Har ta sauka daga cikin napep din jinta take kamar a wata duniya ta daban. Tayi gaba yayi mata Magana.
"Hajiya kudin"
Jakarta ta bude, bata san nawa bace ta dauko ta miqa mishi, tayi juya ya sake cewa,
"Ga canjin, ko kin barmun?"
Hannu tasa ta karba tana zuba su cikin jakar da ko zageta batayi ba. Ta sha jin kalmar tsiraici, ta dauka tasan ma'anar kalmar, a da ta dauka tsiraici shine ka rabu da tufafin jikin ka, sai yau ta fahimci akwai tsiraicin daya girmi rabuwa da tufafi. Akwai suttura da ba kaya bane kawai. . .
I like to be reading the different types of novels