Rai Da Buri
Burirrika kamar mayaka ne a fagen daga, wasu sukan kai labari, wasu duk yadda aka so ba za su taba kai labari ba.
Kano, Nigeria
Ranar Asabar aka kaddamar da sababbin 'yan kungiya. Hindatu, Lubabatu da Rokaiyatou. Aka kafa musu dokokin kungiya kuma duk suka yi mubaya'a.
Shugaba Hajiya Kububuwa wata irin ingarmar mace ce mai jarabar tsawo kamar daren wahala. Fuskarta baka ce kirin mai dauke da kalangu a kuncinta. Yanayin girman jikinta kadai ya isa ya yiwa dan adam kwarjini ya sa masa tsoro, ga ta. . .