amsa cikin fara’a da sakin fuska take kuma na yarda ta canja kamanni koda kuwa bata canza a halaye ba. Don kuwa ta rame tayi bakikkirin.
Na shiga dakinshi da fara ata nayi mishi sannu da zuwa abinda ya ba shi mamaki yasa shi ya rinka bina da kallo har dakinta na koma na kirata don mu ci Abinci.
Sannan ya yi bayanan da zai yi wadanda nuni ke kawai akan ba zai sake lamuntar raini ko karya dokar shi a cikin gidanshi ba, haka nan duk wacce ta sake hantara ko zagin wata to zata bar mishi gidanshi ballantana a kai ga saka hannu a jiki.
To a halin yanzu kam zaman yayi kyau, sai na ce ma ba mu taba zama mai dadi irin wannan ba.
Ta ɓangarena dai ina iyakacin kokarina wajen ganin ban ɓata mata ba, haka nan ita ma ƙokarinta kullum ta kyautata mun ne don ta fahimci zafin barin gidan miji da ya’ya. A kullum kuma za ka same ta tare da Daddy Junior, don a wurinta ma yake wuni don kuwa yan uwanshi basa yarda yayi nesa da su. Shekara ta zagayo don haka na koma makaranta a lokacin da Daddy yake da watanni tara.
Yayi kato dashi har yana kokarin yin tafiya Bani da matsala a game dashi. Don kuwa a wurin Amina dama yake wuni Sai na dawo ne yake shan nono.
Zamanmu gwanin sha’awa mun zama yan uwan Juna, komai zamu yi tare muke yi. Babu wani habaice-habaice ko bakar magana. Mafi akasarin gidajen da zaka ga matan sun kasa zaman lafiya daga mazajen ne a yanzu ne na kara yarda da hakan.
Don kuwa mu a gidanmu da maigidan yayi tsaye gashi abin ya tsaya. Sai na fahimci babu wani abin da yafi auren jarumin namiji dadi a rayuwa.
Ya tsaya ya tsare maka mutuncinka da yancinka a waje a cikin gida kuma ya nuna maka tamfar kai kadai ne saboda yanci da kauna.
Na yarda cewa idan har kaga matsalar ka bata kare ba, to ba ka daga hannu sama ka roki ubangiji ba ne, ko kuma ba ka yi Imani da cewa yana amsawa ba. Don kuwa a yau an wayi gari babu wata Addu’a da nayi na gayawa Allah damuwata ba tare da ya biya mun bukatata ba.
A watan da na mika project dina na kammala karatun Jami’ata a watanne kuma na haifi santaleliyar jaririyata ba tare da wani matsala ba.
Na tuna abinda Babana ya gaya mun a ranar da aurena da Ishak ya mutu, take na yarda cewa Addu’ar iyaye ga ‘ya’yansu karbabbu ne don kuwa ya amshi addu’ar Babana ya ba ni Mallam Zakariyya. Mutumin da nayi ta kokarin na bijirewa aura sai gashi ya zamo mun mijin marainiya.
Na gode.
Hajiya Hafsat C. Sodangi
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
December, 2014