Hannu tasa tana kara gyara kullin lafaya din da yake daure a kugunta, hawaye ne da batasan inda suke sauka ba, saboda kanta da yake a sadde. Har Anty ta gama mata maganar da take yi mata, sam bataji komai ba, hankalinta baya jikinta, bata kara shiga tashin hankali ba sai da taganta tsugunne a gaban Baba, sai da taji muryar shi ta dira kunnuwanta cike da bankwana, tabbas aure ba mutuwa bane ba, amman tana jin kewar Baba har cikin kasusuwan jikinta.
“Haka muke cinye kwanakin mu Hindatu, sai makusanta cikin jimami suyi ta ganin kamar munyi gaggawa, suna manta yanda su dinma basu yi jinkiri ba.”
Baba ya yi maganar yana kasa yarda yau shine Hindu take tsugunne a gaban shi, yau shi ne zai yi sallama da ita, ya mika kulawarta da amanarta a hannun Hamza. Iyaye mata kance rana irin ta yau kanzo musu da farin ciki hadi da firgicin rashin sanin makomar gobe akan auren yaran su mata, abinda ba su sani ba, shine firgicin yafi yawa a tattare da iyayensu maza, ka dauki amanar ‘yarka da ta yi shekaru karkashin kulawarka, kana duk wani kokari da ka ke da iko a kai na ganin wani abu bai cutar da ita ba, rana daya zaka mika ma waninka ita, duk kuwa da tarin kokwanton da yake ranka na ganin babu wanda zai iya kula maka da ita kamar kai.
“Zance kiyi hakuri saboda yana daya daga cikin manyan jigo a cikin zaman aure, amman bance kiyi hakuri idan ya hada da cutarwa ba, na dage akan islamiyar ku saboda ki fahimci darajar da musulunci ya baki a matsayinki na ‘ya mace, idan har hakurin da zakiyi a gidan aure ya nemi taka wannan darajar, Hindu ina da wajen zamanki, karki taba bari al’ada ta tauye danne miki ‘yancin da addinin ki ya baki…”
Cewar Baba, yana dorawa da,
“Allah yai muku albarka…”
Yanayin muryar shi da yanda ta sauka ya kara haduwa ya karyama Hindu zuciya, batasan ta zauna ba, saida taji kanta ya jingina da kafafuwan Baba, kafin wani kuka daya fito daga kasan zuciyarta ya kwace mata, kuka take na barin gida, kuka take cike da firgicin rashin tabbas din da take cikin aure, kuka takeyi saboda yanzun ne take jin kamar bata shirya ma zama da Hamza ba, yanzun ne take jin wani bayanannen tsoro ya lullubeta. Sai da Mama da wata kanwar Baba suka zo suka janyeta da kyar suna fitowa da ita daga bangaren Baba. Kuka take yi har yanzun da aka fito da ita.
Ko da kanta ba’a lullube yake da lafayan jikinta ba, ba lallai ta ga hanya ba saboda kukan da take yi, batasan waye ya kamata yana sakata a mota ba. A wani irin gigice take jinta har suka karasa gidan da yake a unguwar Malali, ta wajen KAD Academy. Batasan waye yake ce mata tayi addu’a kuma ta fara saka kafarta ta dama ba, ita banda sallama babu abinda ya iya zuwa kanta, addua kullum cikin yinta take, fiye da yanda zasu taba fahimta, saboda haka su kyaleta kawai taji da abinda takeji. Tana jin suna rike da ita har aka shiga wani daki, tukunna aka zaunar da ita akan gado.
Har lokacin fuskarta a rufe take, danma tanajin sanyin AC din da ya gauraye dakin yana ratsata, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, kayansu da zasu saka anjima wajen zuwa Dinner yana wajen su Aina’u, su suka harhada komai, tasan kuma sun taho dasu, kilanma suna cikin gidan. Tana jin shige da ficen mutane da masu yi mata fatan alkhairi, da masu yi mata nasiha, ita kam banda hayaniya batajin komai, ba zatace ga awannin da aka dauka a haka ba, sai da taji muryar Hauwa data kama mayafin da yake rufe da fuskarta tana fadin,
“Ke bude kisha iska, duk sun tafi.”
Numfashi Hindu ta sauke hadi da ajiyar zuciya, tana kama mayafin ta kara goge fuskarta da shi, kafin Dimples ta shigo da plate din abinci a hannunta tana kallon Hauwa.
“Ba za kici abincin ba? Bie na kitchen…”
Dan yatsina fuska Hauwa ta yi, ita ba wata yunwa take ji ba, amman taga kamar da hadin salad, zata ci wannan.
“Jiba gulma, yanda kike damun uban kowa da Hamza shine kika garji wannan kukan, kinga fuskarki? Ki tashi ki wanke ko zai sauka kafin lokacin Dinner.”
Dimples ta karasa tana zama gefen gadon, ta fara juya abincin da yake rike a hannunta.
“Wallahi duk fuskarki ta kumbura.”
Hauwa ta fadi tana nufar hanyar da zata fitar da ita daga dakin, ta fice.
“Ki tashi Allah, kinsan dai dole a zageki tunda ango yafi ki kyau, gara ki wanke fuskar ko zai taimaka miki.”
Dan murmushin karfin hali Hindu tayi tana saukowa daga kan gadon, sai dai kofa biyu tagani a cikin tankamemen dakin baccin, na farko ta fara budewa tana ganin dakin sake kayana, saita rufo ta dawo ta bude dayan, dan ware idanuwanta tayi ganin kayatuwar da bandakin ya yi.
“Ke kinga toilet din nan kuwa?”
Hindu ta fadi, tana saka Dimples kusan shakewa da shinkafar da take bakinta.
“Banza yanzun ranki har ya yi sanyi, saboda bandaki.”
Dimples ta karasa tana kwashewa da dariya, itama dariyar Hindu tayi, tana shiga bandakin, komai ta karewa kallo, kamar an ciro shi daga film an ajiye mata, har bango saida ta dafa, yanayin tayal din ruwan gwal yayi matukar daukar hankalinta, lokaci daya ta nemi damuwar da take ciki ta rasa, alwalar magriba ta dauro, dan bata lokacin da aka tsaya yi, sai bayan la’asar aka taho kawota, tasan inba dai babu masallaci a kusa dasu ba, tabbas ana gab da kiran sallar magriba, kuma karfe bakwai sukayi da mai kwalliya zatazo tayi mata, kafin su fara kama hanyar zuwa wajen dinner.
Tana fitowa ta sami su duka ukkun a dakin suna cin abinci.
“Ke ba zakici wani abu ba? Tun dazun ki ke yawo kamar ganga.”
Kai Hindu ta girgizawa Biebee, ko yunwa bata ji ballantana taci wani abinci. Tana zama ana fara kiran magriba
“Wai Magriba har ta yi?”
Hauwa ta fadi cike da mamaki.
“Sai ku tashi kuyi sallah, ni na yi sub.”
Hararar Biebee din Dimples ta yi.
“Abin nan baimun dadi ba, yanda na wanke kwalliyata naso kowama ya wanke ta shi wallahi.”
Dariya Biebee ta yi sosai.
“Dan bakin ciki dai baiji dadin rayuwar shi ba.”
Dimples din bata ko kulata ba, ta mike, ita ta tattara kwanonin da su duka sukaci abinci.
“Allah sarki Kawata, dadina dake baki da matsala.”
Biebee din ta fadi tana sake kwashewa da dariya, fita daga dakin Dimples ta yi tana kin biye mata, tana dawowa itama alwala ta dauro ta fito, duk sallah suka yi banda Biebee da take zaune tana danna wayarta. Basu dade da idarwa ba saiga mai kwalliyar na kira tazo kan street din, Hauwa ta karbi wayar Hindu ta fita tana dawowa da ita. Batare da wani bata lokaci ba ta tsarama Hindu kwalliyarta da tayi matukar karbar fuskarta, suma yi musu aka sake yi, Biebee kuwa dan gyara mata akayi, tunda bata bata tata ba. Kafin kace wani abu har sun kammala shirinsu tsaf, Hindu na sanye da material da dinkin doguwar rigar kawai zaka kalla kasan amarya ce.
Wine color kamar yanda bature yake kiran kalar kayan da suke jikinta, tayi wani irin kyau da har Hauwa sai da ta ce,
“Oh Allah, Hindu kinga yanda ki kayi kyau?”
Murmushi Hindun tayi, tana mata godiya, hotuna suka dinga yi mata, ta mika musu harda wayarta, su material dinsu ruwan madara ne, duka dogayen riguna.
“Ni kadai ce nayi kama da muburkin miya.”
Dimples ta fadi tana saka dukansu kwashewa da dariya.
“Zan taya ki addu’a kawata, yar kibar nan Allah ya dube ki.”
Tsaki Dimples ta ja.
“Bie bana son iskanci, kuma anma fi yayin kalata kiji, yarinya siririya, ga kyau ga dimples.”
Wata dariyar Biebee ta sake kwashewa da ita, Hauwa nata kallon su da murmushi a fuskarta, yanayin kawancen su yana burgeta, tun jiya sunyi fada yafi sau ashirin, kamar kaji haka suke, Dimples saurin kulewa, Biebee kuma tsokana. Hindu kuwa kiran Hamza ta daga, tun bayan wayar da suka yi da aka daura aure, sai da suka zo gidansu akayi hotuna, shima magana ko daya bata hadata da shi ba, sai take ganin wani nisantaccen yanayi shimfide a fuskar shi da batasan na menene ba, basu wani dade ba suka wuce, basu sake neman juna ba kuma, yanzun ma tana karawa a kunnenta yana furta.
“Kun shirya?”
Kai tadan daga mishi tana dorawa da,
“Eh…”
Cikin sanyin murya.
“Kaji wai sun shirya…”
Hamza ya yi maganar daga dayan bangaren da alama wani yake yiwa magana, kafin taji ya kashe wayar a kunnenta, saukewa tayi tana kallon su Biebee a zahirance, a badini kuwa batama ganin su, wani abu ne yazo dai-dai kirjinta yai tsaye, ba tasan akwai wani yanayi a tsakanin tsoro da tashin hankali ba, sai yanzun data tsinci kanta a cikin shi male-male.
“Sauran yan gidan su Hindu fa? Wa zai je ya dauko su?”
Fodio ya bukata.
“Dan Allah Fodio ka kira AbdulHafiz, nifa ban sani ba, bana ji yace ya tura ba?”
Hamza ya fadi yana kara saka comb cikin sumar kanshi ya taje, kafin ya dora hular shi, farar Getzner ce kal a jikin shi sai daukar ido takeyi, duk da babu aiki a jikin riga da wandon da yake sanye dasu, kallo daya zaka yiwa yanayin dinkin saiya burgeka, zaman agogon shi ya gyara, yana daukar babbar rigar shi ya rike hannu, dan bazai sakata tun yanzun ta yamutse ba. Turarukan da suke baje kan gado ya shiga dauka yana kara feshe jikin shi da rigar da take hannun shi.
“Ka cakar dani Hamza.”
Fodio ya fadi yana mikewa tsaye, kan shi harya fara juyawa saboda karfin turarukan, ko kallon shi Hamza bai yi ba, ya mika hannu ya dauki wayar shi da mukullin mota, ficewa yayi daga dakin yana shiga kitchen, yanda yake jin shi idan baidan kara shan wani abu ba, rayuwar shi zata shiga wani yanayi kafin a gama dinner din nan. Kwakbar vodka ya dauka yana samun kofi ya zuba fiye da rabi a ciki, ya rufe kwalbar ya mayar, duk da akwai dan sanyi, saida ya dibi kankaru ya zuba, tukunna ya kwankwade.
“Uban me kake sha? So kake ka fara slow cikin jama’a?”
Fodio ya karasa maganar yana dariya.
“Kaina yamun nauyi ne, kawai abinda zai taimaka mun a gama dinner din nan.”
Dariyar Fodio ya sake yi yana girgiza kai kawai.
“Idan nace maka kayi kuskure kamar na makara ko? Tunda an riga an daura.”
Numfashi Hamza ya sauke yana kara bude fridge din da nufin dauko kwalbar ya sake kwankwada, Fodio yayi saurin karasowa yana mayar da fridge din ya rufe
“AbdulHafiz zai kasheni wallahi, ka wuce mu tafi…”
Runtsa idanuwan shi Hamza ya yi yana sake bude su, yanda kanshi yayi dim yana da tabbacin gab yake da fara buguwa fiye da misali.
“Ya isa Hamza, ya isa haka, ba a karkashin kulawata zaka yi wannan shirmen ba.”
Yasan da gaskiyar Fodio, amman a wani irin takure ya ke jin shi kamar ya saka ihu. Duniyar ta hade mishi waje daya, ga wuyan shi da duka jikin shi da yake ji kamar an shake, tamkar wanda aka garkame a dakin da babu window, kofar ma an kulle an cillar da mukullin haka yake jin shi, iskar da yake shaka tun bayan da aka daura auren kanta da kauri yake jin tana mishi zirga-zirga. Kafin ya fara neman mukullin da zai warware wannan kullin da ya jama kanshi yake so yasha giyar shi harsai ya daina gane komai. Amman hakanma ba zai yiwu ba saboda zaije dinner, dinner din bikin shi.
“Me na yi haka?”
Ya tambaya yana kallon Fodio.
“Komai zai yi dai-dai, calm the fuck down Man. Ka natsu fa.”
Fodio yake fadi muryar shi na rawa saboda yanayin Hamzan ya fara bashi tsoro kuma, tun yana dariya, yanzun abin tsoro yake bashi, da AbdulHafiz yana nan shi yasan yanda zai yi da Hamza, amman koma meye ba zai barshi ya bugu ba tunda taro zasu shiga.
“Kazo mu tafi.”
Numfashi Hamza yaja yana fitar da shi da nauyin gaske, kafin ya jinjina kai, yana saka Fodio sauke numfashin da bai san yana rike da shi ba.
“Na gode.”
Ya furta yana nuna ma Hamza hanyar fita daga kitchen din, bai yi musu ba ya fito, harabar gidan inda motocin su suke suka karasa, har wajen motar Hamza ya raka shi
“Zaka iya tuki?”
Ya tambaya, Hamzan nayin wani irin shiru, saboda ya nisa cikin tunanin da bazai ce ga na mene ne ba, dan taba shi Fodio ya yi tukunna ya daga ma Fodio din girar shi duka biyun.
“Hamza, Hamzaaa”
Fodio ya karasa cike da roko.
“Na yi yarinta da ciwon zuciya, Hamza ka bari in mayar wa AbdulHafiz kai lafiya sai ka yi duk abinda zakayi.”
Sai lokacin Hamzan ya yi dan murmushi.
“Bana son iskanci Fodio.”
Sharce goshin shi Fodio ya yi.
“Kana tsoratani yau din nan.”
Murfin motar shi Hamza ya bude yana shiga, saida ya rufo tukunna Fodio ya wuce yana shiga tashi motar, su duka suna fita daga gidan, da yake Fodio baima dade da samun maigadi ba, su suke jigilar bude gate dinsu da rufewa da, yanzun ko gidanma bai damu daya kulle ba. Malali suka nufa dan su zasu dauki su Hindu, gudun da Hamza yake yi da mota, Fodio addu’a kawai yake a ran shi su dauke su, su karasa wajen dinner din lafiya.
“Karka bari ya yi wani shirme.”
AbdulHafiz ya jaddada mishi kafin ya fita, baya jin yasan wani abu shakka, ko kuma shayin wani tun tasowar shi, ko Yayyen shi tunda ya kawo karfi babu wanda zai daga mishi dan yatsa bai lankwasa ba, amman AbdulHafiz na mishi wani irin kwarjini naban mamaki, akan AbdulHafiz din yasan me ake nufi da samun Babban Yaya da har ranka kake da tabbacin zai kula da kai da duka zuciyar shi, har a kullum yana godema Allah daya kadarta kasancewar AbdulHafiz din a rayuwar su, dan shi Alheri ne tare da su gabaki daya.
Suna karasawa, Hamza ne ya fara shiga da motar, ya samu waje cikin harabar gidan yayi parking dinta, a jiki yabar mukullin yana fitowa, cikin gidan ya shiga kanshi tsaye, duk da bazai ce ga dakin da Hindun take ciki ba, amman yaji hayaniyar su, dan haka ya nufi dakin da yake anan kasa, tunda gidan hawa biyune. Kwankwasawa ya yi, yana tattaro duk wani karfi daya rage mishi ya dora murmushi akan fuskar shi.
“Waye?”
Yaji muryar Dimples da yanajin ita kadai zai iya ganewa duk a kawayen,
“Ku fito.”
Hamza ya fadi, yana gani aka murda hannun kofar ana budewa.
“Ango kasha kamshi.”
Dimples ta furta, murmushi ya karayi.
“Ku fito ko zasu yi wata magana, kafin suce mun saka musu ido.”
Dimples ta fadi tana raba Hamza ta wuce, su Biebee ma wucewar suka yi, Hamza ya taka yana shiga cikin dakin, hadi da mayar da kofar ya rufe, a tsaye ya hangota, tayi wani irin kyau naban mamaki, jira yake yaji abinda yake ji duk idan ya ganta, musamman yanzun da take halalin shi, amman sai take yi mishi kamar abincin da ya dade yana jira bayan matsananciyar yunwar da har taci shi ta cinye, saboda haka duk wani zumudin da yake yi ya fita daga kan shi. Takawa ya yi ya karasa inda take, kamshin da take yi na saka shi lumshe idanuwan shi, kafin ya kara bude su a kanta.
Itama yawatawa take yi da nata idanuwan akan fuskar shi,duk da sai da ta daga kanta saboda tsayin shi, yayi mata kyau matuka, hular kan shi kalar kayan jikinta. Magana take sonyi, amman batasan abinda ya kamata tace mishi ba, ga zuciyarta da take ta dokawa kamar tana son fitowa ta nuna ma Hamzan abinda harshen Hindun ya kasa furta mishi, hannun shi ya dago yana saka yatsan shi ya taba janbakin da yake kan lebenta da ya yi mishi kyau matuka, kafin ya sauke hannun yana amfani da duka biyun ya kamo kowanne cikin nata.
Dago dasu ya yi, ya ware tafukan hannuwanta yana dorawa kan kuncin shi hadi da runtse idanuwan shi yana sauke numfashi.
“Lafiyar ka?”
Hindu ta bukata a tsorace, yanayin shi yana saka gwiwoyinta yin sanyi, hannun shi yana kan nata da yake kuncin shi, har lokacin idanuwan shi a lumshe suke, ya girgiza mata kai.
“Ko ma maka wani abu?”
Ta bukata cike da son gano inda matsalar take, dan wannan ba Hamzan ta bane ba, Hamzan da yake nuna mata ya kasa jira hannuwan shi su sauka a kanta, yanzun gata a gaban shi a matsayin tashi, amman ta nemi duk rawar kan nan ta rasa, sai lokacin ya bude idanuwan shi yana sauke su cikin nata.
“Bake bace ba, babu abinda ki kayi mun.”
Kai tadan daga mishi tana sauke numfashi, kafin a hankali ya sauke hannuwanta daga kan kuncin shi, yana dan dumtsa yatsunta, kafin ya saki hannuwan nata, wani irin mayafine yake gani kamar alkyabba, amman daga kafadarta yake manne, ya sauka har kasa yana baje, yayi mishi kyau, kamawa yayi yana kara gyara mata.
“Kinyi kyau.”
Ya furta da wani irin sanyin murya da yasa kai kawai ta iya daga mishi.
“Mu je?”
Ya bukata, ta daga mishi kai, jakarta ta dauka tana rikewa a hannunta, wayarta na hannun Biebee. Tare suka fita, Hamza ya bude mata mota ta shiga, yana taya ta tattare rigarta da mayafin ta shigar cikin motar sosai, kafin ya zagaya ta dayan bangaren yana shiga shima. Tayar da motar ya yi, yana fita daga gidan, a hankali yake tukin, su dukan su babu mai cewa komai, kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi har suka karasa wajen dinner din.