Mutuwa Mai Tonon Asiri
Mutuwa mai yankan kauna, bakin takobi mai raba soyayya!
Niamey, Niger Republic
A shekara 18 babu wani namiji da zai daga ido ya kalli Rokaiyatou ba tare da bukata daya ta mamaye ransa ba, na ya mallaketa har abada. Amma a zuciyarta mutum guda ne kacal! Frère Momodou. Idan da shi a duniya to ba ta ki sauran maza duk a hada ayi jana'izarsu ba wannan ba matsalarta ba ce!
Sau da dama takan yi tunani a duniya akwai irin Frère kuwa? Dan adam guda. . .