Tsokaci
Wata irin gaba ce tsakanin talaka da maikudi. Maikudi yana yiwa talaka kallon nesa-nesa, irinka irin wahala, Allah Na gode maka ba ni ba ne. Yakan kara yi masa kallon na fi ka, da gumina na nema kai ma sakacinka da mutuwar zuciya ya hana ka ka samu. Ka da ka roke ni don ba ka nan lokacin da na nema.
Talaka na yiwa Maikudi kallon barawo, azzalumi da ya handame dukiyar kasa. Sarkin izza wanda ya ci da rabonmu. Da a ce ni ne ke da kudinka da na yi abinda. . .