Harabar kotun a cike take makil! Babu wanda bai halarci wannan sharia ba mai daukan hankali.
A gefe daya Luba ce zaune da yar modu tana karkade kafa. Daga gefe can Hindatu ce a cikin matsanancin tashin hankali. Abubuwan da suka faru ba abubuwa ne masu dadi ba, ganin Rukky a cikin halin da take ciki ya sa jikinta yayi mugun sanyi. Tsoro take ita ma kar karshenta ya kare a haka. Sai sharar hawaye take.
Bata da wata masaniya akan shirin Luba ko wata manakisa na ta. Ita dai kawai tana tausayawa Rukky.
Almutapha na wani gefe daban shi. . .