Yawon Duniya Mafarki
Yawon duniya mafarki ne, idan an je za a dawo.
Saudi Arabia
A tsammanin Luba duk wanda aka ce ma ta ya tafi saudiyya to lallai kakar shi ta yanke saka domin arziki ne zai dangwala ya dawo gida yana gwalangwaso. Ga mamakinta sai ta ga ashe ba haka ba ne? Ashe rayuwar saudiyya rayuwace ta mai zaman kanta? Ashe gwagwarmaya ce kowa tashi ta fisshe shi?
Har a kullum a gudu kake kar a kama ka a maida ka inda ka fito. Kullum sai ka nema zaka ci. . .