Wata irin zabura yayi! Gumi ya jike shi sharkaf! Har makyarkyata yake. Babu abinda yake yi sai salati. Ransa yana raya masa shartin makiya ne amma ya ka sa yarda.
Cewa yake
" Ta kasheni! Yarinyar nan ta cuce ni! Innalillahi! Yau na shiga uku na!
Ya wawuri wayarsa ya kira kaninsa Bilya. Bai ko bari ya gaishe shi ba ya ce
" Dakata! Me ke tsakaninku kai da Matata Luba?"
Ya fara ma sa rantse rantse ya ce
" Ka fada min gaskiya kawai domin ka san tukwicin da nake yiwa wanda ya min karya akan laifin da ya min! Abunda aka. . .