Haske
Haske shi ne maganin duhu...amma yaushe hasken zai zo? Yaushe zai bayyana?
Kano, Nigeria
Kwance yake akan wani katafaren gado da aka lullube da wani lallausan zanin gado. Ji yake kamar yana bacci kamar idonsa biyu. Irin baccin nan da ka kan yi idan damuwa ta yi maka yawa, gabanka na faduwa fat fat.
Kafin wani lokaci ya ji kamar yana kasa numfashi. Sai a lokacin ya lura ashe wuta ke cin dakin.
Wani abun ban al'ajabi uku ne ya sa shi cikin dimuwa.
Na farko baya ganin hasken. . .